A shekarar 2000 kareena Kapoor aka shirya mata debut mai suna Kaho na pyaar hai wadda za su fi to tare da Hiritick Roshan (Krish)
Sai dai ana tsaka da fara daukar film din bayan photo shoot (a wani majiyar har an fara daukar tittle song da kareena a bakin kogi) sai dai kwatsam kareena ta fice daga film din.
Babu yarda mahaifin hiritick roshan wadda shi ne mai mallakin film din ya iya ban da nemo wata jarumar cikin sa'a ya samu 'yar abokinsa Ameesha Patel ta yi signing kwana 4 kafin fara dauka.
Film din na fita ya zama successful inda dare daya Ameesha ta zama celebrity .
A gefe guda itama kareena ta fito a film nata na farko a shekaran tare da Abisheik bachchan a film mai suna refugee sai dai film din ya yi faduwar tasa a box office.
Bayan kallon kahona pyar hai da aka tambayi kareena me zata iya cewa akan Ameesha Patel a film din sai kareena ta ce "Sam Ameesha bata yi kokari ba, film din na Hiritick ne ba nata ba, fuskar Ameesha dauke yake da kuraje da bakaken tabo wadda ya kamata a ce director ya sa an boye su, in har Ita ce a gurbin Ameesha da sai ta yi abjn da ya fi haka"
Wannan shine masomar rigimar, bayan hakan Ameesha Patel da ake zaton zata samu award sai kwatsam aka ji kareena kapoor aka bai wa da refugee wadda ake tunanin kareena ta yi amfani da girman ahalinta dake Bollywood din dan kwatar award din ko dan Ameesha ta ji haushi.
A bikin bada award ta kara da cewa "ita acting ta yi a refugee sabanin Ameesha da fake da Hiritick Roshan a kahona pyar hai"
Har a wannan lokacin Ameesha Patel dai bata tanka mata ba har sai a shekarar 2001 da Kareena ta kai ta Bango.
SMLAWAN✍🏻

