FASSARAR WAƘAR NOT Ramaiya VASTAVAIYA

FASSARAR WAƘAR NOT Ramaiya VASTAVAIYA



* Sunan Waƙa: Not Ramaiya Vastavaiya

* Sunan Shiri: Jawan

* Shekarar Fita: 2023

* Harshe: Hindi/Hausa 

* Rerawa: Anirudh Ravichander, Shilpa Rao da Vishal Dadlani

* Rubutawa: Kumaar

* Haɗa Sauti: Anirudh Ravichander

* Taurari: Nayanthara da Shah Rukh Khan

* Fassarawa: Haiman Raees 


* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana. 

* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana. 

* Dance with me now. I can’t break away.

  - Yi rawa tare da ni yanzu. Ba zan iya fecewa ba ai. 
  
* Aaj Sari Fikrein Tu Shake Away Shake Away

- Damuwoyi? Kau da su gefe, kau da su gefe. 

* Dil Thirakta Dance Wale Groove Pe
 
- Zuciyata na bin kiɗa da rawa. 

* Nachun Main Tu Step Mera Vekh Ve Vekh Ve

- Bari ku ga yadda zan cashe. 

*Aaj Sare Kam Kal Pe Tal Ke

- Ku yi aikin yau gobe. 

* Tak Dhina-Dhin Nach Jayein Tal Pe Tal Pe

- Mu cashe da kiɗin nan. 

* Disco Dance Blues Sare Bhool Ke

- Manta da salon kiɗan disco, jazz da blues

* Desi Wale Geet Pe Tu Jhool Ke Jhool Ke

- Ku yi juyi da waƙar kiɗan gargajiya na desi. 

* Pehle Kiya Chaiyya Chaiyya Re Ab Karun Tata Thaiya

- Ɗazu mun yi Chaiyya Chaiyya, yanzu kuma za mu yi Tha Tha Thhaiya.

* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana.  

* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana. 

* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana. 

* Sab Mazedar Hua Haule Haule

- Da sannu dai, komai yanzu ya zamo mai faranta rai. 

* Thoda Nashedar Hua Mann Yeh Dole

- Zuciyata ta kaɗu, yanzu sai cashewa take yi. 

* Aaj Koyi Nachta Hua Sa Jadu

- Yau rana ce mai cike da sihiri. 

* Sar Pe Sawar Hua Dil Yeh Bole

- Zuciyata na faɗa min cewa sauti ya shiga kaina. 

* Doobi Khushiyon Mein Rat Apni Jabse Suraj Dhala

- Tun da rana ta faɗi, darare suka cika da annushuwa.

* Chhod Sharmana Aaj Nach Le Pair Chakk Le Zara

- Kada ki ji tsaron barin ƙafafuwanki su taka. 

* Pehle Kiya Chaiyya Chaiyya Re Ab Karun Tata Thaiya

- Ɗazu mun yi Chaiyya Chaiyya, yanzu kuma za mu yi Tha Tha Thhaiya.

* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana.

* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana.

* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana.

* Ramaiya Ae Vastavaiya Aiya Ho Ramaiya Ae Vastavaiya Ho

- Ramaiya, zo da sauri. Ramaiya, zo da sauri mana.

Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com
#haimanraees #Jawan600cr

MASOYAN JARUMI SHAH RUKH KHAN NA NIJERIYA SUN KAFA TARI



Shah rukh Khan fans of Nigeria sun kaffa BABBAN tarihin da Babu wasu fans da din Wani jarumi ko wata jaruma da suka tabba. Kafa ..A wajen celebrating din fitar jawan da sukayi haka ne ya Saka fans din SRK na duniya .. summa sai da sukayi posting dinsu A page nasu ... Kuma wnnn kunyi ita one of fans da SRK yake bibiyarta sannan kowa yaga alamar cewa Shima Kansa SRK ya danna musu (like). Hakanee ya Saka mutanee sukee ta mamaki akan wnnn abun da Babu wata kungiya .. da SRK ya tabba dannawa (like). A Africa baki Daya ..... Tabbas mu fans din boollywood of Nigeria kokarinmu sai karuwa yakeeyi a idon duniya .. musanman wajen jajir cewarmu .. da afiyarmu da dukiyarmu mukee duk abinda muke so .... Masha Allah.. Allah ya karemu🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏main Hoon Yuseep Hassan Khan ✍️...

30 YEARS OF GARDISH


10-09-1993 --- 30 YEARS OF GARDISH

~A irin wannan rana aka fitar da Film ɗin Gardish na Producer Director Priyadarshan inda yake cika shekaru 30 cif,

~Gardish yana ɗauke da jarumai irin su: Shammi Kapoor, Jackie Shroff, Amrish Puri, Aishwarya, Farida Jalal, Dimple Kapadia dss, kuma wannan Film shine na farko wanda Amrish Puri da Farida Jalal suka fito a matsayin mata da miji, Bugu da ƙari kuma dai shine Film ɗin jarumi Mukesh Rishi na farko a Hindi Cinema,

~Javed Akhtar shine ya rubuta waƙoƙin wannan Film yayin da Rd Burman ya bada kiɗan su, sai mawaƙan da suka Baje basirar su a ciki da suka haɗa da: Asha Bhosle, Malabar Gopalan Sreekumar da kuma mawaƙi SBP wanda cikakken sunan sa shine "Sripathi Panditaradhyula Balasubrahmanyam" cikin waƙoƙin har da "Rang Rangeeli Raat Gaaye" da kuma "Yeh Mera Dil To Pagal Hai".@AyƘoƘi.

SALAAM NAMASTE

SALAAM NAMASTE


~Shima dai wannan Film mai suna Salaam Namaste wanda ya rabauta da zaƙaƙan waƙoƙi ya cika shekaru 18 da fitar sa, inda aka sake shi a shekarar 2005, inda ya zamo Film na farko da aka ɗauke shi a Austaraliya, 

~Labari ne dai na wasu matasa guda biyu Nick Saif Ali Khan da Ambar Preity Zinta wadanda suka yanke shawarar barin iyayensu domin suyi rayuwar su ta kashin kansu mai cike da yankin a ganin su, inda suka koma yankin *Melbourne* wato ɗaya daga cikin manyan biranen yankin Australia domin ayi Rayuwar uwa ba ƙwaɓa, Aditya Chopra shine ya shirya wannan Film yayin ta Siddharth Anand ya bada umarni,

~Salaam Namaste shine Film na huɗu mafi kawo kuɗi a shekarar 2005, Haka ita ma jarumar ciki wato Preity Zinta ta rabauta da kyautar Jarumar jarumai a Filmfare Awards, IIFA Awards, Star Screen Awards da kuma Zee Cine, inda mawaƙa Irin su: Shaan, Suno Nigam, Kunal Ganjawala da Vasundhara Das suka bada waƙoƙin cikin sa har guda 7 duk zaƙaƙa kuma shahararru kamar irin su: My Dil Goes Mmmm da kuma waƙar ta tazo da sunan Film ɗin wato Salaam Namaste, sai Vishal–Shekhar da suka bada kiɗan Jaideep Sahni ya rubuta su.@AyƘoƘi.

CHAALBAAZ

CHAALBAAZ




~Film ɗin ChaalBaaz kenan wanda aka fitar a shekarar 1989 inda ya cika shekaru 34, wannan Film dai shine guda ɗaya Tilo wanda aka ga jarumi Sunny Deol da Rajnikanth sunyi aiki tare, Haka Jarimar ciki ma wato Sridevi anyi nominating ɗin ta a matsayin Jarimar jarumai mata ta wancen shekarar bisa gudunmawar da ta bada a cikin wannan Film inda ta rabauta da kyautar a bikin bada kyaututtukan Filmfare Award da akayi a shekarar 1990,

~An gina labarin wannan Film akan wasu yan'uwa mata guda biyu Anju da Manju waɗanda suka rabu tun daga haihuwar su inda kowacce tayi rayuwar ta a wani waje na daban, inda aka ɗauko wasu abubuwa daga labarin Film ɗin nan na Hema Malini, Dharmendra da Sanjeev Kumar wato SEETA AUR GEETA, Ragowar fitattun jariman da suka taka rawa a wanann Film na Chaalbaaz sun haɗa da: Annu Kapoor, Anupam Kher, Shakti Kapoor, Aruna Irani, Kader Khan, Saeed Jaffrey, Johnny Lever dadai sauran su,

~Anand Bakshi shine ya rubuta waƙoƙin cikin sa, yayin da Kavita Krishnamurthy, Muhd Aziz, Amit Kumar, Sudesh Bhosale har ma da Johnny Lever suka rera su, inda waƙar "Na Jaane Kahan Se Aayi Hai" ta zama mafi karɓuwa a wancen lokacin,

~Fitattun Team ɗin nan na makaɗa waɗan da babu waɗan da suka kaisu yawan kida a tarihin Hindi Cinema wato Laxmikant–Pyarelal sune sukayi music ɗin wannan Film, wanda wanda shi Pyarelal (Ramprasad Sharma) a wannan mako ne ma ya cika shekaru 83 duk da yake abokin aikin masa ya jima da wucewa, sunyi music a fina-finai kusan guda 800 tun farawar su.@AyƘoƘi.

FILM DIN JAWAN KASUWANCINSA NA DUNIYA GABADAYA

FILM DIN JAWAN KASUWANCINSA NA DUNIYA GABADAYA.



DAY 1 126.60 CR
DAY 1 110.87 CR
DAY 3 144.22 CR

GABADAYA RANAKU UKU A DUNIYA 384.69 CRORES

A YAU ZAI IYA DOSAR CRORES 500 GABADAYA DUNIYA.

 WANNAN SHI AKE KIRA DA UNPRECEDENTED TRENDING.

SHAHRUKH KHAN YA KIRKIRI SABON TARIHI


SUMIT KADEL PAGE 

MAIN AAPKE YAAR 
SIR ABDULHAMID KULKUL

JAWAN: MEGA BLOCKBUSTER

A JIYA ASABAR SHAHARARREN FILM DIN NAN ( JAWAN) WANDA AKE YI MASA TAKE DA MEGA BLUCKBUSTER .



 A jiya dai ya tattara kimanin crores 78 gabadaya india inda a bangaren hindi ya hada crores 68 fiyeda ranarsa ta farko inda ya hada 65 a ranarsa ta farko gabadaya india kuma ya hada 75 crores.


