LAƘUMAR LIGIDIN LAGWADA
Haƙiƙa jarumi Shamharu ya shaida wa duniya girman shahararsa ta hanyar girgiza tuƙullumar taliƙe matsabban makallata a ko'ina cikin faɗin duniya. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon fitar bijimin shirin nan nasa mai suna Fatattaka wanda jarumi Bijimi da jaruma Tsula suka take masa baya a cikinsa. Shirin, wanda kamfanin Yaji da Yarfe suka shirya, shi ne shiri na farko da jarumin ya jagoranta a cikin shekaru huɗu da suka gabata. Hakan kuma yana da nasaba ne da irin tintsiragudigudin da shirinsa na ƙarshe mai suna Sifili ya yi. Izuwa yanzu dai shirin jarumin ya laƙumo ligidin lagwadar da shirin Babban hula ne kawai ya taɓa lasa har ma yana shirin make shi. Abin alfaharin ma shi ne, duk da an saki sabbin shirye-shirye a cikin 'yan kwanakin nan, hakan bai sa shirin ya tsagaita da lasar ligidin ba.
Haiman Raees
#haimanraees