A yau ne dai wannan ƙasaitaccen shirin da duniya ke jiran fitarsa wato Fatattaka ya antayo sinimu inda tuni makallata suka fara kodumo da shi ta hanyar kashe ƙwarƙwatar idanuwansu. Wannan shiri dai ya tabbata abin tsumaye ga makallata, domin kuwa irin cincirindon da makallatan suka yi a bakin sinimu kaɗai ya isa ya tabbatar maka da hakan. A ɗaya gefen kuma, masu sharhi ne ke ta yabon shirin tare da liƙa mishi taurarin girma da yabo ta kowane fanni. To sai dai kuma fa ba a nan gizo ke saƙar ba, domin kuwa har yanzu dai kallon shi ake yi ba a kai ga fitar da adadin damman da ya ƙwamuso ba a ranar sa ta farko. Sai dai wasu na ganin cewa shirin zai iya rakito karo 50 a ranar sa ta farko. Yanzu dai haka ana ta tuturniyar taro damman da wannan shiri ke ci gaba da ƙwamusowa ne a yanzu haka. Abin da kawai ya tabbata shi ne, shirin ya samu karɓuwa a zukatan makallata. Musamman fitowa ta musamman da Tumbiɗo ya yi wacce ta ƙaddamar da shirin Kamfanin Yaji Da Yarfe na haɗa duniyar 'yan leƙen asiri. Shin a tunaninku nawa shirin zai iya ƙwamusowa?
#haimanraees