Daga mahangar #NayaakBHAI
Sharhin Shirin DRISHYAM2 na #Ajay_Devgan. A kalma daya rak na kira shi #Extraordinary
Na tabbatar 100% babu wanda zai kalla wanan kafce a natse ba tareda ya kayatu gami da kasancewa cikin dogon alajabin hikima gami da matuqar kaifin basira irinta Vijay wato Ajay devgan a cikin kafcan..na jima ban kalla shirin daya tashi kaina irin Dtishyam2 ba.dukda kaifin basirarsa is OUT OF THIS WORLD ammah fa shirin a kaikaice yana nunar damu cewar hikimar kaifin basirar lisaafi gami da fikiri ba karatu mai zurfi kadai ke samar da ita ba kadai ba,abin baiwa CE.Wanda babu Wanda zai yi tunanin Vijay Wanda bashida wani ilimi mai zurfi zai kasance mai matuqar kaifin basirar da ga kisa ya auku da shaidu karara Amman yaki ya bada damarda za a iya nunasu a zahiri ainun domin yi masa hukunci dasu.ana ji ana gani.
Jeetu Joseph ainahin marubuci wanan kafce daga industry din Malayalam ya cancanci yabo ainun.wato a film fadace fadace Action kokuwa soyayya tsinkar fure.basune film ba mallam in kanason salon kafce mafi dadi ka kalli Thriller wato irin rikunin salon da Drishyam yazo dashi..
Ajay Devgan yayi aiki mai matuqar kyau Wanda ya jagoranci kafcen labarin ya rataya a wuyansa,Drishyam2 dukda Remake ne yana daya daga ayyukansa da za acigaba da tunawa dashi a zukatan makallata,supporting Cast wato sauran abokan aikinsa na shirin daga Shriya saran matarsa a shirin,Ishita Dutta yarinyar da ta dalilinta kurar ya samu tushe Wanda duk wanan kaida fatar daya dage akai yar rikoce bashi ya haifeta ba,da ace haka mutane ke jajircewa kan yaran da suke ruko da wani sai yabar iyayanda suka haifeshi ya ya tafi wani wurin Dan a rike shi.Tabu,Akshey Khanna,Rajat Kapoor da Shaurabh Shukla kowa yayi aiki mai kyau a bangaransa..baza ayi tuya a mance da Albasa ba wato Dreban Jirgin Abshekh Pathak daya bada umarnin shirin gami da tsara Labarin na ainihi izuwa Hindi Remake yayi aike mai kyau ainun
BATU NA KARSHE
Drishyam2 shiri ne da duk yanda ka kaiga kushe dola zaha kayatu ainun kuma zai tashi kanka.saidai duk Wanda yasan bai kalli na farko ba kwatakwata.karya soma kallon wanan ba tareda ya kalla wancan ba....ga duk yanda na kaiga zurfin tunanin bin kwakkwafin gano inda shirin yasamu akasi na Gaza gani...Wanda ina ganin rashin gano kuskuren nada nasaba da tashin kaina da shirin yayi ne OVER domin ya barini da baki wangale saboda alajabin kaifin basirar VIJAY..NayaakBHAI na bawa shirin Taurari 5 bisa 5 ...Wanda bai kalla ba Mai Kake JIRA?