Babban Jarumi Aamir Khan Yana Bawa Film Lokaci Maqura Wajen Tsara Shi Da Zuwan Ƴan Kallo Ta Inda Sukeso Hakan Ne Yasa Yake Yawan Karya Rekod Amma Duk da Haka Yayi Rashin Nasara Gagaruma Bayan Ya Saki LAL SINGH CHADDHA Karkashin Kamfanin sa Aamir Khan Productions Bayan Ƴan Kallon India Sunƙi Su Kalla a Sinimu, Kwanaki Yace Zai Zauna Da Iyali Ya Huta.
Amma Kuma Wasu Labarai da Suke Zuwa Shine Manyan Masu Shirya Fina-finai na Kudancin India Suna so Suyi Masa Film.
Na Farko Wanda Yayi Film ɗin KGF na 1 da na 2, Watau Prashanth Neel, Yace Yanaso Ya Haɗa Aamir Khan da NTR a Wani Gagarumin Shiri Wanda Akayi Masa Kasafi Me Girma Kuma Tuni Sun Sanar da Wannan Film Amma Dai Shi Aamir Khan Be Tabbatar Zaiyi ba Zuwa Yanzu.
Sannan na Biyu Shine Sanannen Mashiryin Film Wanda Yayi Ghajini watau Madhu Mantena Yace Yana da Burin Yin Ghajini na 2 Kuma Aamir Khan Yakeso Ya Fito.
Akwai Wani Fitaccen Mashiryin Film da ba a Bayyana Sunan sa Amma Shima Yana Nan Yana Ƙoƙarin Yiwa Aamir Khan Film Indai Kuwa Hakan Ya Tabbata Koda Guda Ɗaya ne Ko Biyu To Babu Batun Hutu ga Wannan Jarumi.
#AbbaIndiaDala