SHIN KAMANCECENIYAR INDIA DA NIGERIA A KO INA TAKE?
Yayin da Watan da Mukayi Bankwana dashi Ana daf da fara cin kasuwar Film ɗin Babban Jarumi Sunny Deol Me Taken Gadar2 An Samu Labarin Bank of Baroda ( BoB) ta tabbatar da Zatayi Gwanjon Gidan Sunny Deol da take Binsa Kimanin 56cr.
Abin Jan Hankali anan Shine Duk da Sunny ya daina fitowa a Fina-finai kafin Wannan Gadar2 ɗin Amma Fa Zaɓaɓɓen Ɗan Majalisa ne na Birnin Gurdaspur Sama da Shekaru 4 Kuma Har Yanzu Shine a Wannan Matsayin Amma Hakan Be Saka Tun Wuri yayi wadaqa da Kuɗin Al'ummar sa ba Domin Biyan Wasu kuɗaɗen Kuma Bugu da Ƙari Jam'iyyar sa take mulkar Ƙasar Amma duk da Haka ba a Samu Labarin Umarni Daga Sama Akan Kar A yiwa Wannan Ɗan Majilisar Haka ba.
Sau da Yawa Ana Kwatanta Kamanceceniyar India da Nigeria Wajen Wasu Al'adu da Kuma Tsarin Siyasa da Akeyi.
#AbbaIndiaDala