SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 04
RUBUTAWA: Anupama Chopra
FASSARAWA: Haiman Raees
A ranar uku ga watan Satumba 3, mutane 13,000 suka cika filin da ke Gwinnett Center maƙil. Bhavesh, Tejal, Kishan, da kuma ɗan uwansa Rupesh su ma sun samu halarta daga Dalton. A wannan lokacin Bhavesh yana tare da takardun da ya kwafo daga Yahoo! Maps a aljihunsa.
Da Tejal ta tambaye shi dalilin da ya sa yake tafe da su, Bhavesh sai ya bata amsa da cewa, “Ba ki sani ba. Ta yiwu in hau filin rawa in haɗu da Shah Rukh Khan. Kinga sai in samo wa Kishan sa hannunsa.” Dama sati ɗaya kafin faruwar haka, Bhavesh ya faɗa wa Tejal cewa ya yi mafarki ya shiga filin rawa tare da Shah Rukh Khan har sun yi rawa tare. Tejal sai kawai ta yi dariya ta ce ai babu yadda za a yi ma hakan ta faru.
A filin taron, su Bhavesh suna zaune ne a layi na 12 daga filin rawar. Daga cikin abubuwan da ake gabatarwa Shah Rukh sai ya ke zaɓan mutane biyu daga cikin 'yan kallon suna cashewa tare. Bayan an zaɓi wata yarinya a matsayin wacce za ta yi rawar, sai Shah Rukh yace yana neman mutumin da zai iya rawa. Nan take sai wani abu ya zo ma Bhavesh.
Sai ya ce wa Tejal yana da wata wawiyar shawara da za ta iya kunyata ta. Tejal, wacce a wannan lokaci ta kiɗime, sai ta ce masa ba ta damu ba. Bhavesh, wanda nauyinsa ya kai 200 pounds yayin da tsawonsa kuma ya kai ƙafa biyar da inci tara sai ya miƙe akan kujerar sa ya kama tiƙar wata rawa irin ta 'yan Bhangra abin sa. Shah Rukh sai ya nuna shi yace: “Kai ɗinnan, hawo filin rawar".
Da fari, tabbatuwar cewa zai yi rawa tare da Shah Rukh Khan bai zauna a kwaƙwalarsa ba.
Bhavesh kawai sai ya tsaye a ƙame akan kujerar sa a ruɗe. Shin shi Shah Rukh yake kira ko wani? Tejal sai ta yi masa ihu ta ce, “ ka je kada su kira wani!” Bhavesh sai ya ruga, duk da cewa ƙafafuwansa na gudu, zuciyarsa ta kasa yarda saboda ya ruɗe. A taƙaice dai ya isa wajen yana numfashi sama-sama saboda abubuwa da yawa da suka lulluɓeshi a dai dai lokacin. Tejal ta ce ta yi tsammanin zai fashe da kuka a lokacin.
Haiman Raees
#haimanraees