Wannan nasarace wacce ake kira UNPRECEDENTED wacce irinta bata taba faruwa ba a baya hakika film din yazo da wata nasara wacce ta wuce tunanin hasashen da manyan masana sukayi kafin fitarsa.



Zuwa yanzu a iya kasar india ya hada crores 206.08 inda a yau akwai kyakykyawan zaton zai tattara makudan kudade fiyeda ranarsa ta farko da kuma ranarsa ta uku 


Inda ya doke tarihin da pathaan ya kafa a kwana uku pathaan yanada 161 crores iya hindi inda jawan yake da 180 iya hindi wannan shi ake kira da TSUNAMI.


Fatan cigaba da samun nasara gagaruma ga SRKIANS


MAIN AAPKE HOON
SIR ABDULHAMID KULKUL

DAIJI FIRST LOOK

RAMESH ARAVIND’S 106TH FILM ‘DAIJI’ FIRST LOOK POSTER UNVEILS… On #RameshAravind’s birthday today, the makers of #Daiji unveil the #FirstLook poster of the #Kannada film.

#AkashSrivatsa - director of #ShivajiSurathkal series - directs #Daiji… Produced by entrepreneur #RaviKashyap.
#HappyBirthdayRameshAravind #DaijiTheMovie








✍️AFFANKHAN KURNA

GUGUWAR SABON FILM ƊIN SRK JAWAN

GUGUWAR SABON FILM ƊIN SRK JAWAN




 Bayan yau An Saki Shirin da Aka Jima Ana Tsumaye na Babban Jarumi Shah Rukh Khan Wanda Yanzu Duk Sinimu Suka Cika Domin Ganewa Idanuwansu, kuma da yawan manyan masana Film da kasuwanci sun yaba da wannan Film kuma kowa yana ganin Film ɗin zai kawo nasara sosai domin har an fara bashi yiwuwar kawo 600cr a karon farko na Film din Bollywood Abinda ba a taɓa ba, Sannan da yawa suna hasashen zai kawo kudin da ba a taɓa kawowa ba a ranar farko na Fina-finan Bollywood Wanda Daman tun lokacin booking na Tikiti Aka fara wannan tunanin na cewa zai iya kawo 70cr a ranar farko bugu da ƙari yau ranar bikin murnar haihuwar Abin bauta a Addinin Hindu watau Krishna ( Ana Kiran ta Janmashtami) tuni yau kasar India Ana Shan Wannan Biki.

#AbbaIndiaDala

600 CR CLUB: FILM DIN #JAWAN YANA SHAN YABO TA KOWANNE BANGARE

600 CR CLUB: FILM DIN #JAWAN YANA SHAN YABO TA KOWANNE BANGARE


_______A yaune aka saki gagarumin film din Nan na jarumi Shahrukh Khan Mai taken JAWAN Wanda matashin Director ATLEE ya shirya film din dai yana samun yabo daga Critic da Kuma ta kowanne bangare yayin da Babban Mai sharhin Nan TARAN ARDASH ya bashi ⭐️⭐️⭐️⭐️½ Kuma ya kirawo film din da MEGA BLOCKBUSTER Yayin da Shima Mai sharhi a Kan film SUMIT KADEL ya kirawa film din da GIGANTIC Blockbuster watan Blockbuster Mai girma Kuma yayi Mai hasashen 500 Cr iya India yayi da yace Kuma zai iya kafa wani sabon Record na 600 Cr Club film din dai ana Yi Mai hasashen zai iya karya kowanne Record Kuma ya kafa wani sabon Record yayi da a Ranar SA ta farko yau ake Tsammanin zai kawo 80 Cr ko sama da Haka World-Wide Kuma ana Mai Tsammanin 140 Cr Indai ya tafi a Haka to film din zai iya kafa saboda record a India da duniya Baki Daya 

✍️✍️
YUSUF KHAN DORAYI
YUSUF UMAR

JARUMA KAREENA KAPOOR TA YI ƘORAFI



Jaruma Kareena Kapoor Bata Jin daɗin ta yanda mutane suke nuna cewa tafi Haskawa acikin Film ɗin Jab we met da Khabi Kush Khabi gum, Jarumar tace Mutane Suna Mantawa da Omkara Wanda Ko Masana Sunfi Jinjina mata a Wannan Film.
Ta bayyana Haka Wajen Kaddamar da Tallar Sabon Film ɗin ta da ya fita me taken Jaane Jaan Wanda Kuma Za a Nuna shi a Netflix Ranar Bikin Zagayowar Ranar Hauwar ta Cikin Wannan Wata Na September.

#AbbaIndiaDala

JAWAN ZAI IYA DOKE PATHAAN



Zuwa Yanzu Duk Wasu Alqalama Suna Nuna Cewa Gagarumin Shirin Film ɗin Babban Jarumi Shah Rukh Khan da Zai Fita Gobe Alhamis Me Taken 'Jawan' Zai Karya Duk Wani Rekod na Ranar Farko Har Shi Kansa Film ɗin sa da Ya Fita Farkon Shekaran nan Watau Pathaan Wanda duk An Samu Gagarumar Nasara Shima Amma alamu suna Nuna Jawan Zai Fishi a Ranar Farko Saboda Tun Daga Ranar Da Aka Fara Bude Kasuwar Siyan Tikiti na Shiga Sinimu ya fara Ƙetare Kowane Film.

#AbbaIndiaDala

SHIN KAMANCECENIYAR INDIA DA NIGERIA A KO INA TAKE?

SHIN KAMANCECENIYAR INDIA DA NIGERIA A KO INA TAKE?



Yayin da Watan da Mukayi Bankwana dashi Ana daf da fara cin kasuwar Film ɗin Babban Jarumi Sunny Deol Me Taken Gadar2 An Samu Labarin Bank of Baroda ( BoB) ta tabbatar da Zatayi Gwanjon Gidan Sunny Deol da take Binsa Kimanin 56cr.
Abin Jan Hankali anan Shine Duk da Sunny ya daina fitowa a Fina-finai kafin Wannan Gadar2 ɗin Amma Fa Zaɓaɓɓen Ɗan Majalisa ne na Birnin Gurdaspur Sama da Shekaru 4 Kuma Har Yanzu Shine a Wannan Matsayin Amma Hakan Be Saka Tun Wuri yayi wadaqa da Kuɗin Al'ummar sa ba Domin Biyan Wasu kuɗaɗen Kuma Bugu da Ƙari Jam'iyyar sa take mulkar Ƙasar Amma duk da Haka ba a Samu Labarin Umarni Daga Sama Akan Kar A yiwa Wannan Ɗan Majilisar Haka ba.

Sau da Yawa Ana Kwatanta Kamanceceniyar India da Nigeria Wajen Wasu Al'adu da Kuma Tsarin Siyasa da Akeyi. 

#AbbaIndiaDala

MU KOMA BAYA: LABARI ME TAƁA ZUCIYA

MU KOMA BAYA: LABARI ME TAƁA ZUCIYA.


Tsohuwar Jaruma kuma Mawaƙiya Sulakshana Asali waqa takeyi Wajen 70s, Daga bisani ta fara Acting a 1975 Kuma ta karɓu sosai domin tana da Ƙoƙari wajen Ayyukan ta, ta kamu da Soyayya Tsohon Jarumi Sanjeev Kumar ( Wanda Akace a zamanin babu wanda ya kaishi iya Acting) Sedai Shi Kuma Yana Matuqar Son Hema Malini ( Dream girl ) Kuma Yayi iya kokarinsa wajen sanarwa Hema Amma taqi Har Daga Bisani ta Auri Dharmendra.
Sanjeev Kumar Ya fara shaye-shaye na takaici har hakan ya fara taɓa lafiyar sa yana yawan zuwa wajen Sulakshana ta bashi shawarwari amma kawai a matsayin ƙawa ya dauke ta, mutane musamman Abokan Aikin su suna yawan cewa Sulakshana ke kaɗai ce zaki iya kula dashi tare da dauke damuwar sa ita kuma a lokacin tana yawan cewa ya aure ta amma yaƙi sedai tana cewa tana jiran wannan lokaci da zai juyo da zuciyarsa gare ta tasan cewa zaizo, kwatsam Sanjeev Kumar ya mutu a lokacin yana da shekaru 47 duk da wasu sukan ce a lokacin yana da shekaru 50, amma dai ya mutu bai taɓa aure ba.
Hakan ya taɓa Zuciyar Sulakshana kuma ta Shiga damuwa marar misaltuwa kuma hakan ya haifar mata da ciwo domin duk wanda yazo neman ta da Aure bata taɓa yarda dashi ba itama dai bata taɓa Aure ba har ta daina aikin film bayan zamanin ta ya huce.
Shekarun bayan nan kusan shekaru 3 kenan a lokacin da take da shekaru 65 tayi mummunan haɗari wanda ƙashin da yake da Alaqa da gamayyar ƙirjin ta ya karye anyi mata aiki sau 4 amma ba a kai ga yanda ake bukata ba, akance tana kasancewa a ɗakinta akan gado tana sauraren Waqoqi na Shekarun kuruciyar su musamman wanda sukayi a lokacin rayuwar su ita da Sanjeev Kumar.

Mutane Sukan ce Banda Ƙaddarar Rayuwa Ina ma Ace Jarumi Sanjeev Kumar Yayi haquri Akan Rashin Hema ya Auri Sulakshana da take mutuwar Son sa.

#AbbaIndiaDala

FASSARAR WAƘAR CHALEYA

FASSARAR WAƘAR CHALEYA 


* Sunan Waƙa: Chaleya

* Sunan Shiri: Jawan

* Shekarar Fita: 2023

* Harshe: Hindi/Hausa 

* Rerawa: Arijit Singh da Shilpa Rao

* Rubutawa: Kumaar

* Haɗa Sauti: Anirudh Ravichander

* Taurari: Nayanthara da Shah Rukh Khan

* Fassarawa: Haiman Raees 



-* Ishq Mein Dil Bana Hai, Ishq Mein Dil Fanna Hai Ho

 - So shi ne mahaɗin zuciya, zuciya ta kamu da ƙauna. 

-* Mita De Ya Bana De, Maine Tujhko Chuna Hai Ho Ho

- Ko ki karya ni ko ki haɗe ni, ke na zaɓa. 

-* Tere Sare Rang Odhke Dhang Odh Ke

- Na kalantu cikin kalolinki, ina kwaikwayon hanyoyinki. 

