Episode 2
Yadda Kareena ta yi ruwa ta yi tsaki wajen kwace film din Yadeiin daga hannun Ameesha
Bayan batun kareena mai zafi akan Ameesha , kareena ta ci gaba da kanananun magana kan Ameesha , sau tari da yawa takan kushe tufafi idan Ameesha ta saka amma hakan bai sa ameesha ta kula ta ba.
Bayan fitar Kahona pyar hai kowa so yake yaga hadin Hiritick Roshan da Ameesha Patel, hakan yasa aka so hada su da a film din Yadeein sai dai kwatsam aka ci an mayar da Kareena a gurbin Ameesha bayan ameesha ta gama shirya wa.
Ameesha ta ji haushi saboda ta kashe wasu uzurinta saboda fita a film din sai dai duk hakan ta yi kokari wajen hadiye haushinta .
Ana sake Yadeein a kasuwa ya zama mummunar asara wadda a wannan lokacin an tabbatar shi ne film mafi kawo asara sbd ko kashi daya cikk. Goma kudin da aka kashe masa bai dawo ba sannan ya sha suka sosai wajen manazarta da 'yan kallo.
A gefe guda ita kuma ameesha Patel next release dinta da Sony mai suna gadar ek prem katha ya zama film da ya fi kowanne kawo kudi a tarihi a wancan lokacin. Wadda har yanzu yana cikin film mafi kawo kudi duk da ya debi shekaru ishirin da abu da fita.
Ameesha ta ce, "Allah ya so ta ne bata fito a film din Yadeein ba , dan haka idan kareena zata yi kwacen film ta san irin wadda zata kwata"
Hakan ya kara haddasa kareena fado wasu kalamai mararsa dadi kan Ameesha wadda ya kai rigimar ta su wani matakin da ko a wajen taro suka hadu sai dai harara.
Mafi yawanci Kareena ita ce me fara jawowa, sai dai daga bisani itama Ameesha ta nuna mata ita Ba kanwar lasa ba ce. Ku jirani da post na ukun dan ji abin da ya faru bayan Yadeein.
SMLAWAN✍🏻