KO ME YAYI ZAFI HAKA 😨🤔 Tunisha Sharma Commiting Suicide
A jiya asabar ne Jaruma "Tunisha Sharma" wacce aka fi sani da fitowa a fina-finan gidan TV masu dogon zango ta rataye kanta a banÉ—aki a yayin da suke tsaka da É—aukar wani Film mai suna Ali Baba: Dastaan-E-Kabul,
Jarumar dai tana kan ganiyar ta domin kuwa shekarunta 20 cif, a halin yanzu,
An haife ta a a shekarar 2002, ta fito a fina-finai irin su; Fitoor, Baar Baar Dekho, Dabangg 3, Kahaani 2, da dai sauransu, inda ta fara sun tana da shekaru 14,
Ana cikin ɗaukar Film ne dai jarumar tace zata shiga banɗaki, ko da aka jita shiru sai aka bita ciki aka tarar tuni ta rataye kanta, nan take aka wuce da ita asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar tata aka miƙa ta zuwa ga alhalin ta.
@AyƘoƘi