A cikin wannan shekara ta 2022 ne dai wasu fitattun Jaruman Bollywood mata suka samu Nassarar zama iyaye, Jaruman dai sun haɗa da Priyanka Chopra, Sonam Kapoor, Alia Bhatt, Bipasha Basu, Nayanthara, Kajal Aggarwal da sauran su.
Ranar 20-08-2022 jaruma "Sonam Kapoor" da mijin ta "Anand Ahuja" suka bada sanarwar samun yaron su da suka sanya masa suna ‘Vayu Kapoor Ahuja’ *Sonam* da maigidan nata sun wallafa sakon murnar su a shafin su na Instagram a lokacin da suka samu wannan ƙaruwa, Ga abin da suka ce _"We welcomed our beautiful baby boy with bowed heads and open hearts. Thank you to all of the doctors, nurses, friends and family who have supported us on this journey. It’s only the beginning, but we know our lives are forever changed.
A watan October 2022 jarumar nan ta cikin Film ɗin *Jawan* na jarumi _Shah Rukh Khan_ wato "Nayanthara" da mijin ta "Vignesh Shivan" suka bada sanarwar samun tasu ƙaruwar na ƴaƴa biyu ras duka maza, amma fa ta hanyar hayar mahaifa,
An dai sanyawa yaran suna "Uyir" da "Ulagam" waɗanda a lokacin da aka haife su ma jarumar tana wajen ɗaukar wani Film.
A Ranar 08-07-2022 jaruma "Priyanka Chopra" da mijinta "Nick Jonas" suka sanar da samun ƴar su mai suna "Malti Marie Chopra Jonas" wacce aka same ta ta hanyar hayar mahaifa wato _surrogacy_
A yayin sanar da haihuwar wannan yarinya, jaruma Priyanka ta wallafa sakon ta a Instagram kamar haka _“We are overjoyed to confirm that we have welcomed a baby via surrogate. We respectfully ask for privacy during this special time as we focus on our family. Thank You so much.”_
A yanzu haka dai wannan ƴa tasu tana da kusan watanni 5 a Duniya.
A ranar 19-04-2022 ita ma Jaruma "Kajal Aggarwal" da maigidan ta "Gautam Kitchu" suka bada sanarwar haihuwar ɗan su da suna sanya masa suna Neil
Haka ma dai a Ranar 12.11.22, ita ma Jaruma "Bipasha Basu" da mijin ta "Karan Singh Grover" suka samu ƙaruwar yarinyar su mai suna “Devi Basu Singh Grover wacce a wannan rana ne ma take cika wata ɗaya cif a Duniya,
Suma dai ma'auratan sun wallafa nasu saƙon murnar haifuwar yar tasu kamar haka; _The physical manifestation of our love and blessings of Ma is here now and she is Divine.
A ƙarshe a ranar 6th November, 2022 ita ma Jaruma "Alia Bhatt" da maigidan ta jarumi "Ranbir Kapoor" suka zama iyaye da "Raha Kapoor" inda suka sha CECE-KUCE a wajen al'umma, tun daga samun juna biyun nasu har zuwa haihuwar da suka samu,
Jaruman sun rubuta a shafin su cewa _“The best news of our lives: – Our baby is here … and what a magical girl she is (heart emoji) We are officially bursting with love – blessed and obsessed PARENTS!!!!!! Love love love Alia and Ranbir.
@AYƘOƘI