Fassarar Waƙar Tere Naal Ishqa

Fassarar Waƙar Tere Naal Ishqa

• Waƙa - Tere Naal Ishqa
• Fim - Shivaay
• Harshe - Hindi/Hausa 
• Shekarar Fita - 2016
• Sauti - Mithoon
• Rubutawa - Sayeed Quadri
• Kamfani - T-Series
• Rerawa - Mithoon feat Kailash Kher
• Fassarawa - Haiman Raees 

Ooo… Aaa…

• Teri Tarah Mujhe Duniya Mein Nahi Koi Chaah Sakta

Babu wacce za ta iya so na kamar yadda kika so ni a duniyar nan. 

• Tere Dil Mein Fikr Meri Rahe Sham-O-Subah

Damuwa akaina shi ne abin da ya kasance a zuciyar ki tsawon yini. 

• Tere Dil Mein Har Pal Har Dam Hai Khayaal Mera Hi Hai Basta

Tunani akaina ya wanzu cikin zuciyar ki koda yaushe, tsawon yini. 

• Tere Lab Pe Zikr Mera Rahe Sham-O-Subah

Furuci a kaina ya zama abin ambaton ki tsawon yini. 

• Tere Saath Hoon Mehfooz Sada Itna Tujhpe Hai Yaqeen Mera

Ina cikin aminci tare da ke, na yarda dake sosai. 

• Tapti Jalti Inn Raahon Mein Tu Saaya Mera

A wannan hanyar me ƙuna, ke ce inuwa ta. 

• Sehra Bhi Hai Gulshan Ban Jata Khushboo Ki Tarah Jab Tu Aata

Hatta sahara ma komawa take yi kamar lambun fure yayin da kika zo kamar turare. 

• Iss Zindagi Mein Har Ghadi Chahun Teri Panaah

Ina so in kasance a ƙarƙashin tsaron ki har ƙarshen rayuwata. 

• Tere Naal Ishqa Mera, Tere Naal Ishqa Mera

Na kamu da ƙaunar ki, na kamu da ƙaunar ki. 

• Lagta Ibaadat Warga

Wannan soyayyar ta fi kama da bauta. 

• Tere Naal Ishqa Mera Mera

Na kamu da ƙaunarki. 

• Zyada Main De Doon Sadka, Zyada Main De Doon Sadka

A shirye nake da in ba da abin da ban saba badawa ba. 

• Lagta Ibaadat Warga

Wannan soyayyar ta fi kama da bauta. 

• Tere Naal Ishqa Mera Mera

Na kamu da ƙaunarki. 

Aa... Aaa…

• Tapti Jalti Inn Raahon Mein Tu Saaya Mera

A wannan hanyar me ƙuna, ke ce inuwa ta. 

• Ho Ek Tere Seene Se Lag Kar Hi Mere Dil Ko Aaye Sukoon

Zuciyata na samun nutsuwa ne kawai yayin da kika rungume ni. 

• Jab Gham Koi Sataaye Mujhe Main Tujhe Hi Toh Dekhun

Duk lokacin da wani baƙin ciki ya dame ni, ke nake nema. 

• Jazbaat Mere Na Koi Samjha Iss Duniya Mein Tu Ek Tere Siva

Ke kaɗai ce a duniyar nan kika fahimci yanayina. 

• Har Din Har Shab Teri Baahon Mein Hai Chain Mila

A kowace rana, kowane dare, ina samun nutsuwa ne kawai yayin da nake hannun ki. 

• Sehra Bhi Hai Gulshan Ban Jata Khushboo Ki Tarah Jab Tu Aata

Hatta sahara ma komawa take yi kamar lambun fure yayin da kika zo kamar turare. 

• Iss Zindagi Mein Har Ghadi Chahun Teri Panaah

Ina so in kasance a ƙarƙashin tsaron ki har ƙarshen rayuwata. 

• Tere Naal Ishqa Mera, Tere Naal Ishqa Mera

Na kamu da ƙaunar ki, na kamu da ƙaunar ki. 

• Lagta Ibaadat Warga

Wannan soyayyar ta fi kama da bauta. 

• Tere Naal Ishqa Mera Mera

Na kamu da ƙaunarki. 

• Zyada Main De Doon Sadka, Zyada Main De Doon Sadka

A shirye nake da in ba da abin da ban saba badawa ba. 

• Lagta Ibaadat Warga

Wannan soyayyar ta fi kama da bauta. 

• Tere Naal Ishqa Mera Mera

Na kamu da ƙaunarki. 

• Ho Tera Naam Main Jis Bhi Ghadi Honthon Pe Laata Hoon

A duk lokacin ambaton ki ya fito daga bakina. 

• Lafzon Mein Kahin Khud Hi Chupa Ehtraam Main Paata Hoon

Sai wani ɓoyayyen mutuntawa ya fito a cikin kalaman da na furta kai tsaye. 

• Chaahe Dekh Loon Main Saara Yeh Jahan Sabse Haseen Manzar Tu Mera

Ko da ace zan zagaye duniya ne baki ɗaya, a wajena ke ce abu mafi kyawun gani. 

• Rehta Basta Nigaahon Mein Ek Chehra Tera

Fuskar ki na wanzuwa a idona koda yaushe. 

• Sehra Bhi Hai Gulshan Ban Jata Khushboo Ki Tarah Jab Tu Aata

Hatta sahara ma komawa take yi kamar lambun fure yayin da kika zo kamar turare. 

• Iss Zindagi Mein Har Ghadi Chahun Teri Panaah

Ina so in kasance a ƙarƙashin tsaron ki har ƙarshen rayuwata. 

• Tere Naal Ishqa Mera, Tere Naal Ishqa Mera

Na kamu da ƙaunar ki, na kamu da ƙaunar ki. 

• Lagta Ibaadat Warga

Wannan soyayyar ta fi kama da bauta. 

• Tere Naal Ishqa Mera Mera

Na kamu da ƙaunarki. 

• Zyada Main De Doon Sadka, Zyada Main De Doon Sadka

A shirye nake da in ba da abin da ban saba badawa ba. 

• Lagta Ibaadat Warga

Wannan soyayyar ta fi kama da bauta. 

• Tere Naal Ishqa Mera Mera

Na kamu da ƙaunarki. 

• Mere Sang Tu Sada

Kina tare da ni a koyaushe. 

• Tu Hai Saaya Mera

Ke ce Inuwa ta. 

• Chaahun Teri Panaah…

Ina so in kasance a ƙarƙashin kulawar ki. 

• Mere Sang Tu Sada

Kina tare da ni a koyaushe. 

• Tu Hai Saaya Mera

Ke ce Inuwa ta. 

• Chaahun Teri Panaah…

Ina so in kasance a ƙarƙashin kulawar ki.

✍🏻
  Haiman Raees 
# haimanraees 

Miyan Bhai Ki Daring

Post a Comment

0 Comments