MATA A FINA-FINAN INDIYA
Kashi na (03)
Tare da
Haiman Raees
Mu ɗan duba matan fina-finan Indiya a yanzu kafin mu ci gaba.
Iron siga, hali ko siffar da mafi yawancin mata ke fitowa da su a cikin fina-finan Indiya a yau ta saɓa wa duk wani addini da duk wata al'ada da ke ƙasar Indiya. A taƙaice ma dai, su kan su indiyawan sau dama suna ƙorafi akan irin wannan tare da bayyana irin haɗarin da ke tattare da fitowa a irin wannan hali, musamman ga tarbiyyar yara masu tasowa. Ba na buƙatar sai na tsawaita zance anan, amma sanin kowa ne cewa abin da ya rage ba a bayyanawa a cikin shirin fina-finan Indiya a yau bai wuce al'aurar namiji da macen ba. To idan kun fahimci wannan, ashe kenan ba laifi bane don wasu sun nuna cewa sun fi son son kallon fina-finan da saboda sun fi koyar da tarbiyya mai kyau, yayin da na yanzu kuma mafi yawancinsu suke koyar da fitsara da ashararanci.
Akwai mata da yawa da suka yi ƙaurin suna ta wajen iya fitsara, bayyana tsaraici da kuma yin ɗabi'u na rashin ɗa'a a cikin fina-finan Indiya. Daga cikin su akwai Sunny Leon wadda dama can ita fitsararriya ce mai yin fina-finan ashararanci daga bayan ta dawo harkar fim. In ban manta ba sai da aka yi ta cecekuce akan shigowararta harkar fim ɗin saboda iyaye da dama suna ganin cewa fitowar ta a cikin fina-finan zai ƙara dagula musu tarbiyyar yara. Jacqueline Fernandez ita ma ta shahara a wannan fannin.
To sai dai kuma fa, hakan ba ya nufin babu mutanan kirki ko masu kamanta shiga ta kamala a cikin su. Misali, akwai jaruman da ko ba a faɗa maka ba kai kanka za ka iya yabonsu da cewa suna kamantawa. Da haka nake cewa; masana'antar fina-finan Indiya tana wulaƙanta mata ta hanyar sa su suna bayyana tsiraici tare da fitowa a matsayi irin wanda bai dace ba kuma zai iya zuwa ya dawo ya dame su.
To amma me ya jawo haka? Shi ne kwaikwayon fina-finan turai da suke ƙoƙarin yi a kowane lokaci wanda hakan ya sa suka rasa daraja da ƙimar da ake ganin fina-finan su da shi a da.
Zan ci gaba in sha Allah.
©️✍🏻
Haiman Raees
# haimanraees
Miyan Bhai Ki Daring