14-07-1938 ---- HAPPY BIRTH ANNIVERSARY OF OM SHIVPURI AND HIS WIFE Sudha Shivpuri @85 & 84

14-07-1938 ---- HAPPY BIRTH ANNIVERSARY OF OM SHIVPURI AND HIS WIFE Sudha Shivpuri @85 & 84



~An haifi jarumi "Om Shivpuri" a irin wannan rana wato 14 ga watan July na shekarar 1938 a garin Patiala dake kudu masu gabas na yankin Punjabi cikin ƙasar India,


~Om Shivpuri ya kasance jarumi ne a guraren wasanni kafin daga baya ya shigo Hindi Cinema, bayan kammala aikin sa a "National School of Drama" a shekarar 1964,


~Yayi fina-finai a Bollywood Fiye da 175, bayan farawar sa da Film É—in "Ashadh Ka Ek Din" na Producer Director "Mani Kaul" inda suka fito tare da: Arun Khopkar, Rekha Sabnis da Aruna Irani, inda yafi buga Role É—in jami'in tsaro,



~Yayi aiki da manyan Producer Directors za jiga-jigan jaruman zamanin sa, inda aikin sa yafi sanuwa a 70s 80s zuwa 90s, KaÉ—an daga fitattun fina-finan da Om Shivpuri ya taka rawa a cikin su akwai:

~Kitaab
~Sholay
~Aandhi
~Koshish
~Achanak 
~Geraftaar
~Khushboo
~Hum Dono
~Khubsoorat
~Don --- 1978
~Disco Dancer
~Zakhmi Aurat
~Biwi Ho To Aisi
~Namak Haraam
~Aakhree Raasta
~Andhaa Kaanoon
~The Great Gambler
~Hum Tere Aashiq Hain
~Hum Kisise Kum Naheen

~Da dai sauran fina-finai masu dama inda wasu ma sai bayan rasuwar sa suka fita, a ɓangaren Directing ma ya shirya wasu fina-finan,

~Ya samu nasarori da dama kamar dai ko wanne babban jarumi,


~A shekarar 1968 ne ya auri matar sa mai suna "Sudha Shivpuri" wadda ita ma a irin wannan rana aka haifeta wato "14 July 1937" inda mijin nata ya girme mata da shekara É—aya, ita ma dai matar tasa jaruma ce musamman a fina-finan gidan television, inda suka haifi Æ´aÆ´ansu guda biyu "Vineet Shivpuri" da "Ritu Shivpuri" wadda ita ma jaruma ce a Kannada Film Industry da kuma Hindi Cinema, Film É—in da ya fara a Bollywood shine Aankhen 1993 inda suka fito tare da Jarumi Govinda da Chunky Pandey da kuma Raj Babbar,

~A ƙarshen shekarar 1990 ne kuma jarumi Om Shivpuri yace ga garin ku nan a sakamakon bugun zuciya da ya same shi, inda ya wuce yana da shekaru 52 a Duniya.

@AyƘoƘi.

Comments