-* Tera Hua Main Sabko Chhodke Ho Ho Ho

- Zan bar kowa a baya, na zamo naki. 

-* Ishq Ni Karna Nap Tolke Raz Khol Ke

- Ba na so in ƙaunace a ƙarƙashin iyakancewa.

-* Aaya Hoon Main Sabko Bolke Ho

- Tuni na faɗa wa kowa. 

-* Oh Main Tan Chaleya Teri Oar Tera Chaleya Hai Zor

- Gani nan tafe gare ki. (saboda) Kin tsafance ni. 

-* Tera Hoya Main Yar Ve Bhuleya Ae Sansar Ve

- Masoyiya! Na zamo naki, na manta da dukka duniya. 

-* Chaleya Teri Oar Tera Chaleya Hai Zor

- Jan hankalinki yana jawo ni gare ki. 

-* Tera Hoya Main Yar Ve Bhuleya Ae Sansar Ve

- Na zamo naki masoyiya, na bar dukkan duniya. 

-* Jag Tere Liye Chhodiya, Dil Tere Sang Jodiya

- Na ƙyale dukkan duniya, na ba ki zuciyata. 

-* Ab Tera Main Toh Ho Gaya, Pake Tujhe Main Kho Gaya

- Tun da na same ki, na rasa kaina yanzu da na zamo naki. 

-* Jag Tere Liye Chhodiya, Dil Tere Sang Jodiya

- Na ƙyale dukkan duniya, na ba ki zuciyata. 

-* Ab Tera Main Toh Ho Gaya, Pake Tujhe Main Kho Gaya, Kho Gaya Han

- Na rasa kaina, tun da yanzu da na zamo naki. 

+* Ishq Mein Dil Bana Hai, Ishq Mein Dil Fanna Hai Ho, Ho Ho Ho

- Zuciya ta faɗa soyayya, ƙauna ce ta ƙirƙire ta. 

+* Hansa De Ya Rula De, Maine Tujhko Chuna Hai Oh, Oh Ho Ho

- Ko ka sa ni dariya ko ka sa ni kuka, ni dai kai na zaɓa. 

+* Duniya Kehti Ishq Bhool Hai Befizool Hai

- Duniya na gardamar cewa so ba shi da wata ma'ana. 

+* Humko Toh Dil Se Kubool Hai Oh Oh Ho Ho

- Duk da haka na rungume shi hannu bibbiyu. 

+* Tujhme Dikhta Rabb Ka Noor Hai Ek Suroor Hai

- Abin akwai ƙayatarwa ganin ubangiji a tare da kai. 

+* Tu Hai Apna Yeh Guroor Hai Oh Oh Oh Ho

- Na darajtu da ka zamo nawa. 

+* Ve Main Tan Chaliya Teri Oar Tera Chaleya Hai Zor

Gani nan tafe gare ka. (saboda) Ka tsafance ni. 

+* Teri Hoyi Main Yar Ve Bhuleya Ae Sansar Ve

Masoyi! Na zamo naka, na manta da dukka duniya. 

+* Chaleya Teri Oar Tera Chaleya Hai Zor

- Gani nan tafe gareka saboda ka damƙe ni a damƙar ka. 

+* Teri Hoyi Main Yar Ve Bhuleya Ae Sansar Ve

- Na zamo naka masoyi, na manta da dukkan duniya. 

-* Tu Ishq-e-Khwab Khwab Sa Hai, Mera Behisab Sa Hai

- Ke tamkar so ne a mafarki, ke tawa ce ba tare da iyakancewa ba. 

-* Tere Lafz Choom Loon Main, Urdu Ki Kitab Sa Hai

- Zan sumbaci kalamanki, ke abar soyuwa ce tamkar littafin waƙen Urdu. 

+* Tu Ishq-e-Khwab Khwab Sa Hai, Mera Behisab Sa Hai

- Ke tamkar so ne a mafarki, ke tawa ce ba tare da iyakancewa ba

+* Tere Lafz Choom Loon Main, Urdu Ki Kitab Sa Hai

- Kina da wani irin zaƙi irin na kundin waƙen Urdu, kuma zan sumbaci kalamanki. 

-* Jag Tere Liye Chhodiya, Dil Tere Sang Jodiya

- Na ƙyale dukkan duniya, na ba ki zuciyata. 

-* Dil Tere Sang Jodiya, Ishq Mein Dil Fanna Hai Ho Ho

- Na ba ki zuciyata, zuciyata ta kamu da ƙaunarki. 

-* Ab Tera Main Toh Ho Gaya, Pake Tujhe Main Kho Gaya,

- Na rasa kaina a ƙoƙarin zamowa naki. 

-* Jag Tere Liye Chhodiya, Dil Tere Sang Jodiya

- Na ƙyale dukkan duniya, na ba ki zuciyata. 

-* Dil Tere Sang Jodiya, Ishq Mein Dil Fanna Hai Ho Ho

- Na ba ki zuciyata, zuciyata ta kamu da ƙaunarki. 

-* Pake Tujhe Main Kho Gaya, Kho Gaya Han

- Na rasa kaina tun da na same ki. 


Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com
#haimanraees #Jawan600cr
 

BAHUBALI THE BEGINNING - FANSAR ZUNUBI TA HANYAR CETO RAI

BAHUBALI THE BEGINNING - FANSAR ZUNUBI TA HANYAR CETO RAI






An hangi lady sivagami dauke da dan jaririn Amarendra bahubali da devsena, kibiyar da sarki bhallaldeva ya harbe ta dashi yana nan soke a bayan ta. A lokacin da ya harbe ta, anyi tunanin ta mutu, in kuwa ta mutun to dole tare da jaririn zasu mutu, tunda suna cikin kogi a lokacin da ya harbe tan so cikin kogin zasu fada..

 Wasu dakarun sarki sun biyo ta a baya, inda ta yi musu kwanton bauna tare da shammatar su, ta kashe su. Cikin galabaita ta ci gaba da tafiya, can ta hango dan karamin gari nesa da ita da alamun fitilu a kunne, amma kafin tayi wani yunkuri se ta zame igiyar ruwa ya jata suka fada cikin kogin ita da jaririn. 

Dake ruwan na da zurfi kuma da fadi, ta tabbatar baza ta rayu ba, kuma ta tabbatar in ta mutu to jaririn ma ya mutu, wanda kuma duk wannan hadarin da ta shiga dan ta cece shi ne.. Anan ta daga fuskar ta ta kalli sama. Sai ta ce 

PARMESHWAR - YA UBANGIJI 

TU MERE PAAPO KA PRASCHIT CHAHTA HAI TOH MERE PRAAN LEY LEY - IDAN MUTUWA KADAI SHINE HANYAR FANSAR WANNAN ZUNUBI DA NA AIKATA TO KA DAU RAINA 

 LEKIN ISS BACHE KO JEEWAN DAN DEY DEY- AMMA YARON NAN YA RAYU 

 JO ISKI PRATIKSHA KAR RAHI HAI USS MAA KE LIYE ISSE JEENA HOGA, - YA RAYU DOMIN MAHAIFIYAR SA DAKE JIRAN SA 

MAHISHMATI SINGASAN KE LIYE ISKO JEENA HOGA. - YA RAYU DOMIN YA DARE KUJERAR SARAUTAR BIRNIN MAHISHMATI 

MAHINDRA BAAHUBALI KO JEENA HOGA! - MAHENDRA BAHUBALI YA RAYU!!!

Gama furta wadannan, se fuskar ta ta fara nutsewa cikin ruwan, alamar ta mutu, Amma abin al'ajabi hannun ta na dage da jaririn bata sauke shi ba, haka hannun ya kasance a dage, jaririn na ta tsala kuka, har se da gari ya waye a haka, har wasu mutane daga kauyen dake kusa da gurin sun fito, kawai suka ji alamar kukan jaririn, sukai ta dube dube, har de suka hango jaririn a hannun ta bata sauke ba duk da ta dade da mutuwa. Har se da mutanen suka nufi gun suka karbi jaririn daga hannun ta, sannan ne aka ga hannun ya sauka ya nutse cikin ruwa.

A zahiri na rayuwa hakan ya saba da hankali, ace mutum ya mutu amma hannun sa na dage kuma da jariri a hannun. Se de a irin cinema da S S RAJAMOULI ya kirkira a film din BAHUBALI, akwai sakon da yake son isarwa...

Sivagami ta aikata kuskure babba na bada odar kashe Amarendra bahubali, wanda bata ma san makirci aka hada ba dan ae masa sharri cewa ya yi yunkurin kashe sarki,...

Bayan kattapa ya kashe bahubali ta hanyar sukan sa a baya, sarki bhallaldeva yazo gun yai ta saran sa, yana fadar yadda suka yaudari sivagami har tayi passing odar cewa a kashe Amarendra bahubali, ta hakan ne kattapa ya fuskanci cewa ashe makirci ne.. Kuma ya bayyanawa sivagami yadda aka shirya makircin,.. Anan nadama ta shige ta sosai. Cikin fusata ta dauki dan jaririn bahubali ta yi wajan bene da shi inda dimbin al'umma suke cikin rudu na rashin sanin shin bahubali na raye ko ya mutu.. Anan ta daga kai tace musu

AMARENDRA BAHUBALI NAHI RAHE - Amarendra bahubali baya raye

ABHI APKE MAHARAJ HAI - Amma yanzu kuna da sabon sarki..

MAHENDRA BAHUBALIII -!!!!

jin kalmar mahendra bahubali ya dawo musu da kwarin gwiwar su.. Nan dimbin al'ummar garin SUKA dinga daga hannu suna cewa

MAHENDRA BAHU!!! MAHENDRA BAHU!!!!

Hakika S S RAJAMOULI ya nuna mana cewa sivagami ta fanshi zunubin da ta aikata ta hanyar sadaukar da rayuwar ta wajan tseratar da jaririn, kuma Ubangiji ya amsa rokon ta sanda take mika bukatar ta gare shi duk da tana tsakiyar kogi mai zurfi da fadi da kibiya cake a bayan ta, tana kuma shirin nutsewa. Alamu sun nuna cewa Ubangiji ya karbi addu'ar ta, shi yasa duk da ta mutu, hannun ta dake dage kuma rike da jariri bai sauka ba, har se da gari ya waye aka samu mutanen da suka ga jaririn a hannun ta suka kawo kawo dauki har suka karbi jaririn, sannan ne tayi giving up gaba daya, inda aka ga hannayen sun karasa nutsewa... 

