BAHUBALI THE BEGINNING - FANSAR ZUNUBI TA HANYAR CETO RAI
An hangi lady sivagami dauke da dan jaririn Amarendra bahubali da devsena, kibiyar da sarki bhallaldeva ya harbe ta dashi yana nan soke a bayan ta. A lokacin da ya harbe ta, anyi tunanin ta mutu, in kuwa ta mutun to dole tare da jaririn zasu mutu, tunda suna cikin kogi a lokacin da ya harbe tan so cikin kogin zasu fada..
Wasu dakarun sarki sun biyo ta a baya, inda ta yi musu kwanton bauna tare da shammatar su, ta kashe su. Cikin galabaita ta ci gaba da tafiya, can ta hango dan karamin gari nesa da ita da alamun fitilu a kunne, amma kafin tayi wani yunkuri se ta zame igiyar ruwa ya jata suka fada cikin kogin ita da jaririn.
Dake ruwan na da zurfi kuma da fadi, ta tabbatar baza ta rayu ba, kuma ta tabbatar in ta mutu to jaririn ma ya mutu, wanda kuma duk wannan hadarin da ta shiga dan ta cece shi ne.. Anan ta daga fuskar ta ta kalli sama. Sai ta ce
PARMESHWAR - YA UBANGIJI
TU MERE PAAPO KA PRASCHIT CHAHTA HAI TOH MERE PRAAN LEY LEY - IDAN MUTUWA KADAI SHINE HANYAR FANSAR WANNAN ZUNUBI DA NA AIKATA TO KA DAU RAINA
LEKIN ISS BACHE KO JEEWAN DAN DEY DEY- AMMA YARON NAN YA RAYU
JO ISKI PRATIKSHA KAR RAHI HAI USS MAA KE LIYE ISSE JEENA HOGA, - YA RAYU DOMIN MAHAIFIYAR SA DAKE JIRAN SA
MAHISHMATI SINGASAN KE LIYE ISKO JEENA HOGA. - YA RAYU DOMIN YA DARE KUJERAR SARAUTAR BIRNIN MAHISHMATI
MAHINDRA BAAHUBALI KO JEENA HOGA! - MAHENDRA BAHUBALI YA RAYU!!!
Gama furta wadannan, se fuskar ta ta fara nutsewa cikin ruwan, alamar ta mutu, Amma abin al'ajabi hannun ta na dage da jaririn bata sauke shi ba, haka hannun ya kasance a dage, jaririn na ta tsala kuka, har se da gari ya waye a haka, har wasu mutane daga kauyen dake kusa da gurin sun fito, kawai suka ji alamar kukan jaririn, sukai ta dube dube, har de suka hango jaririn a hannun ta bata sauke ba duk da ta dade da mutuwa. Har se da mutanen suka nufi gun suka karbi jaririn daga hannun ta, sannan ne aka ga hannun ya sauka ya nutse cikin ruwa.
A zahiri na rayuwa hakan ya saba da hankali, ace mutum ya mutu amma hannun sa na dage kuma da jariri a hannun. Se de a irin cinema da S S RAJAMOULI ya kirkira a film din BAHUBALI, akwai sakon da yake son isarwa...
Sivagami ta aikata kuskure babba na bada odar kashe Amarendra bahubali, wanda bata ma san makirci aka hada ba dan ae masa sharri cewa ya yi yunkurin kashe sarki,...
Bayan kattapa ya kashe bahubali ta hanyar sukan sa a baya, sarki bhallaldeva yazo gun yai ta saran sa, yana fadar yadda suka yaudari sivagami har tayi passing odar cewa a kashe Amarendra bahubali, ta hakan ne kattapa ya fuskanci cewa ashe makirci ne.. Kuma ya bayyanawa sivagami yadda aka shirya makircin,.. Anan nadama ta shige ta sosai. Cikin fusata ta dauki dan jaririn bahubali ta yi wajan bene da shi inda dimbin al'umma suke cikin rudu na rashin sanin shin bahubali na raye ko ya mutu.. Anan ta daga kai tace musu
AMARENDRA BAHUBALI NAHI RAHE - Amarendra bahubali baya raye
ABHI APKE MAHARAJ HAI - Amma yanzu kuna da sabon sarki..
MAHENDRA BAHUBALIII -!!!!
jin kalmar mahendra bahubali ya dawo musu da kwarin gwiwar su.. Nan dimbin al'ummar garin SUKA dinga daga hannu suna cewa
MAHENDRA BAHU!!! MAHENDRA BAHU!!!!
Hakika S S RAJAMOULI ya nuna mana cewa sivagami ta fanshi zunubin da ta aikata ta hanyar sadaukar da rayuwar ta wajan tseratar da jaririn, kuma Ubangiji ya amsa rokon ta sanda take mika bukatar ta gare shi duk da tana tsakiyar kogi mai zurfi da fadi da kibiya cake a bayan ta, tana kuma shirin nutsewa. Alamu sun nuna cewa Ubangiji ya karbi addu'ar ta, shi yasa duk da ta mutu, hannun ta dake dage kuma rike da jariri bai sauka ba, har se da gari ya waye aka samu mutanen da suka ga jaririn a hannun ta suka kawo kawo dauki har suka karbi jaririn, sannan ne tayi giving up gaba daya, inda aka ga hannayen sun karasa nutsewa...
A doro na hankali, aga mutum ta nutse a cikin katon kogi ko teku, kuma ta mutu, amma hannun ta dauke da jiriri yana a dage tun tsakiyar dare har gari ya waje, har se da aka ceci yaron sannan hannun ma ya nutse, to akwai sako mai muhimmanci....
#Akk. 6 YEARS OF BAHUBALI THE CONCLUSION