Aqidar Samsara -Lahirar Mabiya Hindu-.
Mafi girman abinda mabiya Addinin Hindu suke kudurcewa na Aqida ya ta'allaqa ne akan ciratuwar ruhin Bil-adama bayan Mutuwarsa zuwa wata Halitta ta daban
"Tanasukhul Arwah" (reincarnation), sai dai su (mabiya Hindu) suna kiranta da "Saṃsāra", ita dai wannan Aqida kamar yadda muka ambata ta ginune akan riya ciratuwar ruhi daga gangar jikin Mamaci zuwa wani abu na daban, kamar Dabbobi, Mutane ko Alloli!
Aqidar Samsara ta ginune akan wata Aqidar ta su ta biyu, wacce suke kira "Karma", abinda suke nufi shine, aikin da Mutum yake yi a wannan rayuwar ta duniya, to shine zai zama sababin dawowarsa acikin Aqidar "Samsara", ta yadda ko dai ya dawo acikin gangar jikin dabbobi ko duwatsu ko kuma ma ya zama tauraro ko ya dawo acikin siffar Allolinsu!
Suna cewa wannan hukunci haka yake baya canzawa akan Sarki, ko mai Mulki zuwa Talaka, mai Kudi, ko Faqiri, duk abinda mutum ya shuka shi zai girba a dawowa ta gaba.
Tare da cewa ita wannan Aqida bata da wata madogara a zahiri, ba kuma ilimine da aka gwada aka ga karbuwarsa, amma tare da haka ya samu karbuwa wajen wasu daga cikin Musulmai, kamar Gulat na Sufaye da 'yan Shi'a Batiniyya, a cikin wani salo a daban ko Makamancin na mabiya Addinin Hindu, wani abin mamaki hatta wani sashe na Turawa a yau suma zaka ji suna cewa "I believed in Karma"! Wasu yan Boko kuma ko wadanda suka tasirantu da fina-finan India da na Turai suma zaka ji suna cewa sun bada gaskiya da "Karma", alhali su wadannan tagwayen Aqidun sune a makwafin Imani da ranar Lahira wanda yake rukunine daga cikin rukunan Imani a wurin Musulmi! '
Kasancewar cikakken adalci baya samuwa a wannan rayuwar ta duniya, don haka sai bokayen Addinin Hindu suka ga babu makawa su samar da yanayin da zai tabbatar da Adalci a dawowa ta biyu bayan mutuwa a wannan duniya.
Bokayen suna karfafar wannan Aqidar da cewa kyawun Halitta, kaifin kwakwalwa da hazaqa da wasu Mutane suke dauke da shi yana da alaqa da sakamakon ruhin wasu da suka taba rayuwa a matsayin Mutanen kwarai a wannan duniyar, don haka suke kwadaitarwa akan yawaita aiyukan kirki da nisantar mugunta, domin idan Mutum ya tashi dawowa ya dawo a siffa ta kwarai ba a siffar dabbobi masu farauta ba kamar Kare, kyarkeci, Kura da makamantansu, akan kuma haka ne suke haramtawa junansu yanka dabba kowace iri ce ko cin namanta, saboda a riyawarsu wai zai iya yiwuwa wannan wani Mutum ne da ya taba rayuwa a duniya aka dawo da shi a siffar dabba.
Abubakar Umar
18/11/2022