SALAAM NAMASTE
~Shima dai wannan Film mai suna Salaam Namaste wanda ya rabauta da zaƙaƙan waƙoƙi ya cika shekaru 18 da fitar sa, inda aka sake shi a shekarar 2005, inda ya zamo Film na farko da aka ɗauke shi a Austaraliya,
~Labari ne dai na wasu matasa guda biyu Nick Saif Ali Khan da Ambar Preity Zinta wadanda suka yanke shawarar barin iyayensu domin suyi rayuwar su ta kashin kansu mai cike da yankin a ganin su, inda suka koma yankin *Melbourne* wato ɗaya daga cikin manyan biranen yankin Australia domin ayi Rayuwar uwa ba ƙwaɓa, Aditya Chopra shine ya shirya wannan Film yayin ta Siddharth Anand ya bada umarni,
~Salaam Namaste shine Film na huɗu mafi kawo kuɗi a shekarar 2005, Haka ita ma jarumar ciki wato Preity Zinta ta rabauta da kyautar Jarumar jarumai a Filmfare Awards, IIFA Awards, Star Screen Awards da kuma Zee Cine, inda mawaƙa Irin su: Shaan, Suno Nigam, Kunal Ganjawala da Vasundhara Das suka bada waƙoƙin cikin sa har guda 7 duk zaƙaƙa kuma shahararru kamar irin su: My Dil Goes Mmmm da kuma waƙar ta tazo da sunan Film ɗin wato Salaam Namaste, sai Vishal–Shekhar da suka bada kiɗan Jaideep Sahni ya rubuta su.@AyƘoƘi.