Fassarar Waƙar Burjkhalifa

🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻



Fassarar Waƙar Burjkhalifa


• Waƙa - Burjkhalifa

• Fim - Laxmmi Bomb

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2020

• Sauti - Shashi - Dj Khushi

• Rubutawa - Gagan Ahuja

• Kamfani - Zee Music Company

• Rerawa - Shashi - Dj Khushi & Nikhita Gandhi

MATASHIYA: Burj Khalifa wani dogon gini ne da ke birnin Dubai a United Arab Emirates. Tsawon ginin ya kai mota 829.8 wanda hakan ya bashi damar zama gini mafi tsawo a duniya. Taj Mahal kuma wani gini ne mai farin fenti da ke kudancin kogin Yamuna na garin Agra. Mughal emperor Shah Jahan ne ya bada izinin gina shi a shekara ta 1632 domin ya rufe kabarin matarsa Mumtaz Mahal. Ginin yana ɗaya daga cikin gine-ginen da aka fi so a duniya, haka kuma yana daga cikin abubuwan ban mamaki bakwai na duniya da aka ayyana, kuma ana alaƙanta ginin da soyayya. Kylie Jenner kuma wata kyakkywar mace ce da ke harkar kayan kwalliya kuma ta shahara a duniya ta wannan fanni. Ita kuwa FIFA, ita ce babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya. 

• Hot Tere Manner Ni, Manner Ni...

Ɗabi'arki zazzafa ce. 

• Chhapte Tere Banner Ni, Banner Ni... Tere Banner Ni...

Har a jikin allunan talla ake manna ki. 

• Hot Tere Manner Ni, Chhapte Tere Banner Ni
Ɗabi'arki zazzafa ce, Har a jikin allunan talla ake manna ki. 

• Fashion Tu Kardi Jiven Kylie Jenner Ni

Salonki iri ɗaya da na Kylie Jenner

• Ho Munda Thakda Nahi Kar Kar Ke (x2)

Gayu ba sa gajiya. 

• Teriyaan Tareefan...

Da yabonki. 

• Jee Karda Dila Doon, Tainu Burj Khalifa

Zuciyata na so ta siya miki Burj Khalifa. 

• Tainu Burj Khalifa, Ho Tainu Burj Khalifa

(siya) miki Burj Khalifa, (siya) miki Burj Khalifa. 

• Tainu Burj Khalifa 

(siya) miki Burj Khalifa,

• Ho Tainu Burj Khalifa, Tainu Burj Khalifa

(siya) miki Burj Khalifa,siya) miki Burj Khalifa 

• Ho Tainu Burj Khalifa, Tainu Burj Khalifa Ho

(siya) miki Burj Khalifa,siya) miki Burj Khalifa 

• In To Jamila

Ke kyakkywa ce. 

• Habibi (x7) 

Abar Sona. 

• In To Jamila

Ke kyakkywa ce. 

• Habibi (x7) 

Abar Sona. 

• Yeah!

• Ho Tainu Vekh Ke Chadh Gaye Ishqe

Da ganinki sai na kamu da sonki. 

• Tu Diamond Wangu Lishke

Sai ƙyalli kike yi kamar lu'ulu'u 

• Ho Tainu Vekh Ke Chadh Gaye Ishqe

Da ganinki sai na kamu da sonki. 

• Tu Diamond Wangu Lishke

Sai ƙyalli kike yi kamar lu'ulu'u

• Na Karni Siftaan Taj Mahal

Ba sa yabon Taj Mahal haka. 

• Jinni Tere Baare Likhde

Kamar yadda suke yabonki. 

• Oh Munde Tainu Follow Karde

Gayu sai binki suke yi. 

• Munde Tainu Follow Karde

Gayu sai binki suke yi. 

• Chhad Gaye Soccer Fifa

Suna barin ƙwallon ƙafa da FIFA ma gaba ɗaya. 

• Jee Karda Dila Doon, Tainu Burj Khalifa

Zuciyata na so ta siya miki Burj Khalifa. 

• Tainu Burj Khalifa, Ho Tainu Burj Khalifa

(siya) miki Burj Khalifa, (siya) miki Burj Khalifa. 

• Tainu Burj Khalifa 

(siya) miki Burj Khalifa

• Ho Tainu, 

(siya) miki 

• Tainu, Ho Tainu

(siya) miki 

• Tainu

(siya) miki 

Yeah Aye

• Hot Mere Manner Ni, Oh... O...

Ɗabi'ata zazzafa ce. 

• Chhapde Mere Banner Ni, Oh Yeah...

Har a jikin allunan talla ake manna ni. 

• Hot Mere Manner Ni

Ɗabi'ata zazzafa ce. 

• Chhapde Mere Banner Ni

Har a jikin allunan talla ake manna ni. 

• Look Ton Jealous Kardi Ae, Kylie Jenner Ni

Kyawuna har sa Kylie Jenner kishi yake yi. 

• Mere Husn De Charche Charche (x2)

Irin yabon da ake yi wa Kyawuna. 

• London To America

(ya watsu) daga Landan zuwa Amurka. 

• Mundeya Dilaade Mainu Burj Khalifa

Ɗan gaye! Ka siya mini Burj Khalifa. 

• Mainu Burj Khalifa, Ho Mainu Burj Khalifa

(siya) mini Burj Khalifa, (siya) mini Burj Khalifa. 

• Mainu Burj Khalifa

(siya) mini Burj Khalifa

• Ho Mainu Burj Khalifa, Mainu Burj Khalifa 

(siya) mini Burj Khalifa, (siya) mini Burj Khalifa. 

• Ho Mainu Burj Khalifa, Mainu

(siya) mini Burj Khalifa, (siya) mini Burj Khalifa

• In To Jamila

Ke kyakkywa ce. 

• Habibi (x7) 

Abar Sona. 

• In To Jamila

Ke kyakkywa ce. 

• Habibi (x7) 

Abar Sona. 

©️✍🏻
 Haiman Raees 
Infohaiman999@gmail.com 


💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN ROWDY RATHORE

FASSARAR KALAMAN FIM ƊIN ROWDY RATHORE




Shekarar Fita - 2012

 1. Jisne bhi yeh socha ki main dar gaya ... woh saala arthi pe apne ghar gaya 

Wanda duk yake tunanin na tsorata ne... To wawan shi zai koma gida a akwakwu. 

Akshay Kumar

 2. Don't angry me!

Kada ka fusata ni. 

Akshay Kumar 

 3. Naam sunte hi pichwaade mein bhukamp aa gaya na?

Ashe jin sunan ba kamar jin tsawa bane a mazaunanka? 

Akshay Kumar

 4. Sau saal zinda rehne ke liye sau saal ki umar zaroori nahi ... sirf ek din mein aaisa kaam kar jao ... jisse duniya tumhe sau saal tak yaad rakhe

Domin a rayu tsawon shekaru 100 ba ka buƙatar sai ka shekara 100... Ka yi wani abu a yini ɗaya... Ta yadda duniya za ta tuna da kai har na tsawon shekaru 100. 

Yashpal Sharma

 5. Pyar karne ke liye pechaan ki nahi ... dil ki zaroorat hoti hai. 

Ba ka buƙatar sanin mutum domin ka faɗa soyayya... Zuciya ka ke buƙata. 

Akshay Kumar 

 6. Meri sirf ek hi khawaish hai ... jab maut mere samne aaye tab main darra hua na lagon ... bas mera haath meri mooch ko taav de raha ho aur mere chehre par ek muskurahat ho. 

Burina kawai shi ne... Kada in tsorata yayin da mutuwa ta zo gaba gare ni... A maimakon haka hannuna ya zama yana murza gashin bakina tare da murmushi a fuskata. 

Akshay Kumar

 7. Main nahi darta ... maut darti hai mujhse.

Ba na tsoron mutuwa... Mutuwa ita ke tsorona. 

Akshay Kumar

 8. Joh main bolta hoon woh main karta hoon ... joh main nahi bolta woh main definitely karta hoon. 

Duk abin da na ce zan aikata sai na aikata... Abin da ban ce zan aikata ba kuwa tabbas sai na aikata. 

Akshay Kumar

 9. Sachche police officer ki vardi bhi apni duty nibhati hai. 

Hatta Kakin jami'in Ɗan Sanda na gaske ma cika aikinsa yake yi. 

Akshay Kumar

10. Joh bura kaam karte hai ... darr unki nas nas mein hota hai. 

Masu aikata miyagun ayyuka... Kodayaushe a cikin tsoro suke. 

Akshay Kumar.

11. Dekh ke darr gaya ... ya darr ke dekh raha hai?

Ka tsorata da ka ganni... Ko kallona kake yi a tsorace? 

Akshay Kumar

12. Tereko jab gussa aata hai tu chilata hai ... main udata hoon. 

Idan ka fusata abubuwa kake fasawa... Ni kuma fashewa nake yi. 

Akshay Kumar

13. Aurat ka khaas khayal do hi umar ma bahut rakhna padta hai ... ek jab uski umar hovat hai satrah, tab saala badh jaata hai khatra ... aur jab aurat hovat hai tees, oo saali ban javat hai cheez

Kana buƙatar kulawa da mace sosai a yayin da ta kai shekaru iri biyu... Lokacin da ta kai shekara 17 saboda a lokacin ne take da haɗari sannan... Da kuma lokacin da ta kai shekara 30, saboda a wannan lokacin ne ta zama zazzafa. 

