Ƙayataccen Fim ɗin Barkwanci da Ta Fita a 1994 Me Taken Andaz Apna Apna Wanda Manyan Jarumai Suka Fito Aciki Watau Aamir Khan, Salman Khan, Raveena Tandon da Karisma Kapoor.
A Wata Hira da Akayi da Raveena Tandon Tace Basa Magana da Karishma a Lokacin da ake Aikin Wannan Film Kuma Tace Karishma Ta Haɗa Kai Da Salman Khan Domin Suyi Mata Abinda Ba daidai ba Sedai Ita Kuma Karshma Ta Bayyana Cewa Raveena Tandon Ta Haɗu da Mahaifiyar ta Amma Batayi mata Kulawa Irin Wanda Yakamata Ayiwa Dattawa ba Ta Nuna Cewa Haɗuwar Su Mahaifiyar ta Bai Mata Daɗi ba.
Duk da Haka Karishma Tace Lokacin da Stardust India Sukayi Hira da Ita Raveena tana Tsayawa Akan ta da Ɗabi'a Me Kyau Amma dai Bata San Me Takeyi ba Bayan Karishma Bata Wajen Ko tana Gulmar ta.😊
Sannan Karishma Tace Kamar Yanda Raveena Tandon Tace Ita da Salman Khan Sun Haɗe Mata Kai Sam Ba Haka bane Domin Su A Lokacin Suna da Aikin da Yake Gabansu Balle Har Su Wani Damu da Abinda Wata Take Ciki.
To Wannan Labarin Dai Yana Nunawa Ƙwarewa da Sanin Aiki Na Wannan Jarumai Be Bari Sun Nunawa Ƴan Kallo Cewa Akwai Wata Matsala ta Rashin Jituwa ba Sun Tsaya Sun Nishaɗantar da Ƴan Kallo. Domin Indai Ana Maganar Fina-finai na Barkwanci a Bollywood da Suka Ƙayatar to Andaz Apna Apna Yana Ciki.
#AbbaIndiaDala

