SS RAJAMOULI YA NEMI AFUWAR DA YA KWATANTA HRITHIK ROSHAN DA PRABHAS DAYA CE HRITHIK BA KOMAI BANE IDAN AKA HADA SHI DA PRABHAS
_______Wani tsohon bidiyo na SS Rajamouli daya kwatanta jarumi Hrithik Roshan da Prabhas ya yi ta yaduwa a intanet ayi tayin cece-kuce Akan shi A cikin tsohon bidiyon, Director SS RAJAMOULI ya bayyana cewa a cewarsa Hrithik Roshan ba komai bane a gaban Prabhas. Sai dai a kwanan baya Director ya nemi afuwa kan kalaman nasa kuma ya bayyana cewa ba daidai ba ne Kan kalaman da ya yi a lokacin kuma bai yi niyyar wulakanta Jarumi Hrithik din ba.
_______Kamfanin dillancin labarai Mai suna Reuters ya bayyan, ta hanyar ANI, an tambayi Rajamouli game da maganar da yayi wacce ta haifar da cece-kuce, wanda ya amsa da cewa, “ wannan Vedio Ya dade, da dadewa - Ina tsammanin wasu shekaru 15-16 baya. Amma eh, zaɓin kalmomi na ba su da kyau, dole ne in yarda. Niyyata ba ta taba wulakanta shi ba, ina girmama shi sosai. Kuma Ina neman afuwa. Mutane da dama sun yaba wa daraktan saboda tawali'u da kuma amincewa da kuskurensa.
✍️✍️
YUSUF KHAN DORAYI
#YUSUFUMAR