LOKACI ALƘALI
Ƙaurace wa finafinai musamman idan fim ne na daga cikin finafinan 3 Khans ba sabon abu bane a India.
Misali a lokacin sakin fim ɗin Shah Rukh khan mai suna “My Name Is Khan” a shekarar 2010, wani daga cikin ‘yan adawan (Shah Rukh Khan) sa mai suna Debsena shine gaba-gaba wurin haɗa gangamin ƙauracewa wannan fim ɗin. Sun yi du wasu ababe na tsana a kan wannan fim ɗin kaama daga yage fastoci (posters), sambaɗawa wasu daga cikin gidajen kallon da za’a haska fim ɗin wuta da dai shauran aikata du wasu ababe na ƙiyayya amma daga karshe hakarsu bai cimma ruwa ba domin fim ɗin ya samu gagaruman nasara! A karshe ma masoyan Shah Rukh Khan ɗin godiya irin na shaguɓe suka kama yi musu akan sun gode da hauragiyar da suka kama yi wanda hakan yayi sanadiyyar ɗaukakar fim ɗin.
Eh sosai, babu wani riba da suka samu akan hauragiyar da suka yi kuma ba zasu taɓa samu ba. Tun lokacin da aka saki ƙaramar tallar (teaser) na fim ɗin Pathan maƙiya da mahassada suka shiga aikinsu na kira da kala-kalan murya akan a fito a ƙaurace wa fim ɗin. Toh saboda me?? Saboda ƙiyayya! Toh ƙiyayya a kan me? A kan SRK! Laifin me yayi musu? Tohm wata ƙil koh dan musulmi ne? kuma hakane fa, domin idan zamu lura ba iya SRK kawai akayi wa hakan ba koh Aamir Khan ma fim ɗinsa na baya-bayan nan mai suuna “Laal Singh Chaddah” ya sha kashi a wurin ‘yan-ta-ƙaura (Boycutters) du dai saboda shima Khan ne koh??? Toh kusan hakane domin tun a fim ɗin (Aamir Khan) sa “PK” ma’abota bautar gumaka sunce ya ci wa ababen bautarsu da addinansu fuska don haka tun a wannan lokacin ne suka kurɓi ruwan alwashin cewa du wani fim nasa zasu kaurace masa. Domin Allah ya ƙara tabbatar wa da masu Imani cewa addinin bautar wanin Allah ba gaskiya bace kuma babu wani abun bauta da gaskiya sai shi Allah yasa fim ɗin na PK yayi gagaruman Nasara.
Tohm koma dai meye, fim ɗin Shah Rukh Khan ‘Pathan’ a ranar laraba 25th January 2023 zai fita shin koh ya zata kaya idan aka saki fim ɗin????
Shin Haƙar 'yan-ta-ƙaura zai cimma ruwa na ganin fim ɗin ya faɗi???
A’a koh ‘yan-ta-ƙaura zasu mayar da wuƙaƙensu a kube ne su zuba wa sarautar Allah ido koh kuwa za suyi irin yadda suka yi ne lokacin da aka saki fim ɗin MNIK???
LOKACI ALKALI
🖋 UMAR FAROOQ SULAIMAN