SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 07
RUBUTAWA:
Anupama Chopra
FASSARAWA:
Haiman Raees
Waɗanda ma ba indiyawa ba na iya haɗuwa da irin waɗannan waƙoƙi da ƙawa a ƙasashe maban-banta irin su Peru, Indonesia, Greece, da Ethiopia, cike da nishaɗi da kuma zumuɗi.
A ƙalla masana'antar fina-finan Hindi tana da makallata guda biliyan 3.6 a duniya baki ɗaya. Hakan ya sa masana'antar ta zama wata hanyar samun jin daɗi na tilas ta kuma zama wata haɗaka ta buri da fatan alheri. Sai dai kuma Bollywood ba wai salo ne kawai na shirya fina-finai ba, fina-finan Hindi su ke zaɓar kayan sawa, harshe, al'adu da kuma manufa wa injiniyan na'ura da kuma ɗan ƙauyen da ke jaha mafi ci baya a Indiya, wato Bihar. Fasahar ƙere-ƙere ta taimaka wajen yaɗa aiyukan Bollywood. DVD, satellite, da kuma Internet sun samar musu da masoya har a ƙasashen ma da ba a sakin fina-finan Hindi a cikinsu.
A South Korea, akwai wata al'ada da ke gudana a kowane sati. Wasu tawagar mutane da ke kiran kansu da sunan Bollywood Lovers Club kan taru su kalli fina-finan Hindi wanda su suka zauna da kansu suka fassara a wahalce zuwa harshen Korean. Sukan kalla, kamar yadda shugabansu Kwanghyun Jung ya ce, “da salo irin na Indiya.” hakan na nufin, sukan “yi hayaniya, dariya tare da zagin mugu ko boss ɗin fim ɗin.” Haka kuma suna da azuzuwan koyar da rawar fina-finan Bollywood. Membobinsu, waɗanda sun kai dubu 7,000 da yawansu kan sa riguna masu ɗauke da hotunan Shah Rukh Khan da kofuna masu ɗauke da hotunansa. Fim ɗaya ne kaɗai aka taɓa saki a South Korea— wani fim ɗin Tamil mai suna Muthu: The Dancing Maharaja, a 1998.
A wata takarda mai suna Indian Films and Nigerian Lovers: Media and the Creation of Parallel Modernities, wani masanin kimiyyar ɗan Adam mai suna Brian Larkin ya rubuta cewa irin rinjayen da Bollywood ke da shi a arewacin Nijeriya, in da wani ɗan ƙasar Lebanon ya fara shigo da fina-finan Indiya a 1950s. Larkin ya ce: “Har zuwa yau, hotunan fina-finai da jaruman Indiya su ne ababen kwalliyar motocin tasi da bas a arewa, fastocin fina-finan Indiya su ne suka cika bangwayen shaganun teloli da garejin kanikawa yayin da waƙoƙin soyayya daga fina-finan Indiya kuma ake aro su a maida su ƙasidu ana yabon Annabi Muhammadu da su. A tsawon sama da shekaru talatin, fina-finan Indiya, jarumansu, waƙoƙinsu da labaransu sun riga sun zama wani babban ɓangare na al'adun yau da kullum a arewacin Nijeriya.”
Su kuwa 'yan ƙasar Germany, su ne basu daɗe da shigowa ba. Fim ɗin Bollywood na farko da ya fara samun babbar fitarwa a ƙasar shi ne Kabhi Khushi Kabhie Gham a 2003. A Germany, DVD ɗin fina-finan Hindi da aka fassara ana siyar da shi ne tare da rubutu mai ɗauke da saƙon: Bollywood macht glücklich! (ma'ana Bollywood za ta saka farinciki). A Pakistan kuwa, Bollywood ta samu ƙwarin gwiwar da ba a yi tsammani ba. A 1965, bayan yaƙi na biyu a tsakanin Indo-Pak, gwamnatin Pakistan sai ta hana shigowa da kuma haska fina-finan Indiya. To amma ita Bollywood tana ko'ina ne. Don haka, DVDs na satar fasahar sabbin fina-finan Indiya ma ana iya samun su a ranar da aka saki shirin. 'yan jarida kuma, a harshen Turanci ko harshen gida su kuma suna nan suna sharhi akan waɗannan fina-finan. Duk da cewa Radio Pakistan ba ta sa waƙoƙin fina-finan Hindi, masoya na nan sane da wace waƙa ce ke kan gaba, raye-raye, ado da gulmace-gulmacen Bollywood.
Akan layukan Karachi da Lahore kuwa, hotunan Shah Rukh ga su nan manya suna kallonka yayin da yake tallata kayan ƙasashen waje. Asalin gidan kakanninsa da ke Peshawar kuwa ya zamo wajen yawon buɗe ido ma. Mahesh Bhatt ya taɓa cewa ɗaya daga cikin dalilan da suka sa Pakistan ba za ta yi yaƙi da Indiya ba shi ne saboda Shah Rukh yana rayuwa ne a Indiya.
©️✍🏻
Haiman Raees
Infohaiman999@gmail.com