10-09-1993 --- 30 YEARS OF GARDISH
~A irin wannan rana aka fitar da Film ɗin Gardish na Producer Director Priyadarshan inda yake cika shekaru 30 cif,
~Gardish yana ɗauke da jarumai irin su: Shammi Kapoor, Jackie Shroff, Amrish Puri, Aishwarya, Farida Jalal, Dimple Kapadia dss, kuma wannan Film shine na farko wanda Amrish Puri da Farida Jalal suka fito a matsayin mata da miji, Bugu da ƙari kuma dai shine Film ɗin jarumi Mukesh Rishi na farko a Hindi Cinema,
~Javed Akhtar shine ya rubuta waƙoƙin wannan Film yayin da Rd Burman ya bada kiɗan su, sai mawaƙan da suka Baje basirar su a ciki da suka haɗa da: Asha Bhosle, Malabar Gopalan Sreekumar da kuma mawaƙi SBP wanda cikakken sunan sa shine "Sripathi Panditaradhyula Balasubrahmanyam" cikin waƙoƙin har da "Rang Rangeeli Raat Gaaye" da kuma "Yeh Mera Dil To Pagal Hai".@AyƘoƘi.