
Jaruma Manisha Koirala ta Koka da Juyawar Zamani Yanda da take motsawa Son Ranta take Jan Ragamar Film ko tare da Jarumi Amma Yanzu Gashi itace ta fito a matsayin uwa Hakan yayi mata tsauri, ta furta haka bayan ta fito a uwa ga jarumi Kartik Aaryan cikin Film shehzada tace Lallai zamani ya juyata.
Daga gefe Guda An tambayeta game da Yin Aure ko kasancewar ta a uwa tace ita lamarin ta yanzu a batun uwa tana da karen ta da magen ta watau mawgli da simba, amma tace ƙawayen ta masu Aure da yara suna birgeta kuma hakan ita ma zai mata kyau ace tana da abokin rayuwa.
Jarumar yanzu tana da shekaru 52 kuma ta taɓa Auren wani ɗan kasuwa tun a 2010 sunyi shekara biyu sun rabu a 2012 bata kara Aure ba kuma tana ganin Yanzu koda tana da yara yanzu bata da lafiyar kula dasu domin tayi fama da ciwon Kansa ( Cancer) ciwon daji.
#AbbaIndiaDala