A doro na hankali, aga mutum ta nutse a cikin katon kogi ko teku, kuma ta mutu, amma hannun ta dauke da jiriri yana a dage tun tsakiyar dare har gari ya waje, har se da aka ceci yaron sannan hannun ma ya nutse, to akwai sako mai muhimmanci.... 

#Akk. 6 YEARS OF BAHUBALI THE CONCLUSION

WASU LAMURAN GASKIYA AKAN PRIYANKA DA BA KOWA ZAI IYA YARDA BA

WASU LAMURAN GASKIYA AKAN PRIYANKA DA BA KOWA ZAI IYA YARDA BA:


Shahararriyar Jaruma da ta fara Mamaye Bollywood Saboda Kwarewa da Sanin Aiki ta Ƙara Nutsawa Hollywood, Jarumar da ta karɓi Sarauniyar Kyau ta Duniya a 2000 watau Priyanka Chopra Yau 18, ga Watan July ta Cika Shekaru 41 An taɓa tambayar ta Akan Ɓoyayyun Al'amura game da ita tace Acikin su Shine Ita tana da matuqar son zaman gida ( Homebody) domin tana son Rayuwa Cikin Iyali Kuma Tana Amfani da Damar ta basu lokaci Har Yanzu duk lokacin da ta samu faraga, Sannan tace ta tsani yin Party Kwata-kwata Gaba ɗaya tsarin ta da tunanin ta irin na Mutanan dah ne watau can shekarun baya irin wannan zai bawa Mutane mamaki saboda yanda Ake ganinta Cikin Fina-finai musamman na farko-farko wajen 2004 irinsu Andaz da kismat Amma ita wannan Kawai Aiki ne ba haka take ba tasan da yawa Zasuyi mamaki sedai wannan shine gaskiya kuma shine a ran ta a cewar wannan Jaruma kenan yayin da Filmfare sukayi tattaunawa da ita.

#AbbaIndiaDala

FILMFARE MAGAZINE - SEPTEMBER 2021

FILMFARE MAGAZINE - SEPTEMBER 2021


TATTAUNAWA DA JARUMA SONAKSHI SINHA 

CI GABA... 
****************************************************************************************

 ABIN FARIN CIKI NE GANIN IRIN KARƁA DA AKAI MASA, KO?

Kwarai kuwa. Akwai farin ciki mai gamsarwa, kamar yadda nace ne, wani bangare ne da babu isasshen ilimi akan sa, baka san me zaka tarar ba, ina ze zama makomar sa, yadda ze kasance,

 Amma irin karbuwa da abin ya samu da sharhi me kyau daga bakunan mutane, abu ne mai matukar dadi. Nima na saida fenti na na farko, na kuma yi amfani da abinda nake samu a aikin don yin taimako nan da can.. Ko a lokacin lockdown na yi dan yi wasu zanunnuka, sannan na saida wasu daga fenti na nayi taimako da shi.. Wannan ma wani abu ne na farin ciki gare ni,

Amma idan ka saida fentin naka ma ka samu kudi shima ae abu ne me dadi ko, domin babbar alama ce ta nuna cewa ka samu sana'a me kyau bangaren fasaha. Naji dadi da ya kasance zan iya yiwa kaina haka 
****************************************************************************************

ZAKI IYA KAMANTA SHI TA KOWACCE FUSKA DA IRIN KUDIN DA KIKA SAMU A FILM DIN KI NA FARKO? 

SONAKSHI SINHA - Sosai ma. Da yake abu ne da nake yi tun ina karama, hakan ya karawa abin armashi. Kuma Naji shi wani daban haka 
****************************************************************************************

KINA DA WANI SHAKKU AKAN SHIGA TSARI NA MANHAJAR OTTY? 

SONAKSHI SINHA - A gaskiya bazan ce haka ba domin OTT ya kunshi abubuwa na mamaki da kayatarwa. Na samu damar yin aiki da REEMA KATGI a karo na farko Haka ma EXCEL. Ban taba aiki dasu ba. Kuma irin cinema nasu yana burge ni, saboda haka sha'awar aiki dasu ya zama abu me sauki gare ni.

Na kwadaitu da aiki a cikin wannan tawagar, kuma script din nasu ya tsaru sosai, Character dina mai kyau, Na zabi na karbe shi, Babu wani dalili da zan ce A'a,.. To me yasa ma zan ki karɓa? Saboda series ne ba Movie ba? 
****************************************************************************************

YAYA ZAKI BADA LABARIN IRIN KARUWA TA ILIMI DA KIKA SAMU A FAGEN OTT? 

SONAKSHI SINHA - Ya kasance tamkar yin fina finai uku a lokaci guda, Amma akwai nishadi Fa. Nishandin ma na daban ne. Kamar de gashi a series, masu bada umarnin sun haura mutum daya. Muna da masu bada umarni guda biyu, wato REEMA KATGI da RUCHIKA OBEROI.

 Akwai lokuta da suke bani kariya kamar ace, kin gama da SONAKSHI da safe saboda haka kyaleta ta koma gun aiki.. Ni kuma na rike baki ina ta'ajibi na cewa mene kuma haka!!! To kamar yadda nace ne sabon abu ne gare ni, kuma yana nisahadantar dani. 

Akwai kayatarwa kayi aiki da da me bada umarni da safe wanda salon yake daban sannan da yamma kayi aiki mai bada da ya sha bamban to kowace fuska da na safiyar kuma abu mafi ban nishadi shine yadda masu bada umarni guda biyun zasu hade ayyukan da suka yi a lokuta daban zuwa waje guda.. Kuma ya zama abu guda... 
 ****************************************************************************************

TO BE CONTINUED...

AKK

FASSARAR WAƘAR ZINDA BANDA HO



FASSARAR WAƘAR ZINDA BANDA HO 

* Sunan Waƙa: Zinda Banda Ho

* Sunan Shiri: Jawan

* Shekarar Fita: 2023

* Harshe: Hindi/Hausa 

* Rerawa: Anirudh Ravichander

* Rubutawa: Irshad Kamil

* Haɗa Sauti: Anirudh Ravichander

* Tauraro: Nayanthara da Shah Rukh Khan

* Fassarawa: Haiman Raees 


* Asoolon Par Jahan Aanch Aaye Takrana Zaroori Hai

- Yayin da kimar mutum ta shiga haɗari, dole ne ya maida martani. 

* Banda Zinda Ho Toh Zinda Nazar Aana Zaroori Hai

- In dai har mutum na raye, to dole ne ya nuna alamar yana raye. 

* Banda Ho To Zinda Ho

- Matuƙar mutum na so ya wanzu, to dole ya rayu matuƙar iyawarsa. 

* Dil Nachda Re, Dil Nachda

- Zuciya na juyawa, zuciya na juyawa. 

* Khulke Thirakne Se Bachna

- In za ka iya, ka hanu ga barin zumuɗin takawa. 

* Dekh!

  - Kalli! 

* Himmat Se Nacho Thirak Thirak Yaro

- Abokaina ku himmatu da rawa cikin shauƙi. 

* Dharti Hilla Do Thirak Thirak Re

- Ku girgiza ƙasa da rawar ku. 

* Mati Ka Badal Ufak Ufak Jaye, Ambar Jhuka Do Thirak Thirak Re

- Ku jawo giza-gizai su yi rawa tare da ku, ku jawo samaniya ta yi rawa tare da ku. 

* Ladak Madak Banda Ho! Khadak Dalak Banda Ho!

- Dole ne mutum ya bunƙasa, dole ne mutum ya ci gaba. 

* Fikar Fikar Zinda Ho! Banda Ho Zinda Ho!

- Dole ne mutum ya damu! Dole ne alfaharin mutum ya zama yana nan lafiya. 

* Tabad Todak Banda Ho! Falak Talak Banda Ho!

- Dole ne mutum ya zama jarumi! Dole ne tunanin mutum ya girmama kamar sararin samaniya. 

* Sabar Shukar Zinda Ho! Banda Ho Zinda Ho!

- Dole ne mutum ya yi haƙuri! Dole ne alfaharin mutum ya zama yana nan lafiya.  

* Tadpan Rangare Dhadkan Angare

Muradansa dole su zamo wanzazzu. Bugun zuciyarsa dole dole ya dinga tashi da wuta. 

* Tan Mann Gangare Zinda Banda Ho

- Zuciyarsa da jikinsa dole su zama tsarkaka kamar ruwan kogin Ganga. 

* Arre Tan Mann Gangare Zinda Banda Ho

- Zuciyarsa da jikinsa dole su zama tsarkaka kamar ruwan kogin Ganga. 

* Jhatpat Jhoomar Ghoomar Jhanjhar Baje Re

- Sarƙar ƙafa na ci gaba da kaɗawa ba ƙaƙƙautawa. 

* Pairon Thale Dhuan Chale

- Wuta na tashi a ƙasan ƙafafu. 

* Jo Na Soche! Jo Na Nache!

- Wanda ba ya tunani, baya yin rawa. 

* Ab Na Rukna Chalne De!

- Ka da ku dakata yanzu, bar waƙar ta ci gaba da tashi. 

* Jhatpat Jhoomar Ghoomar Jhanjhar Baje Re

- Sarƙar ƙafa na ci gaba da kaɗawa ba ƙaƙƙautawa. 

* Koyi Hamare Jaisa Kahan

- Ina mutane suka fi son wanzuwa ne a duniyar nan? 

* Hum Na Jahan Se Humse Jahan

- Mu ba mallakin duniya ba ce, sai dai ita duniyar ce mallakinmu. 

* Jee Mein Jashan Mein Aahat Chale

- Akwai ƙarar bugawa a zukatanmu da farincikinmu. 

* Apne Hunar Mein Chahat Chale

- Akwai matsananciyar soyayya ga ƙwarewarmu. 

* Thirak Thirak Thakna Kyun! Tunak Tunak Takna Kyun!

- Me zai sa ka gaji yayin da kake rawa? Me zai sa mu yi ta kalle-kalle yayin da muke cashewa? 

* Jhijhak Jhijhak Jakhna Kyun! Banda Ho Zinda Ho!

- Me zai sa mu yi jinkiri? Dole ne fa mutum ya more rayuwarsa. 

* Tabad Todak Banda Ho! Falak Talak Banda Ho!