Nassar

Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com 

Fassarar Waƙar Main Pal Do Pal Ka Shayar Hoon

Fassarar Waƙar Main Pal Do Pal Ka Shayar Hoon



• Waƙa - Main Pal Do Pal Ka Shayar Hoon

• Fim - Kabhi Kabhie

• Shekarar Fita - 1996

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Sauti - Khayyam 

• Rubutawa - Sahir Ludhianvi

• Kamfani - EMI 

• Rerawa - Mukesh 

• Fassarawa - Haiman Raees 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Mujhse pehle kitne shayar aaye 

Marubutan waƙa da dama sun zo kafin ni. 

• Aur aakar chale gaye

Sun zo kuma sun tafi. 

• Kuch aahein bharkar laut gaye 

Wasu kan yi kuka kuma su dawo. 

• Kuch nagme gaakar chale gaye 

Wasu kan yi waƙa su tafi. 

• Woh bhi ek pal ka kisa the 

Su ma wani ɓangare ne na wannan lokacin. 

• Main bhi ek pal ka kisa hoon 

Nima wani ɓangare ne na wannan lokacin. 

• Kal tumse juda ho jaunga 

Gobe zan yi nesa/rabu da ke. 

• Woh aaj tumhara hisa hoon 

Duk da cewa ina cikin yau ɗin ki. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Kal aur aayenge

Wasu kaɗan za su dawo gobe. 

• Nagmo ki khilti kaliyan chunne wale 

Waɗanda za su zaɓi waƙoƙi masu tashe. 

• Mujhse behtar kehne wale 

Za a samu waɗanda suka fi ni iya bada labari. 

• Tumse behtar sunne wale

Da kuma masu sauraro fiye da kai/ke 

• Kal koi mujhko yaad kare

Ina fata wani zai tuna da ni a gobe.
 
• Kyun koi mujhko yaad kare

Amma me yasa wani zai tuna da ni? 

• Mashroof zamana mere liye 

Me ya sa wannan duniyar mai cike da uzuri

• Kyun waqt apna barbad kare 

Za ta ɓata lokacinta a kaina?

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon 

Ni marubucin waƙa ne na ɗan wani lokaci.

• Pal do pal meri kahani hai

Labarina zai daɗe na ɗan wani lokaci ne kawai. 

• Pal do pal meri hasti hai

Wanzuwata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Pal do pal meri jawani hai 

Samartakata za ta kasance na ɗan wani lokaci ne. 

• Main pal do pal ka shayar hoon I'm a poet only for a moment or two
  
©️✍🏻
 Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com 

FASSARAR WAƘAR DOSTI

FASSARAR WAƘAR DOSTI



• Waƙa - Dosti
• Fim - RRR
• Harshe - Hindi/Hausa
• Shekarar Fita - 2021
• Sauti - MM Keeravani 
• Rubutawa - MM Keeravani 
• Kamfani - T Series 
• Rerawa - Amit Trivedi 
• Fassarawa - Haiman Raees

• Azgar aur baaz ki

Na jegare da na shaho

• Sagar jhanjhaar ki

Na teku da na harshen wuta 

• Jalti angaar Se 

Na wuta mai balbali

• Saahil majdaar ki

Na gaɓar tsakiyar teku

• Baagi jallad ki

Na ɗan tawayen makashi 

• Dosti, Dosti 

Abota, abota 

• Kis aor chali yeh aandhi? 

Ina wannan guguwar hadarin take kaɗawa? 

• Aye kaisi kraanti? 

Ta ina wannan juyin-juya-halin/ juyin mulkin ya zo?

• Sangram yaa sangam ki lehre aayegi

Guguwar gwagwarmaya ko haɗaka na nan zuwa.

Da Ra Dum Da Ra Dum, Da Ra Dum Dum

• Chattan aur toofan ki dosti 

Abotar dutse da hadari 

• Gaaz aur garzan ki dosti 

Abotar walƙiya da aradu/tarnatsa 

• Poorab aur pakshim milte hue

Haɗuwar gabas da yamma 

• Hairat yeh dosti 

Ta ba abotar nan mamaki

Ta Ra Dum Ta Ra Dum, Ta Ra Dum Dum 

• Ek raaz chhup gaya andar

Akwai ɓoyayyen sirri a ciki

• Mauji aur gehra samandar 

Nishaɗi ne da zurfin teku

• Badhta hai harpal tumhare bich ye faasla

A duk lokacin da wannan nisa ya ƙaru a tsakanin ku

• Jung yaa sang ka ho bal

Ko ƙarfin yaƙi ne ko na ƙungiyanci ne

• Chhaye hai Kaun se baadal

Wadda girgije ya wanzu a can

• Chalti hai pal pal zehreeli aisi hawa

Irin wannan iska mai cike da dafi na ci gaba da kaɗawa lokaci bayan lokaci.

• Rah alag Nahin Par hai yeh dar

Hanyar ba ta da banbanci, amma tsoron shi ne

• Lakshya alag inke

Manufarsu daban ce

• Toota Jo darpan chhoota bandhan

Madubin da ya fashe, alaƙar da ta ɓace 

• Kaun bache kis se? 

To wa kuma ya rage? 

• Kis aur chali yeh aandhi? 

Ina wannan guguwar hadarin take kaɗawa? 

• Aye kaisi kraanti? 

Ta ina wannan juyin-juya-halin/ juyin mulkin ya zo?

• Sangram yaa sangam ki lehre aayegi

Guguwar gwagwarmaya ko haɗaka na nan zuwa.

Da Ra Dum Da Ra Dum, Da Ra Dum Dum

• Chattan aur toofan ki dosti 

Abotar dutse da hadari 

• Gaaz aur garzan ki dosti 

Abotar walƙiya da aradu/tarnatsa 

• Poorab aur pakshim milte hue

Haɗuwar gabas da yamma 

• Hairat yeh dosti 

Ta ba abotar nan mamaki

Da Ra Dum Da Ra Dum, Da Ra Dum Dum

• Chattan aur toofan ki dosti 

Abotar dutse da hadari 

• Gaaz aur garzan ki dosti 

Abotar walƙiya da aradu/tarnatsa 

• Poorab aur pakshim milte hue

Haɗuwar gabas da yamma 

• Hairat yeh dosti 

Ta ba abotar nan mamaki

✍🏻
  Haiman Raees 
# haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

FASSARAR WAƘAR CHANNA MEREYA

FASSARAR WAƘAR CHANNA MEREYA 




• Waƙa - Channa Mereya

• Fim - Ae Dil Hai Mushkil

• Harshe - Hindi =Hausa 

 • Shekarar Fita - 2016

• Sauti - Pritam

• Rubutawa - Amitabh Bhattacharya

• Kamfani - Sony Music

• Rerawa - Arijit Singh

• Fassarawa - Haiman Raees
 

• Accha Chalta Hoon, Duaaon Mein Yaad Rakhna

Zan tafi yanzu, ki aje ni a cikin Addu'o'in ki. 

• Mere Zikr Ka Zubaan Pe Swaad Rakhna

Ki ajiye ambatona akan harshenki. 

• Accha Chalta Hoon, Duaaon Mein Yaad Rakhna

Zan tafi yanzu, ki aje ni a cikin Addu'o'in ki. 

• Mere Zikr Ka Zubaan Pe Swaad Rakhna

Ki ajiye ambatona akan harshenki. 

• Dil Ke Sandookon Mein, Mere Acche Kaam Rakhna

Ki ajiye aiyukan kirkina a ma'adanar zuciyarki. 

• Chitthi Taaron Mein Bhi, Mera Tu Salaam Rakhna

Ki ajiye aminci na a cikin wasiƙu da saƙonnin waya. 

• Andhera Tera Maine Le Liya

Ta tafi da duhunki. 

• Mera Ujla Sitaara Tere Naam Kiya

Kuma na barki da tauraro na mai haske. 

• Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya

Ya ke Wata taa (Ya ke Masoyiyata) 

• Beliya, O Piya…

Ya Abokiyar zamana, Ya Abar so na. 

• Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya

Ya ke Wata taa (Ya ke Masoyiyata) 

• Beliya, O Piya…

Ya Abokiyar zamana, Ya Abar so na. 

• Ooo… Piya… Piya… Piya… Ooo Piya…

Ya Abar so na. 

Mmm…

• Mehfil Mein Teri Hum Na Rahe Jo

Idan har ban wanzu a bikin murnarki ba. 

• Gham Toh Nahi Hai, Gham Toh Nahi Hai

Bai kamata a samu rashin jin daɗi ba. 

• Qisse Humare Nazdeekiyon Ke

Labarin kusantuwarmu. 

• Kam Toh Nahi Hai, Kam Toh Nahi Hai

Ba 'yan kaɗan bane, ba 'yan kaɗan bane. 

• Kitni Dafa Subah Ko Meri

Sau da dama na sha juya safiyoyi na. 

• Tere Aangan Mein Baithe Maine Sham Kiya

Zuwa yammacoci yayin da nake zaune a shigifarki. 

• Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya

Ya ke Wata taa (Ya ke Masoyiyata) 

• Beliya, O Piya…

Ya Abokiyar zamana, Ya Abar so na. 

• Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya

Ya ke Wata taa (Ya ke Masoyiyata) 

• Beliya, O Piya…

Ya Abokiyar zamana, Ya Abar so na. 

• O… Piya…

Ya Abar so na. 

• Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya

Ya ke Wata taa (Ya ke Masoyiyata) 

• O… Piya…

Ya Abar so na. 

• Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya

Ya ke Wata taa (Ya ke Masoyiyata) 

• O… Piya…

Ya Abar so na. 

• Tere Rukh Se Apna Raasta Mod Ke Chala…

Na sauya hanya ta daga fuskarki. 

• Chandan Hoon Main

Ni tamkar itacen Sandal ne 

• Apni Khushboo Chhod Ke Chala…

Barin ƙamshina nake yi tare da ke. 

• Mann Ki Maaya Rakh Ke Tere Takiye Tale…

Tare da barin duk wasu mafarkan duniya akan matashinki. 

• Bairaagi, Bairaagi Ka Sooti Chaula, Odh Ke Chala…

Na lulluɓe kaina da likkafani, kenan dai tafiya zan yi. 

• Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya, Channa Mereya Mereya

Ya ke Wata taa (Ya ke Masoyiyata) 

• O… Piya…

Ya Abar so na.

Aaa… O Piya…

Ya Abar so na.

 
©️✍🏻
 Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com 

AKSHAY KUMAR

🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻



HAPPY BIRTHDAY AKKI

Na gaida gwani na gwanaye wajen aiki ka wuce jaki, 
Namijin duniya kake sha-kundum kai ne tafki.

Majaujawar nasara kuke ji wannan shi ne Akki,
Balbela da farinta kun san ba ta biɗar wanki.

Gwarzon maza sannu da ƙara shekaru nawa,
Tabbas ka yi mun gani kuma dole mu yo tafawa.

Ka yi haƙuri ya zam nasara yau kai ke shanawa,
Zakaranka ya riƙa yau ga waƙa yana rerawa.

Happy birthday day muke ma domin yau ce ranar ka,
Kuma jajircewa har yau babu wanda ya kamo ka.

Mun yi murna muna ƙara domin muna ƙaunarka,
Aikinka ai na musamman ne shi yasa muke daɗa bibiyarka.

Maƙiya sun sha haushi kai kuma kullum sai tashi
Kai ne iska da ba ta biɗar fuffuke domin tashi.

Maƙiyinka fa kowaye sai mu ce a kamo shi,
Mu danne ɗan nema mu shafe mai ido da toshshi!

Happy birthday sir

©️✍🏻
 Haiman Raees 
Infohaiman999@gmail.com 

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

FASSARAR WAƘAR TOILET KA JUGAAD

FASSARAR WAƘAR TOILET KA JUGAAD 




• Waƙa - Toilet Ka Jugaad

• Shiri - Toilet - Ek Prem Katha

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2017

• Sauti - Vickey Prasad

• Rubutawa - Garima Wahal & Siddharth Singh

• Kamfani - T-Series

• Rerawa - Akshay Kumar & Vickey Prasad

• Fassarawa - Haiman Raees 

• Duniya Chali Mars Pe

Duniya ta cimma bigiren Mars 

• Chaand Zameen Pe Dikh Rayo

Yanzu mutum na iya ganin wata daga wannan duniyar. 

• Arre Black And White Se Colour Hua

Daga (fina-finai) masu baƙi da fari zuwa masu kala. 

• Ab 3D Main Sab Dikh Raheyo

Ka na kuma iya ganin abubuwa a zubin 3D. 

• Duniya Chali Mars Pe

Duniya ta cimma bigiren Mars 

• Chaand Zameen Pe Dikh Rayo

Yanzu mutum na iya ganin wata daga wannan duniyar. 

• Arre Black And White Se Colour Hua

Daga (fina-finai) masu baƙi da fari zuwa masu kala. 

• Ab 3D Main Sab Dikh Raheyo

Ka na kuma iya ganin abubuwa a zubin 3D. 

• Hazaaron Chad Gaye Everest Ka Pahaad (x2)

Dubban mutane sun haura hau kan dutsen Everest

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Kab Tak Lega Tu Pedon Ki Aadh

Tsawon yaushe ne za ka ci gaba da tsuguno a gindin bishiyoyi? 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Public Mein Bhar Do Laaj Sharam, Sabhyata Yahi Sikhaaye

Ka sa kowa ya ji kunya, wannan shi ne abin da zama ɗan al'ada yake nufi. 

• Ghoonghat Khencho Pet Tak, Baitho Saari Uthaaye

Mata na zaune sun ja sarin su har ciki. 

• Bhabhi Nikli Tarke Tarke, Raste Khade Ladke Rehtey Taad

Suruka na tafe cikin jin kunya marasa kunyar unguwa/layi suna kallonta.

• Sun Le Kya Nature Ki Pukar

Kalli abin baƙin cikin da wannan al'amari ke kai. 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Kab Tak Lega Tu Pedon Ki Aadh

Tsawon yaushe ne za ka ci gaba da tsuguno a gindin bishiyoyi? 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Tourist Dekhe Kile Aur Mahal Jo Desh Ki Shaan Badhaye

masu yawon buɗe ido na zuwa fada da manyan wurare, hakan na ƙara daraja wa ƙasa. 

• Hum Toh Samajh Ke Baap Ka Maal Kone Bhigo Ke Aaye

Mu kuma da muke tunanin namu ne sai mu je mu jiƙe wurin (da fitsari) 

• Baas Maare Ab Apni Virasat, Naash Hua Achaar Vichar

Abubuwan da muka gada duk ɗoyi suke yi yanzu, duk al'adar da falsafar ta watse. 

• Tel Dekh Tu Tel Ki Dhaar

Dubi yadda datti ke malala. 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• Mehak Rahi Hai Desh Ki Galiyaan, Saans Lena Ho Gayo Muhaal

Duk hanyoyin gari sai wari suke, numfashi ma wahalar fita yake. 

• Swachh Banega Bharat Khud Hi, Dekh Le Apne Ghar Ka Haal

Shin sai yaushe ne Indiya za ta yi fes, dubi yadda lamarin ya ɓaci. 

• Nadi Kinare Baithega Tu, Sab Paani Mein Mil Jayego

Idan mutum ya tsuguna ya yi fitsari a gefen rafi, duk sai ya haɗe da ruwan kogin. 

• Wahi Bahega Nalkon Se, Phir Usko Hi Tu Pee Jayego

To kuma wannan ruwan ne dai yake dawo muku a famfo, maza ai sai a sha. 

• Haath Mein Leke Izzat Apni, Khada Hai Tu Kyun Maidaano 
Mein

ME yasa kuke tsaye a filin Allah da taƙamar ku a hannu? 

• Dikhe Koi Jo Dhar Maarta, Rapat Likha Do Tum Thaano Mein

Idan kuka ga wani na fitsari a fili, ku shigar da ƙorafi wa 'yan sanda. 

• Khule Mein Hai Jo Shaan Agar Toh, Dhoti Pehan Na Chhod De

In kuma kuna ganin akwai wata fa'ida ce da ke tattare da fitsari a fili sai ku daina saka kaya ma. 

• Har Cheez Parampara Nahi Re Pyaare

Ba komai ne yake al'ada ba masoyi/masoyiya. 

• Aad Tu Lena Chhod De (x3)

Ku daina tsaya a bayan irin waɗannan al'adun. 

• Mil Kar Mauka Na Sabhayta Pe Phaad

Kada ku lalata mana al'ada da miyagun aiyukan ku. 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

• Kab Tak Lega Tu Pedon Ki Aadh

Tsawon yaushe ne za ka ci gaba da tsuguno a gindin bishiyoyi? 

• Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki. 

• O Bhaiya Dhaad Dhaad Dhaad Kar Le Ab Toh Toilet Ka Jugaad

To ɗan uwa yi maza ka fara haɗa kayan banɗaki

©️✍🏻
 Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com 

BESHARAM RANG DA HUKUMAR TACE FINA-FINAN INDIYA



Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasar India (CBFC) Ta Umarci Kamfanin YASH RAJ FILM da Duk Masu Ruwa da Tsaki Na Shirya Gagarumin Film ɗin Jarumi Shah Rukh Khan da Deepika Padukone Me Taken PATHAN da Suyi Sauye-Sauye na Wasu Ɓangarori na Film ɗin Musamman Waqar Nan Me Taken Besharam Rang Wanda Ake Ta Cece Kuce Akan ta Na Cewa Tsarin ta Yazo da Rashin Dacewa Duk Da Wasu Suna Ganin Kwata-kwata Be Dace Wani Dalili Ya Saka a Soki Waqar Ba Domin An Saba Duk Wani Abu da Aka Gani Cikin Waqar Bollywood Sunayi. Daman Kuma Tuni Mutane Suna Surutun Se An Ƙauracewa Wannan Film Watau Boycotting ɗin sa. Kamar Yanda Aka Yiwa Wasu Fina-finan.
Amma Sau da Yawa Wannan ma Wata Nasara ce Saboda Hakan ma Tallatawa Masu Film Akeyi Wani Lokacin Kuma Ana Bawa Film Matsala.

#AbbaIndiaDala

LOKACI ALƘALI



LOKACI ALƘALI

Ƙaurace wa finafinai musamman idan fim ne na daga cikin finafinan 3 Khans ba sabon abu bane a India. 

Misali a lokacin sakin fim ɗin Shah Rukh khan mai suna “My Name Is Khan” a shekarar 2010, wani daga cikin ‘yan adawan (Shah Rukh Khan) sa mai suna Debsena shine gaba-gaba wurin haɗa gangamin ƙauracewa wannan fim ɗin. Sun yi du wasu ababe na tsana a kan wannan fim ɗin kaama daga yage fastoci (posters), sambaɗawa wasu daga cikin gidajen kallon da za’a haska fim ɗin wuta da dai shauran aikata du wasu ababe na ƙiyayya amma daga karshe hakarsu bai cimma ruwa ba domin fim ɗin ya samu gagaruman nasara! A karshe ma masoyan Shah Rukh Khan ɗin godiya irin na shaguɓe suka kama yi musu akan sun gode da hauragiyar da suka kama yi wanda hakan yayi sanadiyyar ɗaukakar fim ɗin.

