Jarumi Ranveer Singh kenan a safiyar yau tare da mai dakin sa jaruma mai zamani "Deepika Padukone" inda suka sauka a airport cikin shigar baƙaƙen kaya, nan take ya sauko ya buɗe mata ƙofar mota ta sakko, ya riƙe hannun abarsa suka shige ciki, wanda hakan ya birge masoyansu sosai,
A karshen shekarar da ta gabata ne dai jaruma Deepika Padukone ta taka wata rawa a cikin waƙar Besharam Rang ta cikin pathaan wacce ta bar baya da ƙura ana ta CECE-KUCE, shi kuwa maigidan nata yaba mata yayi da irin wannan rawa da ta taka, inda ya ƙara da cewa tabbas tayi matuƙar ƙoƙari a waƙar kuma yana alfahari da ita, Hausawa dai sunce wai sai hali yazo ɗaya ake abota, kuma abokin damo guza, Allah ya bar ƙauna.
@AyƘoƘi