- Dole ne mutum ya zama jarumi! Dole ne tunanin mutum ya girmama kamar sararin samaniya. 

* Fikar Fikar Zinda Ho! Banda Ho Zinda Ho!

- Dole ne mutum ya damu! Dole ne alfaharin mutum ya zama yana nan lafiya. 

* Jeena Jane Jo! Dil Ki Mane Jo!

- Rayayyen mutum shi ne wanda ya fahimci yadda ake rayuwa, wanda ke sauraron zuciyarsa. 

* Kar De Thane Jo Zinda Banda Ho

- Wanda ke bin zaɓinsa. 

* Arre Kar De Thane Jo Zinda Banda Ho

- Rayayyen mutum shi ne wanda ke yanke hukuncinsa da kansa. 

* Jhatpat Jhoomar Ghoomar Jhanjhar Baje Re

- Sarƙar ƙafa na ci gaba da kaɗawa ba ƙaƙƙautawa. 

* Pairon Thale Dhuan Chale

- Wuta na tashi a ƙasan ƙafafu. 

* Jo Na Soche! Jo Na Nache!

- Wanda ba ya tunani, baya yin rawa. 

* Ab Na Rukna Chalne De!

- Ka da ku dakata yanzu, bar waƙar ta ci gaba da tashi. 

* Jhatpat Jhoomar Ghoomar Jhanjhar Baje Re

- Sarƙar ƙafa na ci gaba da kaɗawa ba ƙaƙƙautawa.


Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com
#haimanraees #Jawan600cr

HAKA KAWAI DA INA JARUMA AMMA YANZU NA DAWO FITOWA A UWA

HAKA KAWAI DA INA JARUMA AMMA YANZU NA DAWO FITOWA A UWA



Jaruma Manisha Koirala ta Koka da Juyawar Zamani Yanda da take motsawa Son Ranta take Jan Ragamar Film ko tare da Jarumi Amma Yanzu Gashi itace ta fito a matsayin uwa Hakan yayi mata tsauri, ta furta haka bayan ta fito a uwa ga jarumi Kartik Aaryan cikin Film shehzada tace Lallai zamani ya juyata.
Daga gefe Guda An tambayeta game da Yin Aure ko kasancewar ta a uwa tace ita lamarin ta yanzu a batun uwa tana da karen ta da magen ta watau mawgli da simba, amma tace ƙawayen ta masu Aure da yara suna birgeta kuma hakan ita ma zai mata kyau ace tana da abokin rayuwa.
Jarumar yanzu tana da shekaru 52 kuma ta taɓa Auren wani ɗan kasuwa tun a 2010 sunyi shekara biyu sun rabu a 2012 bata kara Aure ba kuma tana ganin Yanzu koda tana da yara yanzu bata da lafiyar kula dasu domin tayi fama da ciwon Kansa ( Cancer) ciwon daji.

#AbbaIndiaDala

ALIA BHATT YANZU TA CHANJA SHAWARA

ALIA BHATT YANZU TA CHANJA SHAWARA:


Jaruma Alia Bhatt Tace yanzu bazata iya sadaukar da iyalanta Akan Aiki ba, tace Yanzu kome yabiyo bayan iyalanta domin a dah Tana iya sadaukarwa Aikin ta na Film kome Kawai ita Aiki ne a gaban ta amma yanzu da tayi Aure kuma ta zama uwa to sune suka fi muhimmanci sama da kome a rayuwar ta.

#AbbaIndiaDala

TATTAUNAWA DA JARUMA SONAKSHI SINHA

FILMMAKER MAGAZINE - SEPTEMBER 2021 



TATTAUNAWA DA JARUMA SONAKSHI SINHA 

KIN KASANCE MACE MAI MATUKAR KWARIN GWIWA A BAYA BAYAN NAN TA HANYAR KUTSAWA CIKIN SABBIN ABUBUWA KO KUMA BARIN KAFAFEN SADARWA WATO SOCIAL MEDIA. KIN KARA NUNA MUHIMMANCI NA AIKATA HAKAN GA DABI'UN KI... 


SONAKSHI SINHA - Ban taba kasancewa irin macen da ke son yin abubuwa dan jan hankali ko burge wasu ba. Na kan yi abu ne da nake tunanin shine ya kamata kuma suka dace da raayina. Saboda haka idan kana ganin cewa ni mace ce mai matukar kwarin gwiwa, to hakan ya faru ne saboda nayi wasu abubuwa da raayi na suka ayyana mini su ne daidai..

Ni mace ce mai son mai son sirri, kuma ina matukar son aiki na kamar yadda nake son sirri, se ya kasance akwai karo da juna tsakanin son aikin nawa da kuma son sirri. Ma'ana dai yanayin aiki na baya bani damar samun kebancewa akan kai na. Saboda haka lokacin da zan samar wa kaina wanda ya kasance nawa ni kadai yayi karanci. Se nake adana wannan dan lokacin dana ke samu dan kaina sosai.

 Irin hakan ne yasa bayan wasu lokuta na yanke shawarar barin kafa ta sadarwa wato social media. 
********************************************

ME YA SA KIKA RUFE KAFAR SADARWAR KI TA TWITTER? 

SONAKSHI SINHA - Lokacin da na fara kokarin sanin mu'amala ta kafar sadarwa, abin ya kasance me kayatarwa da ban sha'awa, musamman da yake sabon abu ga kusan kowa. Ta hakan zaka kara samun yabo daga mutanen da suke jin dadin aikin ka kwatsam bayan wani lokaci se kafar ta rasa karsashi da tafarkin ta. Mutane suka rasa dabi'a ta kwarai a kafar sadarwa, kowane rukuni na mutane na iya kaiwa gare ka ba tare da samun damar tantance su ba... Matukar ba'a yi wani abu a kai ba, hukuncin da zaka yanke mafi dacewa shine ka cire kan ka daga tsarin,.

Wannan shine abinda nayi. Kuma babu wata matsala da hakan ya kawo, tunda be taba min aiki ba. Hasali ma zan iya cewa barin kafar sadarwa ya samar min da nutsuwa da kwanciyar hankali tunda bana ganin suka da aibatawa da marasa dabi'u masu kyau a kafar sadarwa zasu yi maka... A wajena, Hukunci ne da na yanke a daidai lokacin da ya kamata

********************************************

A BAYA BAYAN NAN KI SAMAR DA WURI DA YA SHAFI SANA'A TA FASAHA MAI SUNA HOUSE OF OPPORTUNITIES.. TA YA HAKAN YA KASANCE??

SONAKSHI SINHA - Fasaha wani abu ne da nake maida hankali na akai idan ina neman samun natsuwa. Dama ce a gare ta fita daga cikin rikita rikitar rayuwa. 

A duk lokacin da nake son dauke hankali na daga rikicin duniyar nan, kawai zuwa nake nayi fenti. A Yan kwanakin nan na kasance ina yawan yin sa ma. Ina jin iko akan wannan fasaha na fenti kuma bana son rabuwa da shi. Zan nuna maka dakin da nake fentin. Zaka ga takalma na sauki a kwance a dakin. 

Ni da kanina muka zauna muka shawarta kafin mu zo da wannan tunanin. Damuwar shine mawuyaci ne kai tsaye ka kutsa cikin wani sabon al'amari da ya kasance sabo ne a gare ka. Na kasance sananniyar jaruma, amma a fage na fasaha se na zamto tamkar wacce bata san alkibla ba. Na rasa gun zuwa, na rasa wanda zan tunkara, na rasa ya zanyi.. 

Daga bisani muka zo da shawarar mu bada dama ga masu sha'awar shiga fage na fasaha kuma suke son kaiwa wani matsayi na daukaka. Ta yiwu daga wani background na rayuwa kake, ko kuma ka kafu a harkar da kake yi, abinda ake bukata daga gare ka kawai shine aiki me kyau da inganci, za a baka dama don nuna me kazo dashi. 

Nima a kan kaina na ga hakan yayi ma'ana kuma zan iya kasancewa a fagen duk da cewa ban kafu ba, Ina yin fenti saboda ina son fenti sosai kuma ina da yakinin akwai dama ta samun kasuwa ga irin sana'a ta.. Kaine zaka tsara al'amuran ka yadda kake son su kasance, kai ne zaka samar wa kan ka damarmaki, kuma a yayin hakan idan har ka taimaki wasu, to al'amura sun yi tafi yadda ake so.. 

TO BE CONTINUED...

AKK..

BANA BUKATAR ƘARA RAYUWAR YARA, NA FISON TA DATTAWA: KAJOL

BANA BUKATAR ƘARA




 RAYUWAR YARA, NA FISON TA DATTAWA: KAJOL

Jaruma Kajol Tace ba Wai An ɓata Mata ne a role ɗin Simran Cikin Film ɗin Dilwale Dulhaniya Le Jayenge ba Amma Bataso ta ƙara Rawa da Ƙananan Kaya Acikin Ruwan sama.
Jarumar tace tana matuqar so taga tana Aiki Irin Na Dattawa Wanda Babu Taɓara ko Hauka Aciki.

#AbbaIndiaDala

WASU JARUMAN BOLLYWOOD DA SUKE NADAMAR FITOWA CIKIN WASU FINA FINAI

WASU JARUMAN BOLLYWOOD DA SUKE NADAMAR FITOWA CIKIN WASU FINA FINAI 



1 AMITBAH BACCAHN 
Big boss Namu Baccahn uban jarumai da yake magana game da film din sa Ram gopal Varma ki Aag ya bayyana cewa " idan film bayyi kyau ba director da jarumi ya kamata a tuhuma, fitowa a Wannan shirin yana daya daga cikin kura kuran Dana aikata a rayuwata. 

2 KATRINA KAIF
Shahararriyar Jarumar ta bayyana cewa tana nadamar fitowa cikin film din BOOM, Acewar kat lokacin da ta fito tai aikin wannan film Sam batasan Yaya Al'adun indiyawa suke ba. Ta bayyana rashin sani a Amatsayin dalilin daya sanya muka ganta cikin film din. 

3 GOVINDA
Game da film din kill dil ya bayyana cewa " matata da yarana sune suka karfafamin gwiywa kan cewar na Amshi film din, Acewar su bai kamata ace ina zabar rawar da zannna takawa cikin fina finai ba" Wannan shine musabbai.

