ZURFAFA SOYAYYA GA JARUMAN FINA-FINAI
Bissmillahir Rahmanir Raheem.
Assalamu alaikum Warahmatullah Wabarakatuhu.
'Yan uwa musulmai ina yi mana barka da wannan rana ta juma'a, Allah ya amsa mana ibadunmu kuma ya sada mu da dukkan wani alheri da ke cikin wannan yini, sannan ya kare mu daga dukkan sharrorin da ke cikinsa. Ya Allah ka nuna mana ƙarshen musibar COVID19 a duniya baki ɗaya.
Bayan haka, ba ɓoyayyen abu bane cewa jaruman fina-finai musamman na ƙasar Indiya sun samu karɓuwa sosai a ƙasar Nijeriya, musamman ma a arewacin ƙasar. Dalilin da zai tabbatar maka da hakan shi ne, abu ne mai matuƙar wahala a yau ka samu wani gida a arewacin Nijeriya da babu masoyin fina-finan Indiya a cikin wannan gida. Wannan sai ya haifar da ƙaruwar ƙarfin soyayyar jaruman fina-finan a zukatan jama'a, har ta kai ga mata suna kwaikwayon jarumai mata ta kowace fuska yayin da su ma mazan ke kwaikwayon jaruman ta kowace fuska. A ƙarƙashin haka sai abota, zumunci, barkwanci, soyayya da auratayya ta shigo cikin irin tarayyar da masoya jarumai da kuma harkar Indiya ke yi baki ɗaya.
Amma in da gizo ke saƙar shi ne: masifar da irin soyayyar hauka da indiyawa da mutanen wasu ƙasashe kamar Jamus suke yi wa waɗannan jarumai ne ta tunkaro mu, domin a yau an samu waɗanda har ridda suna yi cikin Kalaman da suke furtawa dangane da jarumansu, sun sani ko ba su sani ba wannan kuma Allah shi ne mafi sani. Hakan yasa ƙiyayya, hamayya, zage-zage, cin mutunci da aibata juna duk sai suka shigo cikin lamarin.
Haba 'yan uwana, ta yaya za mu bari irin wannan ɓaraka ta shigo cikinmu? Me zai sa ba za mu rage irin wannan muguwar soyayya ga waɗannan jaruman ba? Shin laifi ne don mun sassauta soyayyarmu a garesu? Ko kaɗan, hasali ma yin hakan shi ne abin da ya dace. Wani fa yana sane jaruminsa yayi wani abun amma saboda makauniyar soyayya sai ya yi ƙirmijin-ƙememe yace atafau ba haka abin yake ba ayi ta kai ruwa rana da shi, haba aboki baka da aikin yi ne? Haba 'yar uwa baki da abin yi ne? Me zai hana in za mu tattauna mu dinga tattaunawa irin ta hankali a nutse ba tare da cin fuskar juna ba? Na san dai cewa babu wanda zai so ace ga shi ranar ƙiyama sun tashi tare da jaruminsa a gaban Allah, ko ni da nake masoyin SRK ina masa kyakkyawan zato amma wallahi ba zan yarda ace in tashi tare da shi ba ranar alƙiyama. To kuma gashi addini ya tabbatar mana da cewa abin da zai faru kenan ga duk wanda ya mutu yana mai miƙa yana son wasu mutane.
Ashe Kenan akwai buƙatar mu hankalta mu san irin soyayyar da za mu ke yi wa jaruman nan, kuma a ƙoƙarin yin hakan mu tabbatar cewa ba mu ɓata mu'amalarmu da mutanen da muke tare da su ba, domin waɗancan har abada ba za su taɓa maye mana gurbin na nan ba, kuma ba za su taɓa yarda su ɓata da na can saboda mu da ke nan ba (in ma sun san da zamanmu kenan)
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, Aameen Thumma Aameen.
#haimanraees
19 June 2020