Fassarar Wakar Ankhiyaan Milaoon Kabhi
•Waƙa - Ankhiyaan Milaoon Kabhi
• Fim - Raja
• Harshe - Hindi/Hausa
• Shekarar Fita - 1995
• Sauti - Nadeem-Shravan
• Rubutawa - Sameer
• Kamfani - Tips Music
• Rerawa - Udit Narayan & Alka Yagnik
• Fassarawa - Haiman Raees
• Ankhiyaan Milaoon, Kabhi Akhiyaan Churaoon
Wani lokaci sai in kalli idanunka, wani lokaci kuma sai in ji kunyar kallon su.
• Kya Tune Kiya Jaadu
Wani irin asiri ne ka min haka?
• Haan Ankhiyaan Milaoon, Kabhi Akhiyaan Churaoon

• Kabhi Ghabraoon, Kabhi Gale Lag Jaoon
Wani lokaci nakan ji tsoro, wani lokaci kuma na rungume ka.
• Mera Khud Pe Nahi Kaabu
Na kasa mallakar kaina.
• Bina Payal Ke Hi Baje Ghungroo (x2)
Sarƙoƙin ƙafa na fitar da sauti ba tare da an sanya su ba.
• Ankhiyaan Milaye Kabhi Ankhiyaan Churaye
Wani lokaci sai ki kai duba, wani lokaci kuma ki kau da kai.
• Kya Maine Kiya Jaadu
Ban san wane irin asiri na yi miki ba.
• Ankhiyaan Milaye Kabhi Ankhiyaan Churaye
Wani lokaci sai ki kai duba, wani lokaci kuma ki kau da kai.
• Kya Maine Kiya Jaadu
Ban san wane irin asiri na yi miki ba.
• Kabhi Ghabraye, Kabhi Gale Lag Jaaye
Wani lokaci sai ki ji tsoro, wani lokaci kuma sai ki rungume ni.
• Tera Khud Pe Nahi Kaabu
Kin kasa mallakar kan ki.
• Bina Payal Ke Hi Baje Ghungroo (x2)
Sarƙoƙin ƙafa na fitar da sauti ba tare da an sanya su ba.
Aa Aa Aaa… Aa Aa Aa Aaa…
• Aise To Deewane Mujhe Pyaar Na Kar
Kada ka yi min irin wannan son, ya kai me haukan so.
• Aati Hai Sharam Deedar Na Kar
Kunya nake ji, ka daina min irin wannan kallon.
• Chain Chura Ke Takraar Na Kar
Kada ki takura wa jin daɗi na kuma ki takale ni da faɗa.
• Tujhko Kasam Inkaar Na Kar
Kada ki ce min a'a yanzu.
• Tere Armaanon Mein Sawar Gayi Main
Na ƙawatu a cikin muradanka.
• Tune Mujhe Dekha To Nikhar Gayi Main
Tun da ka kalle ni na fara sheƙi.
• Dekha Jab Tujhko Theher Gaya Main
Ina ganin ki na tsaya.
• Aise Hi Adaon Pe To Mar Gaya Main
Na kamu da ƙaunar ki saboda alherin da ke tare da ke/salon ki.
• Ankhiyaan Milaoon, Kabhi Akhiyaan Churaoon
Wani lokaci sai in kalli idanunka, wani lokaci kuma sai in ji kunyar kallon su.
• Kya Tune Kiya Jaadu
Wani irin asiri ne ka min haka?
• Haan Ankhiyaan Milaoon, Kabhi Akhiyaan Churaoon
Wani lokaci sai in kalli idanunka, wani lokaci kuma sai in ji kunyar kallon su.
• Kya Tune Kiya Jaadu
Wani irin asiri ne ka min haka?
• Ankhiyaan Milaoon, Kabhi Akhiyaan Churaoon
Wani lokaci sai in kalli idanunka, wani lokaci kuma sai in ji kunyar kallon su.
• Kya Tune Kiya Jaadu
Wani irin asiri ne ka min haka?
• Kabhi Ghabraoon, Kabhi Gale Lag Jaoon
Wani lokaci nakan ji tsoro, wani lokaci kuma na rungume ka.
• Mera Khud Pe Nahi Kaabu
Na kasa mallakar kaina.
• Bina Payal Ke Hi Baje Ghungroo (x2)
Sarƙoƙin ƙafa na fitar da sauti ba tare da an sanya su ba.
Aa Aa Aaa… Aa Aa Aa Aaa…
• Meri Jaan-E-Jaana Kya Cheez Hai Tu
Ya abar son rayuwata, ban san ta yaya zan misalta ƙimar da kike da shi a wajena ba.
• Mujhko To Jaan Se Azeez Hai Tu
Kin fi min rayuwata muhimmanci.
• Itni Na Kar Taarif Meri
Ka daina zuga ni haka.
• Jaanu Main To Jaanu Chaahat Kya Teri
Na san irin ƙaunar da kake yi min.
• Teri Ulfat Ka Nasha Chha Gaya
Mayen soyayyar ki ya bi ko'ina.
• Kuch Bhi Ho Jaaneja Mazaa Aa Gaya
Koma menene ya faru, na ji daɗinsa sosai.
• Dheere Dheere Duniya Se Door Hui
A hankali na rabu da duniya.
• Ishq Mein Tere Main To Choor Hui
Na shafa'a sam a cikin ƙaunarka.
• Ankhiyaan Milaye Kabhi Ankhiyaan Churaye
Wani lokaci sai ki kai duba, wani lokaci kuma ki kau da kai.
• Kya Maine Kiya Jaadu
Ban san wane irin asiri na yi miki ba.
• Ankhiyaan Milaye Kabhi Ankhiyaan Churaye
Wani lokaci sai ki kai duba, wani lokaci kuma ki kau da kai.
• Kya Maine Kiya Jaadu
Ban san wane irin asiri na yi miki ba.
• Kabhi Ghabraye, Kabhi Gale Lag Jaaye
Wani lokaci sai ki ji tsoro, wani lokaci kuma sai ki rungume ni.
H• Tera Khud Pe Nahi Kaabu
Kin kasa mallakar kan ki.
• Bina Payal Ke Hi Baje Ghungroo (x3)
Sarƙoƙin ƙafa na fitar da sauti ba tare da an sanya su ba.
Aa Aa Aaa… Aa Aa Aa Aaa…
✍🏻
Haiman Raees
# haimanraees
Infohaiman999@gmail.com
Miyan Bhai Ki Daring