WASU JARUMAN BOLLYWOOD DA SUKE NADAMAR FITOWA CIKIN WASU FINA FINAI
1 AMITBAH BACCAHN
Big boss Namu Baccahn uban jarumai da yake magana game da film din sa Ram gopal Varma ki Aag ya bayyana cewa " idan film bayyi kyau ba director da jarumi ya kamata a tuhuma, fitowa a Wannan shirin yana daya daga cikin kura kuran Dana aikata a rayuwata.
2 KATRINA KAIF
Shahararriyar Jarumar ta bayyana cewa tana nadamar fitowa cikin film din BOOM, Acewar kat lokacin da ta fito tai aikin wannan film Sam batasan Yaya Al'adun indiyawa suke ba. Ta bayyana rashin sani a Amatsayin dalilin daya sanya muka ganta cikin film din.
3 GOVINDA
Game da film din kill dil ya bayyana cewa " matata da yarana sune suka karfafamin gwiywa kan cewar na Amshi film din, Acewar su bai kamata ace ina zabar rawar da zannna takawa cikin fina finai ba" Wannan shine musabbai.
4 PRIANKHA CHOPRA
Da take magana akan kan experience dinta game da film din ZANZEER ta bayyana cewa "Wani lokacin Mukan Aikata kuskure da kanmu"
5 SHAHID KAPOOR
A bayanin sa na bayyana yadda yake Nadamar fitowa cikin film din Shaandaar yace "Ni Sam banga Amfanin film din nan ba, Bansan miyasa na fito cikin sa ba.
6. TWINKLE KHANNA
Ba iya twinkle khanna ba, hatta su kansu mashirya shirin Mela basa Wani son tunawa da shi. Twinkle ta bayyana Cewa taso ace Mela babu yadda za'ai a tuna da Mela.
Imam Abdu Bandirawo