FASSARAR WAƘAR ZINDA BANDA HO

FASSARAR WAƘAR ZINDA BANDA HO 

* Sunan Waƙa: Zinda Banda Ho

* Sunan Shiri: Jawan

* Shekarar Fita: 2023

* Harshe: Hindi/Hausa 

* Rerawa: Anirudh Ravichander

* Rubutawa: Irshad Kamil

* Haɗa Sauti: Anirudh Ravichander

* Tauraro: Nayanthara da Shah Rukh Khan

* Fassarawa: Haiman Raees 

* Asoolon Par Jahan Aanch Aaye Takrana Zaroori Hai

- Yayin da kimar mutum ta shiga haɗari, dole ne ya maida martani. 

* Banda Zinda Ho Toh Zinda Nazar Aana Zaroori Hai

- In dai har mutum na raye, to dole ne ya nuna alamar yana raye. 

* Banda Ho To Zinda Ho

- Matuƙar mutum na so ya wanzu, to dole ya rayu matuƙar iyawarsa. 

* Dil Nachda Re, Dil Nachda

- Zuciya na juyawa, zuciya na juyawa. 

* Khulke Thirakne Se Bachna

- In za ka iya, ka hanu ga barin zumuɗin takawa. 

* Dekh!

  - Kalli! 

* Himmat Se Nacho Thirak Thirak Yaro

- Abokaina ku himmatu da rawa cikin shauƙi. 

* Dharti Hilla Do Thirak Thirak Re

- Ku girgiza ƙasa da rawar ku. 

* Mati Ka Badal Ufak Ufak Jaye, Ambar Jhuka Do Thirak Thirak Re

- Ku jawo giza-gizai su yi rawa tare da ku, ku jawo samaniya ta yi rawa tare da ku. 

* Ladak Madak Banda Ho! Khadak Dalak Banda Ho!

- Dole ne mutum ya bunƙasa, dole ne mutum ya ci gaba. 

* Fikar Fikar Zinda Ho! Banda Ho Zinda Ho!

- Dole ne mutum ya damu! Dole ne alfaharin mutum ya zama yana nan lafiya. 

* Tabad Todak Banda Ho! Falak Talak Banda Ho!

- Dole ne mutum ya zama jarumi! Dole ne tunanin mutum ya girmama kamar sararin samaniya. 

* Sabar Shukar Zinda Ho! Banda Ho Zinda Ho!

- Dole ne mutum ya yi haƙuri! Dole ne alfaharin mutum ya zama yana nan lafiya.  

* Tadpan Rangare Dhadkan Angare

Muradansa dole su zamo wanzazzu. Bugun zuciyarsa dole dole ya dinga tashi da wuta. 

* Tan Mann Gangare Zinda Banda Ho

- Zuciyarsa da jikinsa dole su zama tsarkaka kamar ruwan kogin Ganga. 

* Arre Tan Mann Gangare Zinda Banda Ho

- Zuciyarsa da jikinsa dole su zama tsarkaka kamar ruwan kogin Ganga. 

* Jhatpat Jhoomar Ghoomar Jhanjhar Baje Re

- Sarƙar ƙafa na ci gaba da kaɗawa ba ƙaƙƙautawa. 

* Pairon Thale Dhuan Chale

- Wuta na tashi a ƙasan ƙafafu. 

* Jo Na Soche! Jo Na Nache!

- Wanda ba ya tunani, baya yin rawa. 

* Ab Na Rukna Chalne De!

- Ka da ku dakata yanzu, bar waƙar ta ci gaba da tashi. 

* Jhatpat Jhoomar Ghoomar Jhanjhar Baje Re

- Sarƙar ƙafa na ci gaba da kaɗawa ba ƙaƙƙautawa. 

* Koyi Hamare Jaisa Kahan

- Ina mutane suka fi son wanzuwa ne a duniyar nan? 

* Hum Na Jahan Se Humse Jahan

- Mu ba mallakin duniya ba ce, sai dai ita duniyar ce mallakinmu. 

* Jee Mein Jashan Mein Aahat Chale

- Akwai ƙarar bugawa a zukatanmu da farincikinmu. 

* Apne Hunar Mein Chahat Chale

- Akwai matsananciyar soyayya ga ƙwarewarmu. 

* Thirak Thirak Thakna Kyun! Tunak Tunak Takna Kyun!

- Me zai sa ka gaji yayin da kake rawa? Me zai sa mu yi ta kalle-kalle yayin da muke cashewa? 

* Jhijhak Jhijhak Jakhna Kyun! Banda Ho Zinda Ho!

- Me zai sa mu yi jinkiri? Dole ne fa mutum ya more rayuwarsa. 

* Tabad Todak Banda Ho! Falak Talak Banda Ho!

- Dole ne mutum ya zama jarumi! Dole ne tunanin mutum ya girmama kamar sararin samaniya. 

* Fikar Fikar Zinda Ho! Banda Ho Zinda Ho!

- Dole ne mutum ya damu! Dole ne alfaharin mutum ya zama yana nan lafiya. 

* Jeena Jane Jo! Dil Ki Mane Jo!

- Rayayyen mutum shi ne wanda ya fahimci yadda ake rayuwa, wanda ke sauraron zuciyarsa. 

* Kar De Thane Jo Zinda Banda Ho

- Wanda ke bin zaɓinsa. 

* Arre Kar De Thane Jo Zinda Banda Ho

- Rayayyen mutum shi ne wanda ke yanke hukuncinsa da kansa. 

* Jhatpat Jhoomar Ghoomar Jhanjhar Baje Re

- Sarƙar ƙafa na ci gaba da kaɗawa ba ƙaƙƙautawa. 

* Pairon Thale Dhuan Chale

- Wuta na tashi a ƙasan ƙafafu. 

* Jo Na Soche! Jo Na Nache!

- Wanda ba ya tunani, baya yin rawa. 

* Ab Na Rukna Chalne De!

- Ka da ku dakata yanzu, bar waƙar ta ci gaba da tashi. 

* Jhatpat Jhoomar Ghoomar Jhanjhar Baje Re

- Sarƙar ƙafa na ci gaba da kaɗawa ba ƙaƙƙautawa.

Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com
#haimanraees #Jawan600cr

Comments