TATTAUNAWA DA JARUMA SONAKSHI SINHA
KIN KASANCE MACE MAI MATUKAR KWARIN GWIWA A BAYA BAYAN NAN TA HANYAR KUTSAWA CIKIN SABBIN ABUBUWA KO KUMA BARIN KAFAFEN SADARWA WATO SOCIAL MEDIA. KIN KARA NUNA MUHIMMANCI NA AIKATA HAKAN GA DABI'UN KI...
.
SONAKSHI SINHA - Ban taba kasancewa irin macen da ke son yin abubuwa dan jan hankali ko burge wasu ba. Na kan yi abu ne da nake tunanin shine ya kamata kuma suka dace da raayina. Saboda haka idan kana ganin cewa ni mace ce mai matukar kwarin gwiwa, to hakan ya faru ne saboda nayi wasu abubuwa da raayi na suka ayyana mini su ne daidai..
Ni mace ce mai son mai son sirri, kuma ina matukar son aiki na kamar yadda nake son sirri, se ya kasance akwai karo da juna tsakanin son aikin nawa da kuma son sirri. Ma'ana dai yanayin aiki na baya bani damar samun kebancewa akan kai na. Saboda haka lokacin da zan samar wa kaina wanda ya kasance nawa ni kadai yayi karanci. Se nake adana wannan dan lokacin dana ke samu dan kaina sosai.
Irin hakan ne yasa bayan wasu lokuta na yanke shawarar barin kafa ta sadarwa wato social media.
********************************************
ME YA SA KIKA RUFE KAFAR SADARWAR KI TA TWITTER?
SONAKSHI SINHA - Lokacin da na fara kokarin sanin mu'amala ta kafar sadarwa, abin ya kasance me kayatarwa da ban sha'awa, musamman da yake sabon abu ga kusan kowa. Ta hakan zaka kara samun yabo daga mutanen da suke jin dadin aikin ka kwatsam bayan wani lokaci se kafar ta rasa karsashi da tafarkin ta. Mutane suka rasa dabi'a ta kwarai a kafar sadarwa, kowane rukuni na mutane na iya kaiwa gare ka ba tare da samun damar tantance su ba... Matukar ba'a yi wani abu a kai ba, hukuncin da zaka yanke mafi dacewa shine ka cire kan ka daga tsarin,.
Wannan shine abinda nayi. Kuma babu wata matsala da hakan ya kawo, tunda be taba min aiki ba. Hasali ma zan iya cewa barin kafar sadarwa ya samar min da nutsuwa da kwanciyar hankali tunda bana ganin suka da aibatawa da marasa dabi'u masu kyau a kafar sadarwa zasu yi maka... A wajena, Hukunci ne da na yanke a daidai lokacin da ya kamata
********************************************
A BAYA BAYAN NAN KI SAMAR DA WURI DA YA SHAFI SANA'A TA FASAHA MAI SUNA HOUSE OF OPPORTUNITIES.. TA YA HAKAN YA KASANCE??
SONAKSHI SINHA - Fasaha wani abu ne da nake maida hankali na akai idan ina neman samun natsuwa. Dama ce a gare ta fita daga cikin rikita rikitar rayuwa.
A duk lokacin da nake son dauke hankali na daga rikicin duniyar nan, kawai zuwa nake nayi fenti. A Yan kwanakin nan na kasance ina yawan yin sa ma. Ina jin iko akan wannan fasaha na fenti kuma bana son rabuwa da shi. Zan nuna maka dakin da nake fentin. Zaka ga takalma na sauki a kwance a dakin.
Ni da kanina muka zauna muka shawarta kafin mu zo da wannan tunanin. Damuwar shine mawuyaci ne kai tsaye ka kutsa cikin wani sabon al'amari da ya kasance sabo ne a gare ka. Na kasance sananniyar jaruma, amma a fage na fasaha se na zamto tamkar wacce bata san alkibla ba. Na rasa gun zuwa, na rasa wanda zan tunkara, na rasa ya zanyi..
Daga bisani muka zo da shawarar mu bada dama ga masu sha'awar shiga fage na fasaha kuma suke son kaiwa wani matsayi na daukaka. Ta yiwu daga wani background na rayuwa kake, ko kuma ka kafu a harkar da kake yi, abinda ake bukata daga gare ka kawai shine aiki me kyau da inganci, za a baka dama don nuna me kazo dashi.
Nima a kan kaina na ga hakan yayi ma'ana kuma zan iya kasancewa a fagen duk da cewa ban kafu ba, Ina yin fenti saboda ina son fenti sosai kuma ina da yakinin akwai dama ta samun kasuwa ga irin sana'a ta.. Kaine zaka tsara al'amuran ka yadda kake son su kasance, kai ne zaka samar wa kan ka damarmaki, kuma a yayin hakan idan har ka taimaki wasu, to al'amura sun yi tafi yadda ake so..
TO BE CONTINUED...
AKK..