4 PRIANKHA CHOPRA 
Da take magana akan kan experience dinta game da film din ZANZEER ta bayyana cewa "Wani lokacin Mukan Aikata kuskure da kanmu" 

5 SHAHID KAPOOR
 A bayanin sa na bayyana yadda yake Nadamar fitowa cikin film din Shaandaar yace "Ni Sam banga Amfanin film din nan ba, Bansan miyasa na fito cikin sa ba. 

6. TWINKLE KHANNA
Ba iya twinkle khanna ba, hatta su kansu mashirya shirin Mela basa Wani son tunawa da shi. Twinkle ta bayyana Cewa taso ace Mela babu yadda za'ai a tuna da Mela. 

Imam Abdu Bandirawo

PREM KI Shaadi



Jarumi SALMAN KHAN zasu kara haduwa da kamfanin shirya finafinai na RAJESHREE a karo na 5, wadanda suka shirya masa finafinai irinsu "Maine pyar kiya, Hum Apke hain kaun, Hum saath saath hain, Prem RATHAN DAN PAYO" wannan karon ma dai zasu fara aikin film dn nan bada dadewa ba, wanda kuma zai fita a bikin Diwali na shekarar 2024 kamar yadda suka saba fitar da film dn jarumin. Film dn Dai mesuna "PREM KI Shaadi" zaizo ne da labarin maaurata tunda lokacin da sukai neman aure har akai auren sannan aka haihu kuma aka raini yaran har girman su. Shima dn Dai kamar kullm jarumin zaizo da sunan daya saba fitowa dashi a kamfanin wato PREM..

Rikici tsakanin jarumi FARDEEN KHAN dakuma SHAHID KAPOOR



Rikici tsakanin jarumi FARDEEN KHAN dakuma SHAHID KAPOOR ya fara ne tun a lokacin daukar film dn nan na FIDA wanda akai a shekarar 2004, inda achan baya jarumi FARDEEN KHAN ya danyi soyayya da jaruma KAREENA KAPOOR wanda kuma a lokacin daukar film dn take soyayya da jarumi SHAHID KAPOOR wanda haka ne yasa kishi ya turnike FARDEEN KHAN a wajen ya cakumo jarumi SHAHID KAPOOR inda yake tambayar sa meye ne matsalarsa ne da wannan yarinyar, anan Shima jarumi SHAHID dn ya harzuka inda aka raba su, wanda sanadiyar hakanne yasa basa shiri har yanzu.

14-07-1938 ---- HAPPY BIRTH ANNIVERSARY OF OM SHIVPURI AND HIS WIFE Sudha Shivpuri @85 & 84

14-07-1938 ---- HAPPY BIRTH ANNIVERSARY OF OM SHIVPURI AND HIS WIFE Sudha Shivpuri @85 & 84



~An haifi jarumi "Om Shivpuri" a irin wannan rana wato 14 ga watan July na shekarar 1938 a garin Patiala dake kudu masu gabas na yankin Punjabi cikin ƙasar India,


~Om Shivpuri ya kasance jarumi ne a guraren wasanni kafin daga baya ya shigo Hindi Cinema, bayan kammala aikin sa a "National School of Drama" a shekarar 1964,


~Yayi fina-finai a Bollywood Fiye da 175, bayan farawar sa da Film ɗin "Ashadh Ka Ek Din" na Producer Director "Mani Kaul" inda suka fito tare da: Arun Khopkar, Rekha Sabnis da Aruna Irani, inda yafi buga Role ɗin jami'in tsaro,



~Yayi aiki da manyan Producer Directors za jiga-jigan jaruman zamanin sa, inda aikin sa yafi sanuwa a 70s 80s zuwa 90s, Kaɗan daga fitattun fina-finan da Om Shivpuri ya taka rawa a cikin su akwai:

~Kitaab
~Sholay
~Aandhi
~Koshish
~Achanak 
~Geraftaar
~Khushboo
~Hum Dono
~Khubsoorat
~Don --- 1978
~Disco Dancer
~Zakhmi Aurat
~Biwi Ho To Aisi
~Namak Haraam
~Aakhree Raasta
~Andhaa Kaanoon
~The Great Gambler
~Hum Tere Aashiq Hain
~Hum Kisise Kum Naheen

~Da dai sauran fina-finai masu dama inda wasu ma sai bayan rasuwar sa suka fita, a ɓangaren Directing ma ya shirya wasu fina-finan,

~Ya samu nasarori da dama kamar dai ko wanne babban jarumi,


~A shekarar 1968 ne ya auri matar sa mai suna "Sudha Shivpuri" wadda ita ma a irin wannan rana aka haifeta wato "14 July 1937" inda mijin nata ya girme mata da shekara ɗaya, ita ma dai matar tasa jaruma ce musamman a fina-finan gidan television, inda suka haifi ƴaƴansu guda biyu "Vineet Shivpuri" da "Ritu Shivpuri" wadda ita ma jaruma ce a Kannada Film Industry da kuma Hindi Cinema, Film ɗin da ya fara a Bollywood shine Aankhen 1993 inda suka fito tare da Jarumi Govinda da Chunky Pandey da kuma Raj Babbar,

~A ƙarshen shekarar 1990 ne kuma jarumi Om Shivpuri yace ga garin ku nan a sakamakon bugun zuciya da ya same shi, inda ya wuce yana da shekaru 52 a Duniya.

@AyƘoƘi.

14-07-1989 --- 35 YEARS OF BATWARA

14-07-1989 --- 35 YEARS OF BATWARA




A rana irin ta yau Director J.P. Dutta ya fitar da Film ɗin sa mai suna "Batwara" inda yake ɗauke da manyan Jarumai masu yawa irin su: Dharmendra, Vinod Khanna, Mohsin Khan, Shammi Kapoor, Dimple Kapadia, Amrita Singh, Poonam Dhillon, Asha Parekh, Kulbhushan Kharbanda da kuma Amrish Puri dss,

Batwara ya samu nasara kuma shine Film mafi kawo kuɗi a shekarar da ya fita wato 1989. Sai kuma makaɗa Laxmikant Pyarelal da suna buga music ɗin zaƙaƙan waƙoƙin cikin sa.


A bangare guda akwai fina-finai da dama wadanda suma duk a irin wannan rana ta 14 ga watan July suka fita, Ga kaɗan daga cikin su kamar haka:


002 Muqaddar Na Shashi Kapoor da Rekha, 
   14-07-1978. ya cika shekaru 45,



003 Takkar Na Naseeruddin Shah, Sunil Shetty da Sonali Bendre 
   14-07-1995. ya cika shekaru 28,



004 Kunwara Na jarumi Govinda da Urmila Matondkar
   14-07-2000. ya cika shekaru 23,



005 Jungle Na Sunil Shetty, Fardeen Khan, Urmila Matondkar, Makrand Deshpande, Sushant Singh da Himanshu Malik
   14-07-2000 shima ya cika shekaru 23,



006 Jawani Diwani Na Mahaifin Jaruma Karishma Kapoor da Kareena Kapoor wato Randhir Kapoor inda suka fito tare da jaruma Jaya Bhaduri matar Amitabh Bachchan 
     14-07-1972 yau ya cika shekaru 51,



007 Naukar Biwi Ka Na Jarumi Dharmendra da Raj Babbar, Anita Raj, Reena Roy, Kader Khan, Pran da Om Prakash
    14-07-1983, shima ya cika shekaru 40 cif,



008 Jagga Jasoos Na jarumi Ranbir Kapoor da jaruma Katrina Kaif
    14-07-2017, shima ya cika shekaru 6,



009 Golmaal: Fun Unlimited shima wannan Film na Director "Rohit Shetty" wanda na barkwanci inda yake ɗauke da jarumai irin su: Ajay Devgn, Tusshar Kapoor, Arshad Warsi, Sharman Joshi, Rimi Sen da kuma Paresh Rawal, a yau yake cika shekaru 17, 
   14-07-2006.


Abin dai babu wuya... Kamar yau ne zamu ji an saki Film amma sai aji har ya kwashe wasu shekaru masu yawa, Allah dai yasa mu rabauta da kyakkyawan ƙarshe Amen Ya Rabbal-Alamen.

@AyƘoƘi

LOKACIN DA KADER KHAN YA FICE DAGA FILM SABODA BAZAI IYA CEWA AMITABH SIRJI BA

LOKACIN DA KADER KHAN YA FICE DAGA FILM SABODA BAZAI IYA CEWA AMITABH SIRJI BA



Marigayin Jarumi Kuma Fasihin Marubuci Kader Khan da Tsohon Jarumi Amitabh Bachchan Abokai ne Sosai Tun Daga Lokacin da Kader Khan ya fara Rubutawa Amitabh Bachchan Dialogue Sunyi Irin Wannan Aikin Cikin Fina-finai irin su Muqaddar Ka Sikandar (1978), Laawaris” (1981), Coolie (1983), da Amar Akbar Anthony (1977), da sauransu.
Lokacin da Akazo Aikin Khuda Gawah Wajen 1992 Se Akace Ai Lallai Se Kader Khan Ya Kira Amitabh Bachchan da Babban Yallaɓai (Sir ji) Shi Kuma Ya ce Bazai kira Wannan Abokin nasa da Haka ba lallai suka dage ya faɗi haka shi kuma Yace ya haqura da Aikin ma Kwata-kwata.

#AbbaIndiaDala

DAMA HAKA RAYUWA TAKE



Matashin Jarumi Ƙani Ga Jarumi Shahid Kapoor Watau Ishaan Khattar Bayan yayi Fina-finai Biyu Sunyi Nasara Watau Beyond the clouds da Dhadak, Daga Baya yayi Biyu 'Khaali Peeli' da 'Phone Bhoot' Duk An tafka Asara Mutane Suna ta Surutu Akan Haka to ya fito Yace "Dama Haka Rayuwa take Ana sama ana kasa, kuma Ana Komawa Sama" Haka Kowa yake Gudanar da Rayuwar sa.

#AbbaIndiaDala

MANUSHI CHHILLAR TA FARA DA ƘAFAR HAGU



Sarauniyar Kyau ta Matan Duniya Shekarar 2017 ƴar asalin Ƙasar India Manushi Chillar Wadda ta fara Film da Ƙafar Hagu watau Rashin Nasara ta Fannin Kasuwa, Film ɗin na farko me taken Samrat Prithviraj wadda tayi tare da Jarumi Akshay Kumar sedai ƴan kallo basu karɓa ba Hakan be mata daɗi ba amma tace tabbas ta samu wasu Abubuwa da take so kuma tace ba kawai kyau ne zai yi Aiki ba tunda Akwai Jaruman da Suka samu Wannan kambu na kyawun kamar Aishawarya Rai Bachchan da Priyanka Chopra amma ba kowane lokaci sukeyin nasara ba Don Haka Akwai Bukatar mutum ya ɗan ƙara Jajircewa, Yanzu dai Fina-finan ta Na Gaba Sune Bade Miyan Chote Miyan da Tehran.

