Wani Lokaci Anyi Hira da Tsohon Jarumi Marigayi Kader Khan Yace Shi Ya Gama Karatu Ya karanci Civil engineering Be Taɓa Tunanin Film Shine Aikinsa ba Kawai Abin Ya faru Kamar Haka:-
Wani Lokaci Munyi Wata Drama Se Aka Kaiwa Tsoron Jarumi Dilip Kumar Labari Kawai Ina Zaune Se Naji Kiran Waya Se Na Ɗauka Nace Waye? Yace Min Main Yusuf Khan Bol Raha Hun. Ma'ana Yusuf Khan ne Yake Magana.
Nace Masa Koun Hai Yusuf Khan? Waye Yusuf Khan. Yace Min Log jisse Dilip Kumar Ke Naam Se Jaante Hai. Watau Wanda Mutane Suka fi Kiransa da Dilip Kumar. Kawai Se Wayar ta Faɗi Daga Hannu na 😂
Kader Khan Ya Kara Da Cewa Ai Lokacin Dilip kumar Ya Kalli Wasan Sa Kuma Ya Birge Shi Shi yasa Ya Bashi Dama Ya Fito a Wani Film ɗin sa Sagina. Shidai Sagina Ya Fita a 1974 Kuma Acikin Wannan Film Mata da Miji Na Gaske Watau Dilip Kumar da Saira Banu Sannan Shi Dilip kumar Ɗin Sune Aciki.
Dalilin Kawo Wannan Labari Yana da Alaqa da Watan Disamba Watau A Watan ne Dilip ya Cika Shekaru 100 da Haihuwa Duk da Ya Rasu Shekarar da Ta Gabata 2021. Shi Kuma Kader Khan A Ƙarshen Watan Disamba na 2019 Ya Rasu Yana da Shekaru 81. Duk Kafin Su Rasu Sun Gabatar da Aikin Umara.
#AbbaIndiaDala