WANENE ROHIT SHETTY?
Rohit Shetty yana cikin Directors da babu kamarsa a tarihin Bollywood
Rohit Shetty director ne mai tarin nasara inda ya kasance yana cikin Directors din da suke da babbar nasara.
Rohit Shetty ya fara directing dinsa na farko a shekara ta 2003 inda ya fara da rashin nasara.
Zameen na Jarumi Ajay Devgn shine film na farko da Rohit Shetty ya fara directing inda film din ya karkare da Below Average.
Sai a shekara ta 2006 Rohit Shetty ya Kara directing din film dinsa na biyu me suna Golmaal Wanda ya kasance nasararsa dinsa na farko. Golmaal ya zama Hit a Box Office.
A shekara ta 2008 Rohit Shetty yayi film dinsa na uku me suna Sunday Wanda ya kasance Flop a Box Office. Hakan ne nuni da finafinansa guda uku na farko biyu sun fadi yayinda daya yayi nasara .
A shekara ta 2008 Rohit Shetty ya Kara dawowa da Golmaal Returns inda ya zama Hit.
A shekara ta 2009 Rohit Shetty yayi Directing din film dinsa na biyar me suna All The Best wanda shima ya samu nasarar zama Average a Box Office.
A shekara ta 2010 Rohit Shetty yazo da Golmaal 3 wanda ya kasance shine Blockbuster dinsa ta farko.
A shekara ta 2011 Rohit Shetty yayi Directing din Singham wanda ya kasance Super Hit a Box Office.
A shekara ta 2012 Rohit Shetty yayi Directing din film dinsa na 8 me suna Bol Bachchan Wanda ya samu nasarar zama Hit a Box Office.
Wani abunda zai baku mamaki duka wannan finafinai guda 8 da Rohit Shetty yayi Directing dinsu duk na Jarumi dayane wato Ajay Devgn inda duka ya fito acikin wannan finafinai guda 8.
A shekara ta 2013 Rohit Shetty yayi film dinsa na farko ba tare da Ajay Devgn ba wato Channai Express na Jarumi Shah Rukh Khan.
Channai Express ya zama Blockbuster a Box Office sannan ya bawa Rohit Shetty damar 200cr a karo na farko sannan ya zama film dinsa na farko daya saida tickets na sama 2cr.
Singham Return shine film na 10 da Rohit Shetty yayi Directing Kuma shima nasara ce a Box Office inda ya zama Super Hit a shekara ta 2014.
Shekara ta 2015 Rohit Shetty ya kara gwada Jarumi Shah Rukh Khan bayan yayi Singham Return da Ajay Devgn, Rohit Shetty yayi Dilwale wanda ya samu nasarar zama Semi Hit a Box Office.
Golmaal Again a shekara ta 2017 shine film din Rohit Shetty na 12 Kuma shine Blockbuster dinsa ta uku.
A shekara ta 2018 ya Kara samun wata Blockbuster din da Simmba.
A shekara ta 2021 Right Shetty yayi Directing din Sooryavanshi inda ya zama Hit a Box Office.
Tun bayan rashin nasarar Sunday a shekara ta 2008 Rohit Shetty Saida ya shafe shekaru 14 ba tare da film dinsa ya Fadi a Box Office ba. Rohit Shetty ya jera finafinai guda 11 babu failure.
Rohit Shetty yana da finafinai guda 9 da suka saida tickets na sama da 1cr yayinda yake da guda 1 Wanda ya siyar da tickets na sama 2cr.
Rohit Shetty yana da finafinai guda 8 da suka haura 100cr yayinda aciki akwai guda uku da suka haura 200cr.
Channai Express shine film din Rohit Shetty nafi tara yan kallo a Cinema inda ya siyar da tickets na 2.52cr
Simmba shine film din Rohit Shetty da yafi kawo kudi inda ya kawo 239cr a India.
A yau ne aka saki film din Rohit Shetty na 15 wato Cirkus na Jarumi Ranveer Singh. Bisa dukkan alamu wannan film me suna Cirkus zai zama failure dinsa ta farko cikin shekaru 14😭
A yau Cirkus ya kawo 7cr wanda hakan ke nuni da wannan film ba zai ka labari domin bai samu yabo mekyau ba 😭
Rohit Shetty yayi Directing din finafinai guda 15
Ajay Devgn ya fito a guda 10
Shah Rukh Khan a guda 2
Ranveer Singh a guda 2
Akshay Kumar a guda 1
Izuwa yanzu dai finafinai guda 2 ne kawai suka Fadi acikin guda 14 da suka gama kasuwa inda 12 suka samu karbuwa
Acikin guda 12 da suka karbu sun hada da 10 Clean Hits sai 4 Blockbusters
Wannan shine dan bayani akan Rohit Shetty
Daga Abdull Asa