Eh sosai, babu wani riba da suka samu akan hauragiyar da suka yi kuma ba zasu taɓa samu ba. Tun lokacin da aka saki ƙaramar tallar (teaser) na fim ɗin Pathan maƙiya da mahassada suka shiga aikinsu na kira da kala-kalan murya akan a fito a ƙaurace wa fim ɗin. Toh saboda me?? Saboda ƙiyayya! Toh ƙiyayya a kan me? A kan SRK! Laifin me yayi musu? Tohm wata ƙil koh dan musulmi ne? kuma hakane fa, domin idan zamu lura ba iya SRK kawai akayi wa hakan ba koh Aamir Khan ma fim ɗinsa na baya-bayan nan mai suuna “Laal Singh Chaddah” ya sha kashi a wurin ‘yan-ta-ƙaura (Boycutters) du dai saboda shima Khan ne koh??? Toh kusan hakane domin tun a fim ɗin (Aamir Khan) sa “PK” ma’abota bautar gumaka sunce ya ci wa ababen bautarsu da addinansu fuska don haka tun a wannan lokacin ne suka kurɓi ruwan alwashin cewa du wani fim nasa zasu kaurace masa. Domin Allah ya ƙara tabbatar wa da masu Imani cewa addinin bautar wanin Allah ba gaskiya bace kuma babu wani abun bauta da gaskiya sai shi Allah yasa fim ɗin na PK yayi gagaruman Nasara.

Tohm koma dai meye, fim ɗin Shah Rukh Khan ‘Pathan’ a ranar laraba 25th January 2023 zai fita shin koh ya zata kaya idan aka saki fim ɗin????

Shin Haƙar 'yan-ta-ƙaura zai cimma ruwa na ganin fim ɗin ya faɗi??? 

A’a koh ‘yan-ta-ƙaura zasu mayar da wuƙaƙensu a kube ne su zuba wa sarautar Allah ido koh kuwa za suyi irin yadda suka yi ne lokacin da aka saki fim ɗin MNIK???

LOKACI ALKALI

 🖋 UMAR FAROOQ SULAIMAN

KO ME YAYI ZAFI HAKA 😨🤔


KO ME YAYI ZAFI HAKA 😨🤔 Tunisha Sharma Commiting Suicide

A jiya asabar ne Jaruma "Tunisha Sharma" wacce aka fi sani da fitowa a fina-finan gidan TV masu dogon zango ta rataye kanta a banɗaki a yayin da suke tsaka da ɗaukar wani Film mai suna Ali Baba: Dastaan-E-Kabul, 

Jarumar dai tana kan ganiyar ta domin kuwa shekarunta 20 cif, a halin yanzu,

An haife ta a a shekarar 2002, ta fito a fina-finai irin su; Fitoor, Baar Baar Dekho, Dabangg 3, Kahaani 2, da dai sauransu, inda ta fara sun tana da shekaru 14,

Ana cikin ɗaukar Film ne dai jarumar tace zata shiga banɗaki, ko da aka jita shiru sai aka bita ciki aka tarar tuni ta rataye kanta, nan take aka wuce da ita asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar tata aka miƙa ta zuwa ga alhalin ta.

@AyƘoƘi

FASSARAR WAƘAR TU CHALE

FASSARAR WAƘAR TU CHALE




Waƙa: Tu Chale

Shiri: I 

Shekara: 2015 

Sauti: A.R.Rahman

Rubutawa: Irshad Kamil

Kamfani : T-Series

Rerawa: Shreya Ghoshal & Arijit Singh

Fassarawa: Haiman Raees 

*. Tu Chale… Sang Chale Sabhi Gul

Dukkanin furanni kan biyo ki yayin da kike tafiya. 

*. Apna Hai Yeh Khayal (x2)

Abin da na yi imani da shi kenan. 

*. Tu Chale… Sang Chale Sabhi Gul

Dukkanin furanni kan biyo ki yayin da kike tafiya. 

*. Apna Hai Yeh Khayal (x2)

Abin da na yi imani da shi kenan. 

*. Hai Aisa Lage Wahan Roz Khilein Gul

Da alama furanni na ƙara yaɗuwa

*. Jahaan Tera Aana Jaana

A duk wajen da ki ka ziyarta. 

*. Hai Aisa Lage Gul Galti Se Ban Gaye

Da alama an halicci furanni ne bisa kuskure. 

*. Rab Ne Tha Tujhe Banana

Yayin da ubangiji ya ke halitta ki. 

*. Yeh Mehka Mausam Husn Ka Aalam

Wannan wurin mai ƙamshi, wannan wurin mai kyawu. 

*. Hai Teri Hi Parchhayi

(Ba komai bane fa ce) inuwar ki ce kawai. 

*. Apna Hai Yeh Khayal (x2)

Abin da na yi imani da shi kenan. 

*. Tu Chale… Sang Chale Sabhi Gul

Dukkanin furanni kan biyo ki yayin da kike tafiya. 

*. Apna Hai Yeh Khayal (x2)

Abin da na yi imani da shi kenan. 

- De Na Dhin Dhar Ta Ne Na… De Na Na… Aaa…

(salon bin waƙa ne na indiyawa da ba shi da tsayayyar ma'ana)

*. Tu Na Jaane… Na… Main Jaani

Kai ba ka sani ba, nima ban fahimta ba. 

*. Na… Na Maane

Kuma ba mu yi imani da hakan ba. 

*. Jaana Tera Khayal, Jaana Tera Kya Haal

Tunanin me ka ke yi masoyina? Yaya ka ke ji masoyina? 

*. Tere Jiya Ke Taal Surmayi

Sautin zuciyarka mai tsarki ne. 

*. Aankhon Mein Hai Shabaab

Idanuwanka cike su ke d gamsarwa. 

*. Jaise Khile Gulaab

Kamar fure mai yaɗo 

*. Dekhein Aise Hi Khwaab Hum Kayi…

Ina ganin mafarkai irin waɗannan da yawa a kwanakin nan. 

*. Tere Aane Se Yaar Aisa Aaya Nikhaar 

A sanadin isowar ki, wani annuri ya zo. 

*. Jaise Aayi Bahaar Ho Nayi

Kamar dai zuwan lokacin bazara. 

*. Tere Hothon Ke Jaam

A gamsassun laɓɓan ki. 

*Pee Loon Subah Shaam

Na ke so in ta yin maye. 

*. Tu To Mera Hi Naam Ho Gayi…

Yanzu kin zama tawa 

*. Meri Duniya Mein Tune Hai Rang Bhara

Ka cika duniya ta da kaloli. 

*. Meri Saath Yeh Duniya Dekh Zara

Mu je mu zaga duniya tare. 

*. Meri Tu Hi To Hai Pyari Duniya, Saari Duniya

Ke ce duniya ta abar ƙauna, ke na ɗauka a matsayin duniya ta. 

*. Mere Humkadam…

Ya kai abokin tarayya... 

*. Tu Chale… Sang Chale Sabhi Gul

Dukkanin furanni kan biyo ki yayin da kike tafiya. 

*. Apna Hai Yeh Khayal (x2)

Abin da na yi imani da shi kenan. 
 
*. Hai Aisa Lage Wahan Roz Khilein Gul

Da alama furanni na ƙara yaɗuwa

*. Jahaan Tera Aana Jaana

A duk wajen da ki ka ziyarta. 

*. Hai Aisa Lage Gul Galti Se Ban Gaye

Da alama an halicci furanni ne bisa kuskure. 

*. Rab Ne Tha Tujhe Banana

Yayin da ubangiji ya ke halitta ki. 

*. Yeh Mehka Mausam Husn Ka Aalam

Wannan wurin mai ƙamshi, wannan wurin mai kyawu. 

*. Hai Teri Hi Parchhayi

(Ba komai bane fa ce) inuwar ki ce kawai. 

*. Apna Hai Yeh Khayal (x2)

Abin da na yi imani da shi kenan. 

*. Door Khile Rang Kaun Sa

Wani kala na sheƙi a can nesa. 

*. Rang Tera Hai Batlana

Sanar da ni cewa kalannan naka ne. 

*. Lo Haath Se Chhoota Dil

Kalli, zuciyata na sulluɓewa daga hannuwana. 

*. Rang Tere Maine Rang Hai Jaana…

Ina so in kalantu a cikin kalolin ka 

*. Mehak Gayi Hai Le Khushboo

Ƙamshi ya watsu a samaniya. 

*. Mehka Tera Jo Hai Yeh Aanchal

Hatta mayafin ki ma ya koma ƙamshi. 

*. Phoolon Ki Tu Hai Raani

Ke ce Sarauniyar furanni. 

*. Ya Phir Tu Hai Koi Sandal…

Ko kuma (ace) ke itacen sandal ne. 

*. Dheemi Dheemi Baatein, Sehaj Sugam Mausam

(yi) magana a hankali, wannan lokacin mai haƙuri ne. 

*. Piya Mere Aise Mausam Ab Aayenge Hardam

Ya masoyina, irin wannan yanayin zai ci gaba da zuwa har abada. 

