SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 06
RUBUTAWA:
Anupama Chopra
FASSARAWA:
Haiman Raees
Yadda 'yan kallo ke tafiya da motsin majigin abin burgewa ne. Wani lokacin ka ji surutu yayi yawa, ko ma ka ga an tada hayaniya. 'Yan kallon kan yi tafi da ƙarfi a lokacin da jarumin ya yi fitowar farko a shirin ko kuma a lokacin da aka furta wani kalami da ya burge. Sukan bi waƙar cikin shirin yayin da aka zo kanta wani lokaci ma har da jefa kwabbai a jikin majigin tare da tiƙar rawa abinsu. Fim ɗin da ya yi nasara a Indiya shi ne fim ɗin da ya samu maimaicin 'yan kallo. Ma'ana mutanen da suka kalli fim ɗin sau da dama. Wasu fina-finan da suka zama blockbusters an ci gaba da kallon su har na tsawon shekaru biyar wasu ma har goma.
'Yan kallo ba wai zunzurutun abin da yake a zahiri bane suke son kallo, so suke su ga drama wacce ta wuce tunani.
Ƙwararrun masu ƙawata aiyukan ƙasar Indiya sun bada goyon bayan cakuɗa yanayi iri-iri a cikin drama. Fina-finan Hindi, ba tare da jin nauyin komai ba su kan cakuɗa zubin labari, wajen ɗaukan shirin, salo da dai sauran su. A Bollywood komai ma na iya faruwa. Hakan yasa tashin hankalin lokacin da aka yi kisan kai na iya juyewa ta hanya mai ban mamaki inda za a ga jarumin ko jarumar na mafarkin yin caca akan tsibiri.
Wata waƙar raha kuma ta daban kan iya ratsowa ta tsakar shirin baga-ta-tan. Jarumin ka iya yi wa mutane goma dukan tsiya ba tare da wata wahala ko jin rauni ba. Ita kuma jarumar za ta sa mstsatstsen buje guntu tana rawa mai tada hankali amma kuma za ta kasance da mutuncinta tsaf har a gama fim ɗin. Mutane da gidajen cikin fim ɗin dole su zamo masu tarbiyya. Hatta waɗanda ake nuno su a matsayin talakawa ma za ka iske suna da irin nasu kyallin. Dokoki biyu ne kawai: Dole ya zama akwai soyayya kuma dole ya zama akwai waƙoƙi. Waƙoƙi su ne zuciyar fitattun fina-finan Hindi. Kiɗa da waƙa sun riga sun zama wata hanya ta bayyana ƙasar Indiya. Manyan labaran almara na ƙasar Indiya wato Mahabharata da Ramayana, duk an rubuta su ne da zubi irin na waƙa. Akwai wani wasan kwaikwayo na Sanskrit mai suna Mirch Kattika wanda ya kai shekara 3,000 da rubutawa, shi ma a cikinsa akwai waƙoƙi.
A shekarun 1930s da 1940s, ba abun mamaki bane don ka ga fim da waƙoƙi 40. Wani fim mai suna Indrasabha da aka shirya a 1932, ya ƙunshi waƙoƙi guda 70. Amma da aka shigo 1950s sai waƙoƙin suka ragu. Da yawan fina-finan Bollywood za ka iske su da waƙoƙi mafi yawa guda shida ne. Waɗannan waƙoƙi su ke bayyana yadda rayuwa take a yankin Asiya ta kudu wa duniya.
Waɗannan waƙoƙi su ake sakawa a tarukan biki, shagali, taron addini da sauransu. Hanya mafi sauƙi ta tafiyar da lokaci shi ne yin wasan Antakshari, shi kuma wani wasa ne da ya ƙunshi rera waƙoƙin fina-finai. Har aka shigo cikin shekarun 1970s, babu wani kalan waƙa da ya samu wurin zama face waƙoƙin fina-finai. Labaran Bollywood suna da girma amma ba su da wuyar fahimta. Fina-finan Hindi yawanci suna magana ne akan tarbiyya, ta yadda za ka ga jaruman suna fitowa a irin waɗannan matsayin. Fina-finan Indiya na farko-farko duk tamkar labaran kunne ya girmi kaka ne da ke koyar da tarbiyya. Mai shirya fina-finai na farko a ƙasar Indiya wato Dhundiraj Govind Phalke wanda ya shirya Raja Harishchandra a 1913, shi kansa ya fito ne daga ahalin malaman addini.
Jaruman fina-finan Hindi yawanci su kan fito ne a siffa irin ta abin bauta Ram, wanda a cikin Ramayana ake wa laƙabi da maryada purush-ottam, yawanci za ka same shi kyakkywa ne, mai hasken fata kuma ba shi da lahani a jikinsa. A yayin da jarumin zai kasance mai kima, shi kuma azzalumin zai kasance mara tarbiyya, kuma a koda yaushe, alheri dai shi ke sama da sharri. Labarin zai ƙunshi waƙa mai daɗi a cikin ruwan sama, ko kuma zunzurutun mugunta, haka dai. Nishaɗantarwa ne kawai dai wacce a ciki ake nuna tarbiyyar ahali kuma mutuncin jarumar bai zubewa. Fina-finan Hindi ba wai suna nuna rayuwa a yadda take bane, a'a suna nuna rayuwa ne a yadda ya kamata ace ta kasance. Wataƙila hakan ne ma ya sa fina-finan suka karɓu sosai a duniya.
©️✍🏻
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com