MATA A FINA-FINAN INDIYA 01



MATA A FINA-FINAN INDIYA


                 Kashi na (01)

                   Tare da

            Haiman Raees 
            

Wannan wani sabon shiri ne wanda hukumar wannan gida ta Æ™irÆ™iro domin ya dinga zaÆ™ulo muhimman abubuwan da suka shafi mata a masana'antar shirya fina-finan Indiya baki É—aya. Muna fata za ku karÉ“e shi hannu biyu. 

A Faro daga tushe. 

A tsakanin al'umma irin na Æ™asar Indiya, akwai irin yanayin da ake so mace ta fito a cikinsa yayin É—aukar fim domin ya dace da waÉ—annan al'umma. 
Misali, mace ta fito a matsayin Sita a fim. Sita É—aya ce daga cikin jaruman labarin Ramayana, É—aya daga cikin labaru mafi shahara a Æ™asar Indiya waÉ—anda ke Æ™unshe da ladubba tare da nuna banbancin da ke tsakanin daidai da rashin daidai. Sita mata ce ga Rama wanda aka ce yana bayyana zubin abubu nagari kamar daraja, jarumta, da kuma amana. Mafi yawancin fina-finan Indiya sun samo asali ne daga É“uɓɓugin labaran Ramayana da kuma Mahabarata wanda ya Æ™unshi labarin abin bauta Krishna. Sita nagartacciyar mace ce wacce ta ke ganin mijinta da Æ™ima kuma shi ne abin koyi a gare ta. Wannan dalili ya sa fina-finan farko-farko na Bollywood suke nuno mata da siffa irin nata domin ya dace da al'ummar yankin su. 

Haka kuma, a cikin wani gagarumin aikin mai taken Manusmriti, wani kundi ne wanda yake magana akan shari'o'i, É—a'a da kuma tarbiyya. A cikin sa, an bayyana cewa wajibi ne mace ta miÆ™a wuya wa Mahaifinta yayin da take Æ™arama, a yayin da ta girma kuma wa mijinta, bayan ta tsufa kuma ko in mijinta ya mutu, to ta maida hankalinta kacokan wa 'ya'yanta. 
  
Kamar yadda aka tsara a cikin Manusmriti, mata ba su san daÉ—in 'yanci ba. A kullum abin da ake buÆ™ata daga mace kawai shi ne kullum ta fito cikin farin ciki kuma ta kasance cikin kula da gidan ta. Kullum so ake ta kasance me biyayya ga mijinta, har bayan ransa. 

Ko da yake masana'antar fina-finan Indiya tana canjawa tare da samun ci gaba, matan da ke fitowa a cikin irin wannan siga sau da dama ana nuna su da cewa suna cikin farinciki kuma suna da É—a'a matuÆ™a. WaÉ—anda kuwa ba sa fitowa a irin haka ko suke sukar hakan, ana ganin cewa basu da É—a'a kuma ya kamata a hukunta su. 

Irin wannan yanayi ko siga, shi ne mafi shahara daga cikin irin sigogin da mata ke fitowa a cikin sa a fina-finan Indiya. 

Amma a yanzu, ana iya raba irin sigogin da mata ke fitowa a cikin fina-finan Indiya zuwa gida huÉ—u kamar haka:

Sigar farko: Matar Aure

Wannan ita ce sigar nagartacciyar mace wacce babu ruwanta da baÉ—ala da duk wani nau'i na rashin É—a'a. Ya zama wajibi a kanta ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta martaba al'adar indiyawa kuma dole ta É—aukaka darajar gidanta ta hanyar kulawa da shi, kuma dole ne ya zamana ta dogara da mijinta ba wani ba, ba kuma kanta ba. Kuma wajibi ta kasance me zage damtse wajen aikace-aikacen gida 

Siga ta biyu: Mahaifiya

Ita wannan an fi jingina ta da abubuwan da suka shafi addini, don haka ba a taɓa samun ta da yin abin da be dace ba. Indiyawa da yawa suna ɗaukar Mahaifiya da matsayi irin na abar bauta. Wannan kuma ya samo asali ne saboda alaƙar da suke da shi abar bauta Shakti wacce take da ƙarfin gaske a tsakanin addinai da kuma al'adun su. Wannan dalili ya sa har yau indiyawa suke ba wa Mahaifiya matsayi na musamman a cikin fina-finan su. In kana son ganin irin yadda ake nuna girman darajar uwa sosai, kana iya kallon Mother India (1957), a kwana kwanan nan kuma kana iya kallon KGF: Chapter 1 (2018)

 Siga ta uku: 'Yar Æ™walisa 

Wannan ita ce 'yar zamani, kuma tana koyon duk wata É—abi'a irin ta turawan yamma. Daga cikin halayenta akwai shan Æ™wayoyi, busa sigari, shan giya, tiÆ™ar rawa a kan titi da shiga ta fitsara sannan tana iya faÉ—awa soyayya kuma ta fita kafin ka Æ™yafta ido. A koda yaushe irin wannan takan samu hukuncin da ya dace da ita. 

 Siga ta huÉ—u: 'Yar balaja'u

Ita kam irin wannan, ta shallake duk wani mataki na rashin É—a'a a bisa al'ada irin ta mutanen Indiya, ta ma koma tamkar wata karuwa ko kuma 'yar casu kawai. A koda yaushe ita kawai nuna tsiraici ne aikin ta tare da jan hankalin maza zuwa gare ta. Kai ana sa irin wannan a fim ne ma kawai domin ta kashe Æ™warÆ™watar idanuwan mazaje ba don lale ta iya aiki ba, ba kuma don ta isar da wani muhimmin saÆ™o ba. A Æ™arshe akan nuna irin waÉ—annan mata sun rasa wanda suke so É—in kuma sun Æ™are cikin takaici ko kuma su yi mutuwar wulaÆ™anci. 

A taÆ™aice, waÉ—annan su ne ire-iren sigogin sau da dama mata ke fitowa a ciki a masana'antar fina-finan Indiya. To yau da gobe ana samun canje-canje da kuma Æ™alubale iri-iri. Amma kafin mu je can, za mu ci gaba da tattauna batun mu da muka fara na a fara daga tushe. 

Ku tare ni a shiri na gaba don jin abin da ke gaba. 

#haimanraees

Comments