*. Tu Jo Mujhe Haasil, Naina Kare Jhilmil

Tun da na same ki, idanuwana su ka fara ƙyalli. 

*. Saathi Tere Hone Se Hai

Saboda wanzuwarki ne abar so na. 

*. Khushiyon Ke Yeh Kaafile…

Wannan sunƙin murmushin ya wanzu. 

*. Tu Chale… Sang Chale Sabhi Gul

Dukkanin furanni kan biyo ki yayin da kike tafiya. 

*. Apna Hai Yeh Khayal (x2)

Abin da na yi imani da shi kenan. 

*. Hai Aisa Lage Wahan Roz Khilein Gul

Da alama furanni na ƙara yaɗuwa

*. Jahaan Tera Aana Jaana

A duk wajen da ki ka ziyarta. 

*. Hai Aisa Lage Gul Galti Se Ban Gaye

Da alama an halicci furanni ne bisa kuskure. 

*. Rab Ne Tha Tujhe Banana

Yayin da ubangiji ya ke halitta ki. 

*. Yeh Mehka Mausam Husn Ka Aalam

Wannan wurin mai ƙamshi, wannan wurin mai kyawu. 

*. Hai Teri Hi Parchhayi

(Ba komai bane fa ce) inuwar ki ce kawai. 

*. Apna Hai Yeh Khayal (x2)

Abin da na yi imani da shi kenan. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Facebook: Haiman Raees 

Infohaiman999@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring

FASSARAR WAƘAR TU HI TOH HAI

FASSARAR WAƘAR TU HI TOH HAI 




🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

• Waƙa - Tu Hi Toh Hai

• Shiri - Holiday

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2014

• Sauti - Pritam

• Rubutawa - Irshad Kamil

• Kamfani Zee Music Company 

• Rerawa - Benny Dayal

• Fassarawa - Haiman Raees 

• Awaaragi, Karta Hoon, Par Main Aawara Nahi

Na kan yi hauka, amma ni ba mahaukaci bane. 

• Chhoda Khulla, Dil Ko Magar, Khudko Bigaada Nahi

Na bai wa zuciyata cikakken 'yanci, amma ban sangartata ba. 

• Aisa Lage, Tere Bina, Ab Toh Guzaara Nahi

Da alama abu ne mai wahala in tafiyar da wani lokaci ba tare da ke ba. 

• Kisika Bhi, Honga Na Main, Hua Jo Tumhara Nahi

Ba zan kasance tare da kowa ba in ba ke ba. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Zinda Hoon Tujhpe Marke

Ina raye ne saboda ina mutuwa akanki. 

• Bhoola Sab Kuch Tujhko Padhke

Na manta komai tun daga lokacin da na karanta zuciyarki. 

• Kaise Hai Pyaar Tera Haan…

Kalli yadda na zama a soyayyarki... 

• Jo Meri Khwahishein Tujhi Se Hi Lipat Gayi

Muradaina sun amshe ki. 

• Kyun Meri Duniya Tujhi Mein Hai Simat Gayi

Yanzu duniyata a kulle take da ke. 

• Na Jaane Kaise Ghatnayein Hai Yeh Ghat Gayi

Bansan ta yaya waɗannan abubuwan suka faru ba. 

• Main Fida Hoon Tujh Par

Na yi hauka sosai a kanki. 

• Jo Saari Baaziyaan Khayalon Ki Ulat Gayi

Duk cacar da ke kaina sun juye. 

• Kyun Meri Chaahatein Tujhi Pe Mar Mit Gayi

Na sallamar da soyayyata kaf a kanki. 

• Na Jaane Kaise Ghatnayein Hai Yeh Ghat Gayi

Bansan ta yaya waɗannan abubuwan suka faru ba. 

• Main Fida Hoon Tujh Par

Na yi hauka sosai a kanki. 

• Naaraazgi, Teri Ada…

Yawan fushi shi ne salon ki... 

• Pyaari Lagi, Teri Ada…

Salon naki ma na ga abin so ne. 

• Hai Saadgi, Teri Ada…

Sauƙin kai shi ne salon ki... 

• Yeh Jaadu Hai Kaise Tera

Wane irin sihiri ne ke tattare da ke haka? 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Main Ana Tere Aage Dekho Dil Haara Hoon

Kalli, na rasa zuciyata a gabanki. 

• Main Ana Jaise Bhi Hoon Jo Bhi Hoon Tumhara Hoon

Koma menene ni, ni kawai naki ne. 

• Jo Teri Chaahatein Samete Woh Kinara Hoon

Ni be gaɓar nan da ke karɓar soyayyar ki. 

• Kaise Main Yeh Kahoon

Ta yaya zan iya bayyana miki hakan duka? 

• Main Ana Tere Liye Zameen Pe Utaara Hoon

Saboda ke ce kawai na faɗo duniya. 

• Main Teri Bholi Bhaali Aankhon Ka Ishaara Hoon

Ni ne alamar da idanuwanki ke bayarwa. 

• Jo Teri Chaahatein Samete Woh Kinara Hoon

Ni be gaɓar nan da ke karɓar soyayyar ki. 

• Kaise Main Yeh Kahoon

Ta yaya zan iya bayyana miki hakan duka? 

• Tu Paas Bhi, Zara Zara…

Kina kusa da ni, kaɗan. 

• Tu Pyaas Bhi, Zara Zara…

Ke ce ƙishirwata, kaɗan. 

• Tu Raaz Bhi, Zara Zara…

Ke ce sirrina, kaɗan. 

• Main Ho Gaya Hoon Tera

Na zamo naki. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Tu Hi Toh Hai Khayal Mera

Kina nan a cikin tunanina. 

• Tu Hi Toh Hai Qaraar Mera

Zaman lafiyata yana tare da ke. 

• Jhoothe Nashe, Jahaan Ke Sabhi

Duk wani maye a wannan duniyar ƙarya ne.

• Tu Hi Toh Hai Khumaar Mera

Ke ce maye na. 

• Zinda Hoon Tujhpe Marke

Ina raye ne saboda ina mutuwa akanki. 

• Bhoola Sab Kuch Tujhko Padhke

Na manta komai tun daga lokacin da na karanta zuciyarki. 

• Kaise Hai Pyaar Tera Haan…

Kalli yadda na zama a soyayyarki... 

©️✍🏻
 Haiman Raees 
Infohaiman999@gmail.com 

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

FASSARAR WAƘAR THE PAD MAN SONG

🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻



FASSARAR WAƘAR THE PAD MAN SONG 

• Waƙa - The Pad Man Song

• Shiri: Padman

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2018

• Sauti - Amit Trivedi

• Rubutawa - Kausar Munir

• Kamfani - Zee Music Company

• Rerawa - Mika Singh

• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman

• Superhero, Superhero, Superhero, Haaye, Haaye, Haaye, Haaye…

Jarumi, Jarumi, Jarumi, Ayye, Ayye, Ayye, Ayye... 

• Ho… Thaanye Thaanye Na Goli Maare

Shi ba harba harsasai yake ba. 

• Dhaanye Dhaanye Na Entry Maare

Shi ba shigowar bajinta yake ba. 

• Slow Motion Mein Haddi Tode Na

Shi ba karya ƙasusuwa yake yi a hankali ba. 

• Arre Building Se High Jump Na Maare

Ba tsalle yake yi daga dogayen gine-gine ba. 

• Neeche Se Dialogue Na Maare

Ba ya ambato zantuka daga ƙasa 

• High Speed Mein Naache Gaaye Na

Shi ba rawa da waƙa yake yi da sauri ba. 

• Ho… Na Koi Multi-Storey Bangla

Shi bashi da ginin bungalo mai hawa biyu. 

• Na Hai Koi Udan Khatola

Shi bashi da abin hawa mai tashi sama. 

• Par Superhero Hai Yeh Pagla

Amma wannan zararren mutumin duk da haka jarumi ne. 

• O Waah Re Waah Re Waah Re Waah Re…

Ah Dakyau! Dakyau! Dakyau! O 

• Pad Man… Pad Man… O Pad Man…

Mai ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... 

• O Yeh Hai Mad Mad Mad Mad…

Shi cikakken mahaukaci ne. 

• Pad Man… Pad Man… O Pad Man…

Mai ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... 

• O Yeh Hai Mad Mad Mad Mad…

Shi cikakken mahaukaci ne. 

• Pad Man…

Mai ƙunzugu 

Hey Hey Hey Hey….

• O Kaali Kalkatte Waali

Jinjina ga abar bauta Kali na Kolkata!

• Bhabhi Didi Biwi Saali

Ko surika ce ko mata 

• Poori Ya Aadhi Ghar Waali

Abokiyar zama ce ko budurwa. 

• Ya Ho Maiyya…

Ko ma Mahaifiya ce. 

• Item Ho Ya Laaj Ki Moorat

Ko 'yar batsula ce ko mai kamun kai ce. 

• Har Naari Ko Iski Zaroorat

Kowace mace tana buƙatar wannan. 

• Dhanno Ho Ya Munni Ho Ya Sheila, Laila…

Ko da Dhanno ce , Munni, Sheila ko kuma Laila

Hey Hey Hey Hey….

• Ho… Harkatein Risky, Risky

Aikinsa akwai kasada a ciki. 

• Fikar Isse Kiski, Kiski

Yana damuwa matuƙa akan kowa. 

• Hai Yeh Namuna Number One Ziddi…

Shi na musamman ne kuma ga taurin kai. 