#AbbaIndiaDala

ƘWAƘWAF: ALGAITA SUN DAƊE BASU FASSARA SHASHASHAN FIM KAMAR WANNAN BA

ƘWAƘWAF: ALGAITA SUN DAƊE BASU FASSARA SHASHASHAN FIM KAMAR WANNAN BA




Asalin labarin film ɗin an ginashi ne akan #Black_Hole wato #Baƙin_Rami, abinda yasa nace sha-sha-shan film shine Black Hole yana buƙatar nagartaccan aiki kafin a gane abinda Ake son nunawa amma basuyi hakan ba, kawai suka birbira labarin suka barshi, Kuma Black Hole mas'ala ce mai girman gaske wadda tana buƙatar bayani sosai kafin a fahimta.

Abinda ya faru a film ɗin: sun nuno wani Malamin kimiyya yana maganar zuciya yana cewa ya yarda da kansa kuma shi kaɗai zaiyi nasara a wannan aiki, a ƙoƙarinsa na samar da na'urar da zata kai mutum zuwa ga Black Hole (Wanda har yanzu a duniya an kasa samun wanda zaije wannan duniya ta Black Hole, saidai an samu dakyar an dakko hoton black holes a wasu shekaru da basu wuce 5 zuwa 7 ba)

NASAN MAI KARATU ZAI SO YAJI MENE BLACK HOLE

#BLACK HOLE (Baƙin Rami) A TAƘAICE
A cikin ilimin Physics game da duniya da abubuwan da ke kewaye da ita (Space), malaman Physics (Astrophysics/Astronomy) tun shekaru da dama sun gano wata duniya ta musamman da suke kira "Black Hole (Baƙin Rami)". A dunƙule shi Baƙin Rami (Black Hole) wata duniya ce mai zamana kanta a kaunu (space), wadda take da matuƙar tasirin zuƙo da finciko (gravity) duk wani abu da ya kasance ta ya faɗa cikinta. Malaman Physics suna cewa game da duniyar Baƙin Rami: "Once you go black you will never go back!" Ma'ana: duk abin da ya sake ya faɗa cikin baƙin rami, ba zai sake dawowa ba! Suna ƙiyasta girman ƙaramar duniyar Black Hole da adadin girman duniyar rana sau miliyan ɗari (100 million).

#Masana kimiyya suna yiwa (Singularity) wato tsakiyar Black Hole take da “NO MAN'S LAND!”

Duk abin da yazo wucewa ta kusa da "black hole", ta wani guri da ake kira da "event horizon" to sai ya zukoshi ya hadiyeshi saboda karfin janyowar da "gravity" yake da shi a gurin.

Babu mutumin da ya taba kusantar inda "black hole" yake amma da wani zai je gurin da sai ta hadiyeshi irin hadiyar da injin taliya yake yiwa fulawa. Da yake duk abin da ya fada "black hole" to ko alamarsa ba a kara ji domin yana rasa duk wani bayani da yake tattare da shi ta hanyar wani yanayi da suka kira "information loss." Kuma ga shi duk abin da aka harba ya kusanci "black hole" to tasa ta kare, wannan ta sanya komai na Kimiyya yake rikicewa da an zo gun.

To amma yanzu tun da har an iya dauko hotonsa ana tsammanin wannan wata 'yar karamar dama ce da aka samu ta cewa za a iya nazartar cikin "black hole" din a nan gaba domin a ajiye duk wani hasashe a dauki hakika.

#Abinda yasa na kira film ɗin da sha-sha-shan film shine, sunyi abinda hankali bazai ɗauka ba, su sai suka nuna har sun samar da hanyar da za'a shiga waccan duniyar kuma har sun gano mutane ne masu kama damu rayuwarmu ma iri ɗaya ce dasu, #Richard Feynman, wanda ya yi bincike akan me zai faru da zamu iya fadawa cikin "black hole" kuma bamu mutu ba, ya ce idan ka fada cikin "black hole" to wata duniyar (universe) din za ka fada mai wata irin dokar ta dabi'a daban! Dama dai dokokin dabi'a sun rabu gida biyu, tsakanin na manyan abubuwa (Newtonian mechanics) da kuma na mitsi-mitsin abubuwa (Quantum mechanics). Kuma duk masu bincike su tabbatar da cewa dabi'un mutane mabanbanta duniyoyi dole su banbanta.

kenan su shirme sukayi da suka nuna dabi'ar mu iri ɗaya ce da mutanen da suke duniyar Black Hole, kenan har gwara #PK na jarumi #Aamir_Khan tunda sunyi amfani da Maganar masa kimiyya suka nuna dabi'ar mu ba iri ɗaya bace da duniyar su PK. da za'a sake tsara labarin tabbas zai zama babban film idan aka faɗaɗa shi akayi bayani sosai da kuma yin abinda hankali zai ɗauka.

✍️ #Ameenu_Sharada

SHIN KUNA SHA'AWAR KALLON HORROR FILM NA BOLLYWOOD?

SHIN KUNA SHA'AWAR KALLON HORROR FILM NA BOLLYWOOD?




An fara Aikin Film Me taken 'Stree:2' Wanda Wannan Film na Ɗayansa ya fita a 2018 An Samu Nasara Sosai, Film ne Me Launin Ban tsoro ( Horror film) Matasan Jarumai irinsu:- Shraddha Kapoor,Rajkummar Rao,Pankaj Tripathi,Aparshakti Khurana da Kuma
Abhishek Banerjee Sune Suka Ja Ragamar sa Kuma a kashi na biyun ma sune.

#AbbaIndiaDala

ME YA SA RANBIR KAPOOR YA ƘI YIN AIKI DA SONAKSHI SINHA?

Tambayar da Akayi Shin Me yasa Ranbir Kapoor yaƙi yin Aiki da Sonaksi Sinha?



A Shekarun Baya Lokacin da Akaso a Haɗa Waɗannan Jarumai Acikin Film guda Sedai shi Ranbir Yace Tayi Kalar Wadda ta Girmeshi Duk da ya bata Shekaru 4 a Duniya Kuma a irin wannan lokacin tuni yayi Aiki da Jaruman da suka Girme ta Kamar Priyanka Chopra Sunyi aiki da Ranbir Cikin Fina-finai guda biyu Anjana-Anjani da Barfi Haka yayi da Bipasha Basu Cikin Bachena Ae Haseeno.
Daga Gefe Guda kuma ita Sonakshi Sinha tayi Fina-finai da Waɗanda Ranbir ɗin ya girma kamar Ranveer Singh da Arjun Kapoor. Amma duk da haka Ranbir Kapoor a Wannan lokacin yaƙi yin film da Sonakshi Kan Cewa tayi kalar wadda ta Girme shi.

#AbbaIndiaDala

12-07-2002 - CELEBRATING 21 YEARS OF DEVDAS

12-07-2002 - CELEBRATING 21 YEARS OF DEVDAS



A rana irin ta yau ne aka fitar da babban Film ɗin nan mai ɗauke da labari mai taɓa zuciya inda aka nuna wani lokacin iyaye kan shiga tsakanin masoya su farraƙa su ta ƙarfi, wanda a irin hakan ne kuma garin neman gira akan rasa idanun ma gaba ɗaya. 


Fasihin Director ɗin nan Sanjay Leela Bhansali shi ne ya bada umarnin wannan Film inda Bharat Shah ya zama Producer, duk dai ƙarƙashin kampanin Eros International Media Ltd sai jaruman ciki da suka haɗa da: jarumi Shah Rukh Khan, Aishwarya Rai da kuma Madhuri Dixit a Leading Role, sai kuma irin su: Jarumi Jackie Shroff, Kirron Kher, Smita Jaykar da sauransu wadanda suka taka rawar gani. 


Devdas Film ne wanda ya samu matuƙar Nasara, inda aka yi masa babban Budget har na fiye da Crore 50, duk da hakan ya janyo cece-kuce har daga ɓangaren Hukumomin ƙasar ta India domin ana ganin kuɗin da aka kashewa wannan Film sun yi yawa matuƙa, har ake masa laƙabi da Most Expensive Indian Film Ever Made Amma fa a wancen lokacin kenan, duba da yanayin da ƙasar Indian ke ciki a daidai lokacin da Film ɗin ya fita, Amma dai duk da haka kwalliya ta biya kudin sabulu. 


Wasu daga cikin nasarorin da wannan Film ya samu sun haɗa da: National Film Award for Best Popular Film Providing Wholesome Entertainment, Filmfare Award d.s, Haka mafi yawan jaruman ciki sune suka rabauta da zama jariman jarumai a bikin bada kyaututtuka na shekarar 2002, kamar Best Director, Best Actor, Best Actress, Best Supporting Actress da dai sauransu,


A ɓangaren waƙoƙi ma dai wannan Film ba'a barshi a baya ba, domin kuwa fitattun mawaƙan da ake ji da su sune suka baje basirar su irin su: Udit Narayan, Vinod Rathod, Shreya Ghoshal, KK, Kavita Krishnamurthy har ma da ita kanta Madhuri Dixit akwai Muryar ta a cikin daya daga waƙoƙin wato waƙa mai suna Kaahe Chhed Mohe


Makaɗa irin su: Ismail Darbar, Birju Maharaj da kuma Monty Sharma wanda dan'uwa ne wajen shahararren makaɗin nan da baya wato Pyarelal wanda ya shahara da yin aiki tare da Laxmikhan, sune suka bada music ɗin wskonl Waƙoƙin wannan Film ciki har da waɗan da suka fi shahara wato waƙar Dola Re Dola, Maar Daala da kuma Silsila Ye Chahat Ka inda ita ma mawaƙiya Shreya Ghoshal ta samu nasarar tafiya da Best Female Playback Singer da waƙar ta mai suna Bairi Piya. 


Tun a shekarar 1955 wani Producer Director mai suna Bimal Roy ya yi Film mai wannan suna wato Devdas inda yake ɗauke da jarumi Dilip Kumar, Suchitra Sen da Vyjayanthimala, duk da yake akwai wasu fina-finan ma kafin shi din da suka zo da irin wannan suna na DEVDAS.

