SUNIL SHETTY YA RAGE AMFANI DA TUMATUR TUNDA YAYI TSADA
Babban Jarumi Sunil Shetty Yace Mutane suna Ganin Cewa Tunda Shi Babban Tauraro ne a Bollywood Bazai damu da irin tsadar kayan miya ba to ba haka bane shima mutum ne Dole yayi maganin duk Abinda zai bashi matsala don haka shi ya rage amfani da tumatur cikin Abincin sa idan za ayi masa miya ko wani Abu da ya Danganci haka Daga Lokacin da yaga kuɗinsa yana hau hawa. Ana Siyar da tumatur Akan Kuɗi rupees 120 Zuwa 15O a duk kg ɗaya Cikin kasuwar da Ake masa siyayya ta kasar India.
#AbbaIndiaDala