• Kahe Jo Koi Kuch Bhi, Kuch Bhi

(Bai damu ba) da abinda kowa zai ce (game da shi)

• Raah Chale Sach Ki, Sach Ki

Shi kullum hanyar gaskiya yake bi. 

• Lagta Hai Yeh Kudrat Ki Galti…

Da alama dai shi kuskure ne a ƙaddara. 

• Haan Bhaad Mein Jaaye Re Angreji

Turanci ya ci ƙaniyarsa. 

• Nahi Chaahiye Imported Degree

Shi bai damu da baƙon digiri ba. 

• Made In India Hai Yeh Jigri

Mutum ne shi mai nagarta ɗan Indiya. 

• O Waah Re Waah Re Waah Re Waah Re…

Ah Dakyau! Dakyau! Dakyau! O 

• Pad Man… Pad Man… O Pad Man…

Mai ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... 

• O Yeh Hai Mad Mad Mad Mad…

Shi cikakken mahaukaci ne. 

• Pad Man… Pad Man… O Pad Man…

Mai ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... Mai Ƙunzugu... 

• O Yeh Hai Mad Mad Mad Mad…

Shi cikakken mahaukaci ne. 

• Pad Man…

Mai ƙunzugu 

• Superhero, Superhero, Superhero, Haaye, Haaye, Haaye, Haaye…

Jarumi, Jarumi, Jarumi, Ayye, Ayye, Ayye, Ayye... (x2)

©️✍🏻
 Haiman Raees 
Infohaiman999@gmail.com 

Happy Birthday Akshay Kumar 

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

FASSARAR WAƘAR TAY HAI

FASSARAR WAƘAR TAY HAI 




Waƙa: Tay Hai

Fim: Rustom 

Harshe: Hausa

Shekara: 2016 

Sauti: Ankit Tiwari

Rubutawa: Manoj Muntashir

Kamfani: Zee Music Company

Rerawa: Ankit Tiwari

Fassarawa: Haiman Raees
 

Mmm… Hoo… Ra Ra Re…

• Tere Bin Jee Na Paunga

Ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. 

• Sach Much Mar Hi Jaunga

Mutuwa zan yi haƙƙun. 

• Yeh Tay Hai… Yeh Tay Hai…

Wannan haka yake, wannan haka yake. 

• Hasna Rona Tujhse Hi

Kece dalilin dariya da kuma kuka na. 

• Mera Hona Tujhse Hi

Ina wanzuwa ne kawai saboda ke. 

• Yeh Tay Hai… Yeh Tay Hai…

Wannan haka yake, wannan haka yake. 

• Maujood Hai Har Saans Mein

Ki na cikin kowane numfashi nawa. 

• Tu Har Dafa Yeh Tay Hai

A kowane lokaci, wannan haka yake. 

• Tu Hai Dawa Ya Dard Hai

Shin ke magani ce ko raɗaɗi ce? 

• Par Hai Mera Yeh Tay Hai

Amma ke tawa ce, wannan haka yake. 

• Maujood Hai Har Saans Mein

Ki na cikin kowane numfashi nawa. 

• Tu Har Dafa Yeh Tay Hai

A kowane lokaci, wannan haka yake. 

• Tu Hai Dawa Ya Dard Hai

Shin ke magani ce ko raɗaɗi ce? 

• Par Hai Mera Yeh Tay Hai

Amma ke tawa ce, wannan haka yake. 

• Tere Bin Jee Na Paunga

Ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. 

• Sach Much Mar Hi Jaunga

Mutuwa zan yi haƙƙun. 

• Yeh Tay Hai… Yeh Tay Hai…

Wannan haka yake, wannan haka yake. 

• Tu Naseebon Sa, Mere Haathon Pe, Shuru Se Likha Hai

Ki na rubuce a cikin ƙaddarata tun da fari. 

• Mera Haq Hai Tu, Aasmano Se, Mujhe Jodta Hai

Ke ce daidai na, ke ce mahaɗi na da aljanna. 

• Tere Kadmon Pe, Jahaan Rakh Doon Main, Kabhi Jo Kahe Tu

Zan ajiye duniya gaba ɗayanta a ƙasan ƙafarki in kina buƙatar hakan. 

• Koi Shaq Ho Toh, Aazma Lena, Kisi Din Mujhe

In kuma kina da tantama to ki gwada ni duk ranar da kika so. 

• Maujood Hai Har Saans Mein

Ki na cikin kowane numfashi nawa. 

• Tu Har Dafa Yeh Tay Hai

A kowane lokaci, wannan haka yake. 

• Tu Hai Dawa Ya Dard Hai

Shin ke magani ce ko raɗaɗi ce? 

• Par Hai Mera Yeh Tay Hai

Amma ke tawa ce, wannan haka yake. 

• Maujood Hai Har Saans Mein

Ki na cikin kowane numfashi nawa. 

• Tu Har Dafa Yeh Tay Hai

A kowane lokaci, wannan haka yake. 

• Tu Hai Dawa Ya Dard Hai

Shin ke magani ce ko raɗaɗi ce? 

• Par Hai Mera Yeh Tay Hai

Amma ke tawa ce, wannan haka yake. 

• Tere Bin Jee Na Paunga

Ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. 

• Sach Much Mar Hi Jaunga

Mutuwa zan yi haƙƙun. 

• Yeh Tay Hai… Yeh Tay Hai…

Wannan haka yake, wannan haka yake.

ƘARIN HASKE: Wannan waƙa ce ta soyayya zalla kuma tana bayyana irin ƙaunar da jarumin ke yi wa maaoyiyarsa, sai dai akwai buƙatar a kiyaye irin Kalaman da ake furtawa yayinda aka shiga sauƙin soyayya saboda kada a yi tsallen taɓarya. Nagode

©️✍🏻
 Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com 

FASSARAR WAƘAR SHAITAN KA SAALA

FASSARAR WAƘAR SHAITAN KA SAALA 



 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻AKSHAY KUMAR FANS NIGERIA 🇳🇬🕺🏻🇮🇳🕺🏻

• Waƙa - Shaitan Ka Saala 

• Fim - Housefull 4

Shekarar Fita - 2019

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Sauti - Sohail Sen 

• Kamfani - T-Series 

• Rubutawa - Farhad Samji 

• Rerawa - Vishal Dadlani & Sohail Sen 

• Fassarawa - Haiman Raees 

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... Ravan ne hai paala 

Ni ne Bala ... Ravana ne ya tayar da ni. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... Ravan ne hai paala 

Ni ne Bala ... Ravana ne ya tayar da ni. 

• Sab kahe mujhe shaitan ka saala ... Bala Bala Bala Bala 

Kowa na kira na da abokin shaiɗan.

• Looto looto looto looto japta hoon mala ... Bala Bala Bala Bala 

Na kan zurfafa tunani kuma in yi wa mutane sata. 

• Sab kahe mujhe shaitan ka saala ... Bala Bala Bala Bala 

Kowa na kira na da abokin shaiɗan.

• Log bole Bala kya cheez hai saala ... Bala Bala Bala 

Mutane na cewa Bala haɗaɗɗe ne. 

• Log bole Bala kya cheez hai saala ... Bala Bala Bala 

Mutane na cewa Bala haɗaɗɗe ne. 

• Ravan ne hai paala bole beti, mausi, khala

Duk matan sun ce Ravana ne ya tayar da ni. 

• Gore se gore ka munh karta hoon kaala 

Ina iya sukar mafiya girma daga cikin su. 

• Khud ki Diwali aur auron ka diwala

Murna nake yi yayin da wasu ke kuka. 

• Bala Bala Bala Bala chichori pathshala 

Makarantar Bala cike take da fitina. 

• Bala Bala Bala Bala keeda of the naala 

Bala ƙwaron cikin kwata ne. 

• That's right! 

Haka yake. 

• Khata hoon main murga dalke masala 

Nakan ci kaji masu yaji sosai. 

• Gareebon ke munh se cheenu main niwala

Nakan sace abinci daga bakin talaka. 

• Bala Bala Bala Bala peg patiala 

Bala tamkar ƙaton tulun giya yake. 

• Bala Bala Bala Bala keeda of the naala 

Bala ƙwaron cikin kwata ne. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... Ravan ne hai paala 

Ni ne Bala ... Ravana ne ya tayar da ni. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala Bala Bala chichori pathshala 

Makarantar Bala cike take da fitina. 

• Bala Bala ... shaitan ka saala

Ni ne Bala... Abokin shaiɗan. 

• Bala Bala ... Ravan ne hai paala 

Ni ne Bala ... Ravana ne ya tayar da ni. 

💫 *AKKIANS NA ALFAHARI DA KU* 💫

©️✍🏻
 Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com 

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 05


DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 

Kashi Na ɗaya 03

Fitowa Ta Biyar 05

Daga Haiman Raees 

Bismillahir Rahmanir Raheem. 

Barkan Mu da Warhaka. 

A wanna fitowa kuma zan kawo muku wasu Zantuttuka ne na wannan Jarumi waɗanda su ke ƙunshe da saƙonni na soyayya, jan hankali da kuma Nasiha dangane da abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum. Mafi yawancin waɗannan zantuka ya furta su ne a wajen tarukkan sa aka gayyace shi. Ga su kamar haka:

1. “Kada ka zama masanin Falsafa kafin ka zama mai kuɗi". (har sai ka zama mai kuɗi) 
 
 2. "Kada ku bari abubuwan da kuke tsoro su zama kwalayen da zasu rufe ku. Ku Buɗe su, ku ji su kuma ku maida su manyan abubuwan da zasu dinga ƙarfafa muku guiwa. Na yi muku Alƙawari babu abinda zai ɓaci". (idan kuka aikata hakan). 
 
