Tsohuwar Jaruma kuma Mawaƙiya Sulakshana Asali waqa takeyi Wajen 70s, Daga bisani ta fara Acting a 1975 Kuma ta karɓu sosai domin tana da Ƙoƙari wajen Ayyukan ta, ta kamu da Soyayya Tsohon Jarumi Sanjeev Kumar ( Wanda Akace a zamanin babu wanda ya kaishi iya Acting) Sedai Shi Kuma Yana Matuqar Son Hema Malini ( Dream girl ) Kuma Yayi iya kokarinsa wajen sanarwa Hema Amma taqi Har Daga Bisani ta Auri Dharmendra.
Sanjeev Kumar Ya fara shaye-shaye na takaici har hakan ya fara taɓa lafiyar sa yana yawan zuwa wajen Sulakshana ta bashi shawarwari amma kawai a matsayin ƙawa ya dauke ta, mutane musamman Abokan Aikin su suna yawan cewa Sulakshana ke kaɗai ce zaki iya kula dashi tare da dauke damuwar sa ita kuma a lokacin tana yawan cewa ya aure ta amma yaƙi sedai tana cewa tana jiran wannan lokaci da zai juyo da zuciyarsa gare ta tasan cewa zaizo, kwatsam Sanjeev Kumar ya mutu a lokacin yana da shekaru 47 duk da wasu sukan ce a lokacin yana da shekaru 50, amma dai ya mutu bai taɓa aure ba.
Hakan ya taɓa Zuciyar Sulakshana kuma ta Shiga damuwa marar misaltuwa kuma hakan ya haifar mata da ciwo domin duk wanda yazo neman ta da Aure bata taɓa yarda dashi ba itama dai bata taɓa Aure ba har ta daina aikin film bayan zamanin ta ya huce.
Shekarun bayan nan kusan shekaru 3 kenan a lokacin da take da shekaru 65 tayi mummunan haɗari wanda ƙashin da yake da Alaqa da gamayyar ƙirjin ta ya karye anyi mata aiki sau 4 amma ba a kai ga yanda ake bukata ba, akance tana kasancewa a ɗakinta akan gado tana sauraren Waqoqi na Shekarun kuruciyar su musamman wanda sukayi a lokacin rayuwar su ita da Sanjeev Kumar.
Mutane Sukan ce Banda Ƙaddarar Rayuwa Ina ma Ace Jarumi Sanjeev Kumar Yayi haquri Akan Rashin Hema ya Auri Sulakshana da take mutuwar Son sa.
#AbbaIndiaDala