Fassarar Waƙar Hardum Humdum


Fassarar Waƙar Hardum Humdum

• Waƙa - Hardum Humdum

• Fim - Ludo

• Harshe - Hindi = Hausa 

• Shekarar Fita - 2020

• Sauti - Pritam

• Rubutawa - Sayeed Quadri

• Kamfani - T-Series

• Rerawa - Arijit Singh

• Fassarawa - Haiman Raees 



• Ye Li Hai Meri Aankhon Ne Kasam Ae Yaar

Wannan rantsuwa ce da idanuwana suka yi. 

• Rakhegi Tujhe Khwaab Mein

Cewa za su ajiye ki a cikin mafarkansu. 

• Hamesha Hardum Harpal

Har abada, koda yaushe, kowane lokaci. 

• Harshab Humdum Humdum

A kowane irin yanayi, abokiyar tarayya ta. 

• Ye Li Hai Meri Aankhon Ne Kasam Ae Yaar

Wannan rantsuwa ce da idanuwana suka yi. 

• Rakhegi Tujhe Khwaab Mein

Cewa za su ajiye ki a cikin mafarkansu. 

• Hamesha Hardum Harpal

Har abada, koda yaushe, kowane lokaci. 

• Harshab Humdum Humdum

A kowane irin yanayi, abokiyar tarayya ta. 

• Kitna Hoon Chaahta, Kaise Kahun Tujhe

Ba zan iya bayyana irin ƙaunar da nake yi miki ba. 

• Saaya Tera Dikhe, Toh Choom Loon Usse

A duk sanda na kalli inuwarki, sai in ji kamar in sumbace ta. 

• Jis Din Tujhe Miloon, Dil Yeh Dua Kare

 Tun ranar da na haɗu da ke zuciyata ke addu'ar. 

• Din Yeh Khatam Na Ho, Na Shaam Ko Dhale

Ina ma wannan yinin kada ya ƙare, ina ma ace kada yamma ta yi. 

• Rahe Bas Saath Hum, Tu Rahe Paas

Ina ma ace za mu kasance tare da juna a koyaushe, kuma ki kasance kusa da ni. 

• Rakhun Main Tujhe Baahon Mein

Ina so in rungume ki a hannayena. 

• Hamesha Hardum Harpal

Har abada, koda yaushe, kowane lokaci. 

• Harshab Humdum Humdum

A kowane irin yanayi, abokiyar tarayya ta. 

• Ye Li Hai Meri Aankhon Ne Kasam Ae Yaar

Wannan rantsuwa ce da idanuwana suka yi.

©️✍🏻
  Haiman Raees 
# haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com 

Post a Comment

0 Comments