12-07-2002 - CELEBRATING 21 YEARS OF DEVDAS

12-07-2002 - CELEBRATING 21 YEARS OF DEVDAS



A rana irin ta yau ne aka fitar da babban Film É—in nan mai É—auke da labari mai taÉ“a zuciya inda aka nuna wani lokacin iyaye kan shiga tsakanin masoya su farraÆ™a su ta Æ™arfi, wanda a irin hakan ne kuma garin neman gira akan rasa idanun ma gaba É—aya. 


Fasihin Director É—in nan Sanjay Leela Bhansali shi ne ya bada umarnin wannan Film inda Bharat Shah ya zama Producer, duk dai Æ™arÆ™ashin kampanin Eros International Media Ltd sai jaruman ciki da suka haÉ—a da: jarumi Shah Rukh Khan, Aishwarya Rai da kuma Madhuri Dixit a Leading Role, sai kuma irin su: Jarumi Jackie Shroff, Kirron Kher, Smita Jaykar da sauransu wadanda suka taka rawar gani. 


Devdas Film ne wanda ya samu matuÆ™ar Nasara, inda aka yi masa babban Budget har na fiye da Crore 50, duk da hakan ya janyo cece-kuce har daga É“angaren Hukumomin Æ™asar ta India domin ana ganin kuÉ—in da aka kashewa wannan Film sun yi yawa matuÆ™a, har ake masa laÆ™abi da Most Expensive Indian Film Ever Made Amma fa a wancen lokacin kenan, duba da yanayin da Æ™asar Indian ke ciki a daidai lokacin da Film É—in ya fita, Amma dai duk da haka kwalliya ta biya kudin sabulu. 


Wasu daga cikin nasarorin da wannan Film ya samu sun haÉ—a da: National Film Award for Best Popular Film Providing Wholesome Entertainment, Filmfare Award d.s, Haka mafi yawan jaruman ciki sune suka rabauta da zama jariman jarumai a bikin bada kyaututtuka na shekarar 2002, kamar Best Director, Best Actor, Best Actress, Best Supporting Actress da dai sauransu,


A ɓangaren waƙoƙi ma dai wannan Film ba'a barshi a baya ba, domin kuwa fitattun mawaƙan da ake ji da su sune suka baje basirar su irin su: Udit Narayan, Vinod Rathod, Shreya Ghoshal, KK, Kavita Krishnamurthy har ma da ita kanta Madhuri Dixit akwai Muryar ta a cikin daya daga waƙoƙin wato waƙa mai suna Kaahe Chhed Mohe


MakaÉ—a irin su: Ismail Darbar, Birju Maharaj da kuma Monty Sharma wanda dan'uwa ne wajen shahararren makaÉ—in nan da baya wato Pyarelal wanda ya shahara da yin aiki tare da Laxmikhan, sune suka bada music É—in wskonl WaÆ™oÆ™in wannan Film ciki har da waÉ—an da suka fi shahara wato waÆ™ar Dola Re Dola, Maar Daala da kuma Silsila Ye Chahat Ka inda ita ma mawaÆ™iya Shreya Ghoshal ta samu nasarar tafiya da Best Female Playback Singer da waÆ™ar ta mai suna Bairi Piya. 


Tun a shekarar 1955 wani Producer Director mai suna Bimal Roy ya yi Film mai wannan suna wato Devdas inda yake É—auke da jarumi Dilip Kumar, Suchitra Sen da Vyjayanthimala, duk da yake akwai wasu fina-finan ma kafin shi din da suka zo da irin wannan suna na DEVDAS.

@AyƘoƘi

Comments