Shahararriyar Jaruma da ta fara Mamaye Bollywood Saboda Kwarewa da Sanin Aiki ta Ƙara Nutsawa Hollywood, Jarumar da ta karɓi Sarauniyar Kyau ta Duniya a 2000 watau Priyanka Chopra Yau 18, ga Watan July ta Cika Shekaru 41 An taɓa tambayar ta Akan Ɓoyayyun Al'amura game da ita tace Acikin su Shine Ita tana da matuqar son zaman gida ( Homebody) domin tana son Rayuwa Cikin Iyali Kuma Tana Amfani da Damar ta basu lokaci Har Yanzu duk lokacin da ta samu faraga, Sannan tace ta tsani yin Party Kwata-kwata Gaba ɗaya tsarin ta da tunanin ta irin na Mutanan dah ne watau can shekarun baya irin wannan zai bawa Mutane mamaki saboda yanda Ake ganinta Cikin Fina-finai musamman na farko-farko wajen 2004 irinsu Andaz da kismat Amma ita wannan Kawai Aiki ne ba haka take ba tasan da yawa Zasuyi mamaki sedai wannan shine gaskiya kuma shine a ran ta a cewar wannan Jaruma kenan yayin da Filmfare sukayi tattaunawa da ita.
#AbbaIndiaDala