3."Ku yi karatu sosai, ku yi wasa Matuƙa. Kada ku bari wani abu ya dakatar da ku, kuma kada ku sake ku rayu a cikin mafarkin wani". 

 4. "Ruɗu wata hanya ce ta samun fahimta a duniya. Kada ka damu da shi sosai, kuma kada ka taɓa ɗaukan kanka da muhimmanci ta yadda zaka yarda da Ra'ayin ka har ya kai matakin da zaka daina girmama Ra'ayin sauran Mutane". 

5. “Nasara da rashin ta duk wani ɓangare ne na Rayuwa, dukkan su suna zama ne na dindindin". 

 6. "Ka bayar da wani abu naka zuwa ga mutane, kuma yayin da kake yin hakan, ka tabbata ka fahimci cewa ba wai kyautatawa wani kake yi ba. Komai Kuɗin ka, komai Nasarar da ka samu ko ɗaukakar da kayi, kada ka sake ka raina girman da jama'a suke baka kawai ta hanyar zaman su masu karɓar kyautatawa daga gare ka".
 
7. "A duk lokacin da rayuwa ta yi maka ɗaurin minti, (ka sani cewa) ƙatuwar mota ba zata iya kwantar maka da hankali ba. Amma karamcin aboki yana iya yin hakan, kuma idan kaga baka samu nutsuwa irin wacce kake so ba, kada ka ruɗe. Komai na daidaituwa ne a hankali". 
 
8. "Duk wani suna da zaka kira kanka da shi, ko wanda wasu ke kiran ka da shi matakai ne kawai. Ba da su ne za'a bayyana ka ba, komai kyawun su ko munin su. Abinda Ke bayyana haƙiƙanin ko kai wanene ita ce zuciyar ka". 

9. "Duk iya aiki tuƙurun da za mu yi, Jagoranci ya nuna mana cewa dole mu tsammaci zuwan Masifa". 

10. "Duk wani abu da ke maida kai baya ba zai Ƙyale ka ba har sai ka miƙe mishi tsaye ka fara saita hanyar ka da dukkan ƙarfin ka izuwa inda kake son zuwa. Don haka, ku bar Haniniya ku fara tafiya".

11. "Idan a karan farko baka yi nasara ba, yi sabon shiri sannan ka ƙara jarrabawa".

12. "Farinciki da baƙin ciki duk wasu ɓangarori ne na tabbatar rayuwa. Rayuwa tana tafiya daidai ne sakamakon canjin da ke wakana a tsakanin su. Kada ka ta'allaƙa kanka da ko ɗaya daga cikin su, domin a hankali kowannen su yana iya canzawa. Ka tafi da su tare kana mai yarda da cewa kowannen su zai zo ya wuce, ka yiwa kanka dariya idan kaga kana gab da Wargajewa, ka yi kuka idan kaga wani kafce na ya baka dariya". 

13. “Nasara ba Malamar ƙwarai bace, rashin nasara ita ce". 

14. "Ku rayu tun daga zuciya, ku yi soyayya, ku so mutane, ku so duniyar da take kewaye da ku, ku so dabbobi da Tsuntsaye, da manyan Birane da kuma tsaunuka, ku so Mafarkai, ku so rayuwa, ku so ayyukan ku, ku so abokan ku harda maƙiyan ku ma ko da kuwa ba da san ranku ba. Amma abu mafi muhimmanci abokai na, ku so kawunan ku". 

15. "A duk lokacin da naji ina jin girman kai, sai in tafi Ƙasar Amurka. Jami'an shige da ficen nan suna Korar Jarumi daga cikin shahara ta". 

16. "Ku rayu ayau, ba lallai bane ku hango hakan saboda matasan idanun ku, amma yanzu lokaci ne mai muhimmanci kamar yadda zaku iya samu a rayuwa. Saboda gobe duk mutuwa zamu yi". 

17. "Babu wani Lokaci ko wuri da ya fi dacewa da soyayya, so shi bashi da Shekaru". 

18. "Rayuwa tana farawa ne daga lokacin da muka yanke Shawarar cewa zata fara mana".

19. "Babbar Nasarar da na samu a rayuwa ita ce ina iya sanya mutane da dama murmushi ko da kuwa a jikin tallan Kamfanin Lux ne". 

20. “gudu na ke a Gasar tsere su kuma mutane suna ɗaya layin, tsere na ke yi da kaina". 

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah 

HAIMAN RAEES 
Twitter: @HaimanRaees 
 Instagram: Haimanraees 
 Infohaiman999@gmail.com

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 04



DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 

Kashi Na ɗaya 02

Fitowa Ta huɗu 04

Daga Haiman Khan Raees 

Bismillahir Rahmanir Raheem. 

Barkan Mu da Warhaka. 

11. MOHABBATEIN: A Yayinda kake son mutum so na Haƙiƙa, ko mutuwa ba zata iya raba ku ba, domin ko da ɗayan ya mutu zai ci gaba da Wanzuwa a cikin zuciyar ɗayan. Ma'ana dai, daga lokacin da ka faɗa soyayya ta zahiri, to babu kai babu Kaɗaici. Har abada! 

12. KABHI KHUSHI KABHIE GHAM: A Rayuwa ba kullum ake kwana a gado ba, wani lokaci ka kan tsinci kanka a cikin farin ciki, wani lokaci kuma akasin haka. Amma ka sani cewa ahalin ka zasu kasance tare da kai a cikin kowane irin yanayi ka tsinci kanka. Idan kuwa soyayya ta ratso, to ka tsaya da kyau ka yanke hukuncin da ya dace, ko da ace ya saɓa musu, kada ka damu komai zai yi daidai. Ahali sun saba haka.

 13. MY NAME IS KHAN: 
A duk inda ka tsinci kanka a rayuwa, ka kasance mutum mai gaskiya da riƙon amana, ka zama mai cika alkawari kuma mai magana ɗaya. Kada ka raina mutum ko yaya yake, kada ka zalunci kowa. Ka taimakawa duk wani mai neman taimako ko da kuwa ba garin ku ɗaya ba, ko da yaren ku ba ɗaya ba kuma ko da Addinin ku ba ɗaya ba. Abu mafi muhimmanci kuma, kada ka ji tsoron bayyana Ra'ayin ka ko a ina ne. 

14. HUM TUMHARE HAIN SANAM: Yarda da juna shi ne ginshiƙin kowane irin zama zaka yi da wani. Ba zaku taɓa samun nagartacciyar zamantakewa ba Matuƙar baku yarda da juna ba. Sannan yanke hukunci cikin fushi da ƙiyayya yana iya tarwatsa alaƙar da ke tsakanin masoya kuma yana iya farraƙa su. Lallai ya kamata mutum ya kula da kyau yayin yanke hukunci don kada ya bar baya da Ƙura. 

15. MAIN HOON NA: Haƙiƙa so Makaho ne, kuma so mahaukacin abu ne, don haka babu wata damuwa don kayi hauka a kan soyayya. Sannan shi so yana iya faruwa a kowane irin yanayi, a kowane waje, ga kowane mutum ba tare da duba tsari ko cancanta ba. Don haka kada kayi mamaki don kaga Tsofaffi suna soyayya, ko kuma kaga tsohuwa da yaro suna soyayya, dama abin haka yake. 

16. VEER-ZAARA: Kada ka ka bari wani abu yayi maka Iyaka da abinda kake so, domin shi so baya bin kowace irin doka face nashi. Babu abinda ya shafe shi da ƙasa, Addini, kalar fata, yare ko kuma ƙabilar Masoyan. Kana iya son duk wanda ya kwanta maka a zuciya ko wanene shi, daga baya komai ya biyo baya, kai dai kawai kayi so na gaskiya. 
Haka kuma fim ɗin ya koya mana cewa, ko da ace akwai wani Shamaki a tsakanin Masoyan gaskiya, wannan shamakin bai isa ya hana su jin ɗumin juna a cikin zukatan su ba. Kamar dai yadda Squadron Leader Veer Pratap Singh daga India 🇮🇳 ya kamu da son Zaara Hayat Khan daga Pakistan 🇵🇰. 

17. KABHI ALVIDA NAA KEHNA:

Wannan Fim ya sha suka daga mutane da dama kan rashin ɗa'a da halin banza da aka nuna a ciki. Amma hakan bai hana saƙon sa fitowa fili ba. Idan har Zamantakewar auren ku baya yi muku daɗi, kuna iya rabuwa da juna salin Alin. Domin cin Amanar juna a bayan fage ba zai magance muku matsalar ba, aure wani irin zama ne da yake buƙatar abokan zaman su so junan su dagaske, kuma su kula da juna yadda ya kamata.

18. JAB TAK HAI JAAN:
Wannan fim mai suna Jab Tak Hai Jaan ya baiwa mutane da dama damar fahimtar Camfi a zahirin sa da kuma irin yadda yake iya hana masoyan gaskiya kasancewa tare da junan su. Amma in har son na gaskiya ne, ƙaddarar ku zata haɗa ku daga Ƙarshe ko ana ruwa ko ana iska. 

