FASSARAR WAƘAR CHALEYA

FASSARAR WAƘAR CHALEYA 


* Sunan Waƙa: Chaleya

* Sunan Shiri: Jawan

* Shekarar Fita: 2023

* Harshe: Hindi/Hausa 

* Rerawa: Arijit Singh da Shilpa Rao

* Rubutawa: Kumaar

* Haɗa Sauti: Anirudh Ravichander

* Taurari: Nayanthara da Shah Rukh Khan

* Fassarawa: Haiman Raees 



-* Ishq Mein Dil Bana Hai, Ishq Mein Dil Fanna Hai Ho

 - So shi ne mahaɗin zuciya, zuciya ta kamu da ƙauna. 

-* Mita De Ya Bana De, Maine Tujhko Chuna Hai Ho Ho

- Ko ki karya ni ko ki haɗe ni, ke na zaɓa. 

-* Tere Sare Rang Odhke Dhang Odh Ke

- Na kalantu cikin kalolinki, ina kwaikwayon hanyoyinki. 

-* Tera Hua Main Sabko Chhodke Ho Ho Ho

- Zan bar kowa a baya, na zamo naki. 

-* Ishq Ni Karna Nap Tolke Raz Khol Ke

- Ba na so in ƙaunace a ƙarƙashin iyakancewa.

-* Aaya Hoon Main Sabko Bolke Ho

- Tuni na faɗa wa kowa. 

-* Oh Main Tan Chaleya Teri Oar Tera Chaleya Hai Zor

- Gani nan tafe gare ki. (saboda) Kin tsafance ni. 

-* Tera Hoya Main Yar Ve Bhuleya Ae Sansar Ve

- Masoyiya! Na zamo naki, na manta da dukka duniya. 

-* Chaleya Teri Oar Tera Chaleya Hai Zor

- Jan hankalinki yana jawo ni gare ki. 

-* Tera Hoya Main Yar Ve Bhuleya Ae Sansar Ve

- Na zamo naki masoyiya, na bar dukkan duniya. 

-* Jag Tere Liye Chhodiya, Dil Tere Sang Jodiya

- Na ƙyale dukkan duniya, na ba ki zuciyata. 

-* Ab Tera Main Toh Ho Gaya, Pake Tujhe Main Kho Gaya

- Tun da na same ki, na rasa kaina yanzu da na zamo naki. 

-* Jag Tere Liye Chhodiya, Dil Tere Sang Jodiya

- Na ƙyale dukkan duniya, na ba ki zuciyata. 

-* Ab Tera Main Toh Ho Gaya, Pake Tujhe Main Kho Gaya, Kho Gaya Han

- Na rasa kaina, tun da yanzu da na zamo naki. 

+* Ishq Mein Dil Bana Hai, Ishq Mein Dil Fanna Hai Ho, Ho Ho Ho

- Zuciya ta faɗa soyayya, ƙauna ce ta ƙirƙire ta. 

+* Hansa De Ya Rula De, Maine Tujhko Chuna Hai Oh, Oh Ho Ho

- Ko ka sa ni dariya ko ka sa ni kuka, ni dai kai na zaɓa. 

+* Duniya Kehti Ishq Bhool Hai Befizool Hai

- Duniya na gardamar cewa so ba shi da wata ma'ana. 

+* Humko Toh Dil Se Kubool Hai Oh Oh Ho Ho

- Duk da haka na rungume shi hannu bibbiyu. 

+* Tujhme Dikhta Rabb Ka Noor Hai Ek Suroor Hai

- Abin akwai ƙayatarwa ganin ubangiji a tare da kai. 

+* Tu Hai Apna Yeh Guroor Hai Oh Oh Oh Ho

- Na darajtu da ka zamo nawa. 

+* Ve Main Tan Chaliya Teri Oar Tera Chaleya Hai Zor

Gani nan tafe gare ka. (saboda) Ka tsafance ni. 

+* Teri Hoyi Main Yar Ve Bhuleya Ae Sansar Ve

Masoyi! Na zamo naka, na manta da dukka duniya. 

+* Chaleya Teri Oar Tera Chaleya Hai Zor

- Gani nan tafe gareka saboda ka damƙe ni a damƙar ka. 

+* Teri Hoyi Main Yar Ve Bhuleya Ae Sansar Ve

- Na zamo naka masoyi, na manta da dukkan duniya. 

-* Tu Ishq-e-Khwab Khwab Sa Hai, Mera Behisab Sa Hai

- Ke tamkar so ne a mafarki, ke tawa ce ba tare da iyakancewa ba. 

-* Tere Lafz Choom Loon Main, Urdu Ki Kitab Sa Hai

- Zan sumbaci kalamanki, ke abar soyuwa ce tamkar littafin waƙen Urdu. 

+* Tu Ishq-e-Khwab Khwab Sa Hai, Mera Behisab Sa Hai

- Ke tamkar so ne a mafarki, ke tawa ce ba tare da iyakancewa ba

+* Tere Lafz Choom Loon Main, Urdu Ki Kitab Sa Hai

- Kina da wani irin zaƙi irin na kundin waƙen Urdu, kuma zan sumbaci kalamanki. 

-* Jag Tere Liye Chhodiya, Dil Tere Sang Jodiya

- Na ƙyale dukkan duniya, na ba ki zuciyata. 

-* Dil Tere Sang Jodiya, Ishq Mein Dil Fanna Hai Ho Ho

- Na ba ki zuciyata, zuciyata ta kamu da ƙaunarki. 

-* Ab Tera Main Toh Ho Gaya, Pake Tujhe Main Kho Gaya,

- Na rasa kaina a ƙoƙarin zamowa naki. 

-* Jag Tere Liye Chhodiya, Dil Tere Sang Jodiya

- Na ƙyale dukkan duniya, na ba ki zuciyata. 

-* Dil Tere Sang Jodiya, Ishq Mein Dil Fanna Hai Ho Ho

- Na ba ki zuciyata, zuciyata ta kamu da ƙaunarki. 

-* Pake Tujhe Main Kho Gaya, Kho Gaya Han

- Na rasa kaina tun da na same ki. 


Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com
#haimanraees #Jawan600cr
 

Comments