@AyƘoƘi

32 YEARS OF PHOOL BANE ANGARAY

32 YEARS OF PHOOL BANE ANGARAY



Shima wannan Film mai suna "Phool Bane Angaray" na Producer Director K. C. Bokadia a irin wannan rana ya fita,


Film ɗin yana ɗauke da jarumai irin su: Rekha, Rajinikanth, Prem Chopra da dai sauransu, Kuma wannan Film shine kaɗai guda ɗaya Tilo wanda jaruma Rekha da Rajinikanth suka taka rawa tare,



BAPPI LAHIRI shine ya bada kiɗan waƙoƙin cikin sa, Sai kuma Lata Mangeshkar, Amit Kumar, Muhammad Aziz, Kavita Krishnamurthy, Sudesh Bhosale da shi kansa Bappi Lahiri ɗin suka yi wskonl Waƙoƙin baki daya.

@AyƘoƘi

SUNIL SHETTY YA RAGE AMFANI DA TUMATUR TUNDA YAYI TSADA

SUNIL SHETTY YA RAGE AMFANI DA TUMATUR TUNDA YAYI TSADA




Babban Jarumi Sunil Shetty Yace Mutane suna Ganin Cewa Tunda Shi Babban Tauraro ne a Bollywood Bazai damu da irin tsadar kayan miya ba to ba haka bane shima mutum ne Dole yayi maganin duk Abinda zai bashi matsala don haka shi ya rage amfani da tumatur cikin Abincin sa idan za ayi masa miya ko wani Abu da ya Danganci haka Daga Lokacin da yaga kuɗinsa yana hau hawa. Ana Siyar da tumatur Akan Kuɗi rupees 120 Zuwa 15O a duk kg ɗaya Cikin kasuwar da Ake masa siyayya ta kasar India.

#AbbaIndiaDala

ME YA JAWO FAƊUWAR SHIRIN KISI KA BHAI KISI KI JAAN?

#Kisi Ka Bhai... Kisi Ki Jaan


Duk yadda film ɗin #Sallu_Bhai ya kai da yin kyau to dole sai ya ɓatama rai a abubuwa guda 3

Na farko: #RAWA kwata-kwata bai iya rawa ba rawarsa ɓatama rai kawai zatayi.

Na biyu: #SOYAYYA ya kamata ya gane ya girma, soyayya bata masa kyau kwata-kwata saboda shekaru da kuma girman jiki, duk da dama can ba wani talent bane akan soyayya.

Na uku: #TUƁE_RIGA kullum cikin cire rige yake tun yana burgeka har sai ya fara ɓatama rai, mutum bashi da aiki sai nunawa mutane damatse 😒😔🥴

Amma gaskiya #KBKJ yayi kyau kuyi ƙoƙari ku kalleshi, Film ɗin yayimin kyau shiyasa na kasa gano dalilin faɗuwar film ɗin nan a kasuwancinsa, sai Kuma na tuna su ƴan addinin Hindu ba kyan labari suke dubawa ba, burunsu kawai ai ta yabon gumakansu, haka sukayi tsammani a Adpurish na Prabhas daya fita a kwanakin nan, shikuma bai yabi gumakan nasu da yawa ba karshe suka ƙauracewa kallon film ɗin Wanda hakan ya jawo masa faɗuwa, Kuma suka dinga kira da hukuma ta Hana haska film ɗin a cinema.

Saboda haka Ko da film ya faɗi a kasuwancinsa to kuyi ƙoƙari ku kalli ba mamaki ya birgeku.

✍️ #Ameenu_Sharada

DALILIN MUSULUNTAR DHARMENDRA




Tsohon Jarumi da a Lokacinsa Akayi Hasashen yafi duk Jarumai Kyau Watau Dharmendra Ya Auri Parkash Kaur a 1954 yana da Shekaru 19 ya Fara Samun ɗan farko Jarumi Sunny Deol a 1956 Lokacin yana da Shekaru 21, kenan tazarar Shekarun Uba da ɗa a Nan 21 Watau yanzu Shekarun Dharmendra 87 shi Kuma ɗansa na Fari Shekaru 66 Sannan me binsa Bobby Deol Shekarunsa 54 tazarar Sunny da Bobby Deol Shekaru 12.
Dharmendra Matansa Biyu Da Mahaifiyar Su Sunny Watau Parkash Kaur da Tsowuwar Jaruma Hema Malini Da ya Aura a 1980 Lokacin da Suka Kamu da Soyayyar Juna Kuma
Gashi Addinin Hindu be Aminta da Haɗa Mata Biyu Wannan Dalilun Yasa Jarumi Dharmendra ya Musulinta ya Auri Hema Kuma Har Yanzu Matansa Guda Biyu Suna Nan tare Dashi.

#AbbaIndiaDala

KIARA ADVANI: SAI DA NA AURI SIDDHARTH MALHOTRA NA SAMU SOYAYYAR GASKIYA



Jaruma Kiara Advani Mata Ga Jarumi Siddharth Malhotra Tace Lallai tana da Sa'a a Rayuwa domin se da ta Auri Siddharth tasan ta samu soyayyar gaskiya ga Abinda ta faɗa da Hindi ɗin "Abhi abhi meri shaadi Hui hai. Yeh ek love marriage tha. So naturally, main toh believe karti hoon (in true love) 

#AbbaIndiaDala

KASUWANCIN ADIPURUSH A KWANAKI GOMA



#Adipurush Nizam 10 days (All versions)

Gross - 54.2 Cr

Share - 35.88 Cr (including GST)

Share includes distributors 3D commission. Gross doesn't include 3D charges.

Break even - 51.5 Cr

A huge loss venture

Gwari Gwari da Hausa

Abinda aka samu a yankin Nizam dukkan versions da aka saki kama daga hindi, telugu, Tamil da sauran - 54.2cr

Daga cikin wannan 54.2cr din, dillalan da suka yi dillanci na Adipursh a yankin Nizam sun samu 35.88cr

Abinda dillalan ke bukatar samu dan maida kudin da suka saya na dillanci - 51.5cr

Dillalan da suka yi dillanci na Adipursh a yankin Nizam sunyi Asara ta kusan 16cr

AKK 

MANOJ BAJPAYE: MATATA TA HANA NI FITOWA A WASU FINA-FINAI



Jarumi Manoj bajpaye Yace Matarsa ta hana shi fitowa cikin wasu Fina-finai.
Jarumin yace ta nemi Alfarma tare da bashi izinin daina fitowa Cikin film domin kuɗi kawai.
Saboda ta kalli wani film ɗinsa taga Abin a wulaqance da cin mutumci.
Tace masa sufa ba wai kuɗi sukeso ido rufe ba da zai rinka karɓar kowane Film ai mutunci ma wani Abu ne da Yakamata mutum ya rinka dubawa.

#AbbaIndiaDala

Fassarar Kalaman Fim Ɗin Kabhi Kabhie


Fassarar Kalaman Fim Ɗin Kabhi Kabhie

Shekarar Fita - 1976

• Aapne kabhi apni aankhen dekhi hai? ... jahan dekhti hai ek rishta kayam kar leti hai

Shin kin taɓa kallon idanuwanki kuwa?... Duk inda suka kai duba, alaƙa suke ginawa. 

 Amitabh Bachchan

• Kabhi raste mein mil jao toh katrakar guzar jana ... hum mein is tarah takna jaise pechana nahi tumne ... hamara zikr jab aaye toh yun anjaan ban jana ... ki jaise naam sunkar bhi hum mein jana nahi tumne

Idan ki ka ganni a hanya to kauce ki wuce... Ki kalle ni kamar ba ki san ni ba... Idan kuwa har sunana ya fito daga bakinki cikin rashin sani... Ki ɗauka cewa ba ki sanni ba ko da kin ji sunana. 

 Amitabh Bachchan

• Tera haath, haath mein ho agar ... toh safar hi asle-hayaat ha i ... mere har kadam pe hai manzilein ... tera pyar gar mere saath hai

Da ace hannunki nawa ne... To tafiyar ita kanta rayuwa ce... Kuma akwai bigire a kowane takuna... Idan soyayyarki ta kasance tare da ni. 

Amitabh Bachchan

• Mere dil ka woh hissa ... kambakht mera kab tha

A wannnan ɓangaren na zuciyata... Jahannama ba tawa bace. 

 Amitabh Bachchan

• Meri baat ka meri humnafas, tu jawab de ki na de mujhe ... teri ek chup mein joh hai chupi, woh hazaar baaton ki baat hai

Ya ke rayuwata ko da ba ki bani amsar tambaya ta ba... Shirun da ke ɓoye tare da ke ya bani amsar tambayoyi dubu. 

 Amitabh Bachchan

• Meri zindagi ka har ek pal, tere husn se hai judha hua ... tere honth thirke toh subah hai, teri zulf bhikre toh raat hai

Kowane lokaci na rayuwata, manne yake da jikinki... Duk sanda laɓɓanki suka motsa to safiya ce, duk sanda kika buɗe gashinki kuma dare ne. 

Amitabh Bachchan

• Is duniya mein aadmi insaan ban jaye ... toh bahut badi b aa t hai

• A wannan Duniyar, idan mutum ya zama ɗan adam... Ba ƙaramin al'amari bane. 

Shashi Kapoor

• Tum insaan ke roop mein devta ho ... yah devta ke roop mein insaan

Shin kai ubangiji ne a siffar mutane... Ko kuma mutum ne a siffar ubangiji? 

Rakhee Gulzar

• Zindagi chand sawaal aur kuch jawaab hi toh bankar reh jaati hai

A ƙarshe rayuwa kan zamo wasu 'yan tambayoyi ne kawai da wasu amsoshi. 

 Rakhee Gulzar

• Main zara romantic kisam ka aadmi hoon ... s ha adi ke baad ishq karna toh chhod diya hai ... is liye biwi se romance karke kaam chala leta hoon

Ni mutum ne mai soyayya kaɗan... Kuma na daina kula mata tun da na yi aure... Hakan ya sa na ke rayuwata ta hanyar kula matata. 

 Shashi Kapoor 

• Aap sooch kuch aur rahen hain ... pooch kuch aur rahen hain

Abin da kike tunani daban... Abin da kike tambaya daban. 

 Amitabh Bachchan