19. RAEES: Duk da cewa wannan Fim ya samu mixed reviews a yayin fitowar sa, hakan bai hana saƙon da ke cikin sa fitowa ba. Abu na farko dai da fim ɗin yake koyarwa shi ne kowane ɗa yana buƙatar ya ɗauki maganar mahaifiyar sa da girma Matuƙa. A duk inda ta ce maka bari ka bari inda ta ce maka yi je kayi, zaka ga haske. Sannan a gidan ka fa lallai kana da iko, amma a mafi yawancin lokuta matar ka ita ke da iko akan Ikonka a cikin gidan, don haka wani abun fa dole sai dai kayi haƙuri kuma kayi shiru sannan ka maida shi wasa. 
Haka kuma ko wacce irin Harka zaka yi ka zamo mai gaskiya zaka ga ci gaba. Sannan kai tsaye fim ɗin ya tabbatar mana da cewa MAZA MA FA SUNA YIN KUKA, kuma yin wannan kukan bai kai ace za'a binciki mazantakar su ba.

20. FAN: Abu ne sananne cewa kowane Jarumi yana da masoya a duniya, kuma kowane Jarumi yana son Masoyan sa a ko ina cikin faɗin duniya. Amma me? Akwai wani mummunan tunani da yake shiga cikin zukatan wasu masu yiwa wasu jarumai Makauniyar soyayya na cewa, duk da cewa bai san su ba, ai da ya gansu zai gane su kuma zai karɓe su hannu biyu tare da girmama su. Saboda me? Tunanin su a iya kansu kawai ya tsaya. Wannan Fim na Fan yana ɗauke da darussa masu yawa wanda Alhamdulillahi mafi yawancin mutane basu so fim ɗin ba saboda gaskiyar da ya nuna, amma har cikin zuciyar su sun fahimci saƙon. Fan ya nuna mana cewa duk son da za ka yiwa mutum to kada ka zurfafa, kada ka zuba yawan tsammani a tsakanin ka da wanda kake so, kada ka taɓa barin abinda kake da shi don ganin ka samu abinda kake nema har sai ka samu tukun. Sannan, ba dukkan abinda kake gani bane yake haka a baɗini, kada kuma ka taɓa tsammanin cewa kafi kowa domin duk irin matakin da kake tunanin ka kai akwai wanda ya fi ka. Amma babban Darasin wannan shiri shi ne KA DA KA GAZA BADA HAƘURI GA WANDA KA SAƁA WA, KO MAI ƘANƘANTAR SA 

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.

Haiman Raees 
Twitter: @HaimanRaees 
 Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com 
 Infohaiman999@gmail.com

YAYIN DA MATASHIYAR JARUMA TA GABATAR DA AIKIN TA NA UMARA

YAYIN DA MATASHIYAR JARUMA TA GABATAR DA AIKIN TA NA UMARA.


Matashiyar Jaruma Jannat zubair rahmani Me Kimanin Shekaru 21 Ta Gabatar da Aikin nata Na Umarah a Karan Farko Tare da Ɗan Uwanta.
Jarumar ta Fito da Suna Natasha a Film Ɗin Jaruma Rani Me Taken Hichki Duk da Matashiyar Tafi Yin Film na Shirye shirye Gidan Talabijin Musamman Wani Me Taken Kashi – Ab Na Rahe Tera Kagaz Kora. Sannan A Yanzu Suna Gabatar da Shirin Khatron Ke Khiladi.

#AbbaIndiaDala

WANENE ROHIT SHETTY?



WANENE ROHIT SHETTY?

Rohit Shetty yana cikin Directors da babu kamarsa a tarihin Bollywood

Rohit Shetty director ne mai tarin nasara inda ya kasance yana cikin Directors din da suke da babbar nasara.

Rohit Shetty ya fara directing dinsa na farko a shekara ta 2003 inda ya fara da rashin nasara.

Zameen na Jarumi Ajay Devgn shine film na farko da Rohit Shetty ya fara directing inda film din ya karkare da Below Average.

Sai a shekara ta 2006 Rohit Shetty ya Kara directing din film dinsa na biyu me suna Golmaal Wanda ya kasance nasararsa dinsa na farko. Golmaal ya zama Hit a Box Office.

A shekara ta 2008 Rohit Shetty yayi film dinsa na uku me suna Sunday Wanda ya kasance Flop a Box Office. Hakan ne nuni da finafinansa guda uku na farko biyu sun fadi yayinda daya yayi nasara .

A shekara ta 2008 Rohit Shetty ya Kara dawowa da Golmaal Returns inda ya zama Hit.

A shekara ta 2009 Rohit Shetty yayi Directing din film dinsa na biyar me suna All The Best wanda shima ya samu nasarar zama Average a Box Office.

A shekara ta 2010 Rohit Shetty yazo da Golmaal 3 wanda ya kasance shine Blockbuster dinsa ta farko.

A shekara ta 2011 Rohit Shetty yayi Directing din Singham wanda ya kasance Super Hit a Box Office.

A shekara ta 2012 Rohit Shetty yayi Directing din film dinsa na 8 me suna Bol Bachchan Wanda ya samu nasarar zama Hit a Box Office.

Wani abunda zai baku mamaki duka wannan finafinai guda 8 da Rohit Shetty yayi Directing dinsu duk na Jarumi dayane wato Ajay Devgn inda duka ya fito acikin wannan finafinai guda 8.

A shekara ta 2013 Rohit Shetty yayi film dinsa na farko ba tare da Ajay Devgn ba wato Channai Express na Jarumi Shah Rukh Khan.

 Channai Express ya zama Blockbuster a Box Office sannan ya bawa Rohit Shetty damar 200cr a karo na farko sannan ya zama film dinsa na farko daya saida tickets na sama 2cr.

Singham Return shine film na 10 da Rohit Shetty yayi Directing Kuma shima nasara ce a Box Office inda ya zama Super Hit a shekara ta 2014.

Shekara ta 2015 Rohit Shetty ya kara gwada Jarumi Shah Rukh Khan bayan yayi Singham Return da Ajay Devgn, Rohit Shetty yayi Dilwale wanda ya samu nasarar zama Semi Hit a Box Office.

Golmaal Again a shekara ta 2017 shine film din Rohit Shetty na 12 Kuma shine Blockbuster dinsa ta uku.

A shekara ta 2018 ya Kara samun wata Blockbuster din da Simmba.

A shekara ta 2021 Right Shetty yayi Directing din Sooryavanshi inda ya zama Hit a Box Office.

Tun bayan rashin nasarar Sunday a shekara ta 2008 Rohit Shetty Saida ya shafe shekaru 14 ba tare da film dinsa ya Fadi a Box Office ba. Rohit Shetty ya jera finafinai guda 11 babu failure.

Rohit Shetty yana da finafinai guda 9 da suka saida tickets na sama da 1cr yayinda yake da guda 1 Wanda ya siyar da tickets na sama 2cr.

Rohit Shetty yana da finafinai guda 8 da suka haura 100cr yayinda aciki akwai guda uku da suka haura 200cr.

Channai Express shine film din Rohit Shetty nafi tara yan kallo a Cinema inda ya siyar da tickets na 2.52cr

Simmba shine film din Rohit Shetty da yafi kawo kudi inda ya kawo 239cr a India.

A yau ne aka saki film din Rohit Shetty na 15 wato Cirkus na Jarumi Ranveer Singh. Bisa dukkan alamu wannan film me suna Cirkus zai zama failure dinsa ta farko cikin shekaru 14😭

A yau Cirkus ya kawo 7cr wanda hakan ke nuni da wannan film ba zai ka labari domin bai samu yabo mekyau ba 😭

Rohit Shetty yayi Directing din finafinai guda 15 

Ajay Devgn ya fito a guda 10
Shah Rukh Khan a guda 2
Ranveer Singh a guda 2
Akshay Kumar a guda 1

Izuwa yanzu dai finafinai guda 2 ne kawai suka Fadi acikin guda 14 da suka gama kasuwa inda 12 suka samu karbuwa

Acikin guda 12 da suka karbu sun hada da 10 Clean Hits sai 4 Blockbusters

Wannan shine dan bayani akan Rohit Shetty

Daga Abdull Asa 

DARUSSAN TELUGU 15



✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿
DARUSSAN TELUGU
✿━━━ ✬◦ ❖ ◦✬ ━━━✿

            15

181. Dabbu teesukondi - karɓi kuɗin
182. Ippudu Kaadu - Ba yanzu ba
183. Meeku emi kaavali - me kake so?
184. Naaku Pantinoppi undhi - haƙorina na min ciwo
185. Shabdam cheyyakandi - Kada ka yi motsi
186. Nenu lopaliki raavachcha - zan iya shigowa ciki?
187. Idi naadi - Ni ne
188. Vaaram oru okkasari - sau ɗaya a sati
189. Nelalo okkasari - sau ɗaya a wata
190. Iroju thedi enti? - Yau nawa ga wata?
191. Iroju thedi March 03 - Kwanan wata yau 3 ga watan Maris
192. Naaku jvramga undhi - Ina fama da zazzaɓi
193. Naaku dhaggu undhi - Ina fama da tari
194. Naaku vaddu - bana so
195. Nuvvu Nannu premisthunnava? - kina sona/kana so na?
196. Avunu nenu ninnu premisthunnanu - Eh ina sonki/sonka
197. Idhi naa kalamu - wannan alƙalamina ne
198. Ela? - Ta yaya?
199. Eppudu? - Yaushe?
200. Idhi me kosam - wanna naka ne/ naki ne.

Alhamdulillahi. Iya abinda na samu ikon gabatarwa kenan a wannan ɓangare na darussan Telugu. Allah ya tabbatar mana alherin da ke tattare da shi ya kuma kare mu daga sharrin da ke cikin sa. Nagode

©️✍🏻
 Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com