~Film ɗin ChaalBaaz kenan wanda aka fitar a shekarar 1989 inda ya cika shekaru 34, wannan Film dai shine guda ɗaya Tilo wanda aka ga jarumi Sunny Deol da Rajnikanth sunyi aiki tare, Haka Jarimar ciki ma wato Sridevi anyi nominating ɗin ta a matsayin Jarimar jarumai mata ta wancen shekarar bisa gudunmawar da ta bada a cikin wannan Film inda ta rabauta da kyautar a bikin bada kyaututtukan Filmfare Award da akayi a shekarar 1990,
~An gina labarin wannan Film akan wasu yan'uwa mata guda biyu Anju da Manju waɗanda suka rabu tun daga haihuwar su inda kowacce tayi rayuwar ta a wani waje na daban, inda aka ɗauko wasu abubuwa daga labarin Film ɗin nan na Hema Malini, Dharmendra da Sanjeev Kumar wato SEETA AUR GEETA, Ragowar fitattun jariman da suka taka rawa a wanann Film na Chaalbaaz sun haɗa da: Annu Kapoor, Anupam Kher, Shakti Kapoor, Aruna Irani, Kader Khan, Saeed Jaffrey, Johnny Lever dadai sauran su,
~Anand Bakshi shine ya rubuta waƙoƙin cikin sa, yayin da Kavita Krishnamurthy, Muhd Aziz, Amit Kumar, Sudesh Bhosale har ma da Johnny Lever suka rera su, inda waƙar "Na Jaane Kahan Se Aayi Hai" ta zama mafi karɓuwa a wancen lokacin,
~Fitattun Team ɗin nan na makaɗa waɗan da babu waɗan da suka kaisu yawan kida a tarihin Hindi Cinema wato Laxmikant–Pyarelal sune sukayi music ɗin wannan Film, wanda wanda shi Pyarelal (Ramprasad Sharma) a wannan mako ne ma ya cika shekaru 83 duk da yake abokin aikin masa ya jima da wucewa, sunyi music a fina-finai kusan guda 800 tun farawar su.@AyƘoƘi.