Wasu Abubuwa na musamman game da jaruma kajol da ba kowa ya sani ba.
Credits: Isma'il Gambo
1 Ita da Rani Mukreji 'yan uwan juna ne
2 Jarumar 'yar gidan tsohuwar jaruma Tanuja ce.
3 An san da cewa maza ke furta Kalmar so ga mata, sai dai kajol ita ta durkusa gaban Ajay ta furta masa tana sonsa kuma ya amince.
4 jarumar bata kasance mai yawan magana ba , ko shiga cikin mutane ta fi sha'awar karance karancen littafi idan bata komai.
5 Jarumar bata taba shiga cikin ba da sunan dafa abinci , saboda lokacin da take yarinta mamarta kullum tana location, bayan ta fara girma aka kai ta sakandire daga nan ita ma ta zama jaruma hakan yasa dafa abinci baya cikin tsare-tsarenta.
6 Jarumar bata son rawa da ya wuce gona da iri , hakan yasa ta yi rejecting film din Dil To Pagal Hai da Devdas
7 Duk da irin competition na jarumai mata a 90s dama early 2000s ita ce jarumar dake da mafi yawan Filmfare award for best actress (tied with Nutan) in da take rike da award 5 gaban su madhuri, Juhi, karishma, sredevi da ma vidya balaan
8 Ita ce jaruma ta farko a tarihin India da ta samu award na negative role da film din Gupt
9 Jarumar ta dauki film din We are Family dauke da juna biyu a jikinta, hakan nan ta dauki film din KKKG da juna biyu a jikinta wadda ya bare, (miscarriage) kafin a gama daukar film din, sannan a lokacin daukar film din KKKH ta kamu da ciwon mantau sakamakon faduwa da ta yi a keke lokacin daukar wakar Ye ladka Hai.... Inda ta kasa tunawa da komai sai sunan Ajay Devgan kafin daga bisani ta samu sauki
10 Jarumar bata da wata kawa a cikin yammatan Bollywood sai abokan mutunci, abokanta maza sune Karan Johar da Sharu Khan
11 Ita kadai ce jarumar da ta yi film 5 da sharu khan kuma mafiya nasara idan aka cure su guri guda.
13 Ita ce jarumar da duk film din karan johar sai an ganta koda kuwa fitowa daya ce kafin lokacin da suka samu sabani daga bisani kuma suka sasanta.
14 Jarumar bata kwalliyar indai bai zama a film ba ko kuna dole kamar yadda aka ganta a KKKH
15 Tana cikin jarumai 5 da aka yi mutum mutumin su a kasar turawa dan nuna girmanawa.