TATTAUNAWA DA JARUMA SONAKSHI SINHA
CI GABA...
****************************************************************************************
ABIN FARIN CIKI NE GANIN IRIN KARƁA DA AKAI MASA, KO?
Kwarai kuwa. Akwai farin ciki mai gamsarwa, kamar yadda nace ne, wani bangare ne da babu isasshen ilimi akan sa, baka san me zaka tarar ba, ina ze zama makomar sa, yadda ze kasance,
Amma irin karbuwa da abin ya samu da sharhi me kyau daga bakunan mutane, abu ne mai matukar dadi. Nima na saida fenti na na farko, na kuma yi amfani da abinda nake samu a aikin don yin taimako nan da can.. Ko a lokacin lockdown na yi dan yi wasu zanunnuka, sannan na saida wasu daga fenti na nayi taimako da shi.. Wannan ma wani abu ne na farin ciki gare ni,
Amma idan ka saida fentin naka ma ka samu kudi shima ae abu ne me dadi ko, domin babbar alama ce ta nuna cewa ka samu sana'a me kyau bangaren fasaha. Naji dadi da ya kasance zan iya yiwa kaina haka
****************************************************************************************
ZAKI IYA KAMANTA SHI TA KOWACCE FUSKA DA IRIN KUDIN DA KIKA SAMU A FILM DIN KI NA FARKO?
SONAKSHI SINHA - Sosai ma. Da yake abu ne da nake yi tun ina karama, hakan ya karawa abin armashi. Kuma Naji shi wani daban haka
****************************************************************************************
KINA DA WANI SHAKKU AKAN SHIGA TSARI NA MANHAJAR OTTY?
SONAKSHI SINHA - A gaskiya bazan ce haka ba domin OTT ya kunshi abubuwa na mamaki da kayatarwa. Na samu damar yin aiki da REEMA KATGI a karo na farko Haka ma EXCEL. Ban taba aiki dasu ba. Kuma irin cinema nasu yana burge ni, saboda haka sha'awar aiki dasu ya zama abu me sauki gare ni.
Na kwadaitu da aiki a cikin wannan tawagar, kuma script din nasu ya tsaru sosai, Character dina mai kyau, Na zabi na karbe shi, Babu wani dalili da zan ce A'a,.. To me yasa ma zan ki karɓa? Saboda series ne ba Movie ba?
****************************************************************************************
YAYA ZAKI BADA LABARIN IRIN KARUWA TA ILIMI DA KIKA SAMU A FAGEN OTT?
SONAKSHI SINHA - Ya kasance tamkar yin fina finai uku a lokaci guda, Amma akwai nishadi Fa. Nishandin ma na daban ne. Kamar de gashi a series, masu bada umarnin sun haura mutum daya. Muna da masu bada umarni guda biyu, wato REEMA KATGI da RUCHIKA OBEROI.
Akwai lokuta da suke bani kariya kamar ace, kin gama da SONAKSHI da safe saboda haka kyaleta ta koma gun aiki.. Ni kuma na rike baki ina ta'ajibi na cewa mene kuma haka!!! To kamar yadda nace ne sabon abu ne gare ni, kuma yana nisahadantar dani.
Akwai kayatarwa kayi aiki da da me bada umarni da safe wanda salon yake daban sannan da yamma kayi aiki mai bada da ya sha bamban to kowace fuska da na safiyar kuma abu mafi ban nishadi shine yadda masu bada umarni guda biyun zasu hade ayyukan da suka yi a lokuta daban zuwa waje guda.. Kuma ya zama abu guda...
****************************************************************************************
TO BE CONTINUED...
AKK