Duk yadda film ɗin #Sallu_Bhai ya kai da yin kyau to dole sai ya ɓatama rai a abubuwa guda 3
Na farko: #RAWA kwata-kwata bai iya rawa ba rawarsa ɓatama rai kawai zatayi.
Na biyu: #SOYAYYA ya kamata ya gane ya girma, soyayya bata masa kyau kwata-kwata saboda shekaru da kuma girman jiki, duk da dama can ba wani talent bane akan soyayya.
Na uku: #TUƁE_RIGA kullum cikin cire rige yake tun yana burgeka har sai ya fara ɓatama rai, mutum bashi da aiki sai nunawa mutane damatse 😒😔🥴
Amma gaskiya #KBKJ yayi kyau kuyi ƙoƙari ku kalleshi, Film ɗin yayimin kyau shiyasa na kasa gano dalilin faɗuwar film ɗin nan a kasuwancinsa, sai Kuma na tuna su ƴan addinin Hindu ba kyan labari suke dubawa ba, burunsu kawai ai ta yabon gumakansu, haka sukayi tsammani a Adpurish na Prabhas daya fita a kwanakin nan, shikuma bai yabi gumakan nasu da yawa ba karshe suka ƙauracewa kallon film ɗin Wanda hakan ya jawo masa faɗuwa, Kuma suka dinga kira da hukuma ta Hana haska film ɗin a cinema.
Saboda haka Ko da film ya faɗi a kasuwancinsa to kuyi ƙoƙari ku kalli ba mamaki ya birgeku.
✍️ #Ameenu_Sharada