ƘWAƘWAF: ALGAITA SUN DAƊE BASU FASSARA SHASHASHAN FIM KAMAR WANNAN BA
Asalin labarin film ɗin an ginashi ne akan #Black_Hole wato #Baƙin_Rami, abinda yasa nace sha-sha-shan film shine Black Hole yana buƙatar nagartaccan aiki kafin a gane abinda Ake son nunawa amma basuyi hakan ba, kawai suka birbira labarin suka barshi, Kuma Black Hole mas'ala ce mai girman gaske wadda tana buƙatar bayani sosai kafin a fahimta.
Abinda ya faru a film ɗin: sun nuno wani Malamin kimiyya yana maganar zuciya yana cewa ya yarda da kansa kuma shi kaɗai zaiyi nasara a wannan aiki, a ƙoƙarinsa na samar da na'urar da zata kai mutum zuwa ga Black Hole (Wanda har yanzu a duniya an kasa samun wanda zaije wannan duniya ta Black Hole, saidai an samu dakyar an dakko hoton black holes a wasu shekaru da basu wuce 5 zuwa 7 ba)
NASAN MAI KARATU ZAI SO YAJI MENE BLACK HOLE
#BLACK HOLE (Baƙin Rami) A TAƘAICE
A cikin ilimin Physics game da duniya da abubuwan da ke kewaye da ita (Space), malaman Physics (Astrophysics/Astronomy) tun shekaru da dama sun gano wata duniya ta musamman da suke kira "Black Hole (Baƙin Rami)". A dunƙule shi Baƙin Rami (Black Hole) wata duniya ce mai zamana kanta a kaunu (space), wadda take da matuƙar tasirin zuƙo da finciko (gravity) duk wani abu da ya kasance ta ya faɗa cikinta. Malaman Physics suna cewa game da duniyar Baƙin Rami: "Once you go black you will never go back!" Ma'ana: duk abin da ya sake ya faɗa cikin baƙin rami, ba zai sake dawowa ba! Suna ƙiyasta girman ƙaramar duniyar Black Hole da adadin girman duniyar rana sau miliyan ɗari (100 million).
#Masana kimiyya suna yiwa (Singularity) wato tsakiyar Black Hole take da “NO MAN'S LAND!”
Duk abin da yazo wucewa ta kusa da "black hole", ta wani guri da ake kira da "event horizon" to sai ya zukoshi ya hadiyeshi saboda karfin janyowar da "gravity" yake da shi a gurin.
Babu mutumin da ya taba kusantar inda "black hole" yake amma da wani zai je gurin da sai ta hadiyeshi irin hadiyar da injin taliya yake yiwa fulawa. Da yake duk abin da ya fada "black hole" to ko alamarsa ba a kara ji domin yana rasa duk wani bayani da yake tattare da shi ta hanyar wani yanayi da suka kira "information loss." Kuma ga shi duk abin da aka harba ya kusanci "black hole" to tasa ta kare, wannan ta sanya komai na Kimiyya yake rikicewa da an zo gun.
To amma yanzu tun da har an iya dauko hotonsa ana tsammanin wannan wata 'yar karamar dama ce da aka samu ta cewa za a iya nazartar cikin "black hole" din a nan gaba domin a ajiye duk wani hasashe a dauki hakika.
#Abinda yasa na kira film ɗin da sha-sha-shan film shine, sunyi abinda hankali bazai ɗauka ba, su sai suka nuna har sun samar da hanyar da za'a shiga waccan duniyar kuma har sun gano mutane ne masu kama damu rayuwarmu ma iri ɗaya ce dasu, #Richard Feynman, wanda ya yi bincike akan me zai faru da zamu iya fadawa cikin "black hole" kuma bamu mutu ba, ya ce idan ka fada cikin "black hole" to wata duniyar (universe) din za ka fada mai wata irin dokar ta dabi'a daban! Dama dai dokokin dabi'a sun rabu gida biyu, tsakanin na manyan abubuwa (Newtonian mechanics) da kuma na mitsi-mitsin abubuwa (Quantum mechanics). Kuma duk masu bincike su tabbatar da cewa dabi'un mutane mabanbanta duniyoyi dole su banbanta.
kenan su shirme sukayi da suka nuna dabi'ar mu iri ɗaya ce da mutanen da suke duniyar Black Hole, kenan har gwara #PK na jarumi #Aamir_Khan tunda sunyi amfani da Maganar masa kimiyya suka nuna dabi'ar mu ba iri ɗaya bace da duniyar su PK. da za'a sake tsara labarin tabbas zai zama babban film idan aka faɗaɗa shi akayi bayani sosai da kuma yin abinda hankali zai ɗauka.
✍️ #Ameenu_Sharada