~Shah Rukh Khan.
~Vidya Balan.
~Irrfan Khan.
~Rajeev Khandelwal.
~Ram Kapoor.
~Ayushmaan Khurrana.
~Jarumi "Shah Rukh Khan" ya fara career ɗin sa da wani ƙaramin TV shows _"Series Film"_ mai suna Fauji da kuma Circus, a 1989,
A haka dai yayi ta fafutuka har zuwa shekarar 1992 inda aka fara shirya masa cikakken Film ɗin sa na farko mai suna Deewana, daga nan kuma har yakai inda yakai a halin yanzu.
Vidya Balan
Jaruma "Vidya Balan" da wani Film ɗin barkwanci mai dogon zango tun a 1995, mai suna "Hum Paanch" inda kuma a shekarar 2005, tayi Film ɗin ta mai suna Parineeta wanda suka fito tare da jarumi "Saif Ali Khan" kuma shine ya kafa jarumar a Hindi Cinema.
Daga nan ne kuma tayi ta fitowa a fina-finai gadan gadan bisa salo na ƙwarewa, har ana yi mata laƙabin Versatile actress ma'ana takan iya hawa ko wanne mataki idan aka bata a cikin Film.
Irrfan Khan
Jarumi Irrfan Khan shima ya fara career ɗin sa ne da fina-finai masu dogon zango irin su; Chanakya, Chandrakanta, Mahanharata da kuma Bharat Ek Khoj.
Daga baya kuma sai jarimin ya fara taka rawa da film ɗin "Salaam Bombay," a shekarar 1988 inda yayi ta jan zaren sa har kusan shekaru 30 har lokacin da rai yayi halin sa a ranar 29 April 2020.
R.MADHAVAN
Shima dai wannan jarumi wanda cikakken sunan sa shine Ranganathan Madhavan, an fara ganin sa tun a shekarar 1993, da wasu TV Shows, irin su "Benegi Apni Baat", da kuma "Ghar Jamai.
Daga baya kuma jarumin ya fara fitowa a fina-finan yankin Tamil inda yayi wani Film ɗin soyayya mai suna "Alaipayuthey" 2000, daga nan kuma tauraruwar sa ta cigaba da haskawa a masana'antar.
Ayushmaan Khurrana
Jarumi "Ayushmaan Khurrana" shima TV shows ɗin ya fara irin su; "Ek Thi Rajkumari", da kuma "The Voice of Youngistan," har ma da "Kayamath,"
Daga baya kuma ya kafu a Bollywood a shekarar 2012 da film mai suna "Vicky Donor" was loved by the audience.
Daga nan kuma sai aka cigaba da damawa dashi a Hindi Cinema gadan-gadan har zuwa inda yake a halin yanzu.
Jaruma "Yami Gautam" ta fara da TV shows na South Indian mai suna "Chaand Ke Paar Chalo" a shekarar (2008–2009), ta ƙara yin wani TV series ɗin mai suna "Yeh Pyar Na Hoga Kam" (2009–2010), inda daga nan kuma ta cigaba da fitowa a fina-finai musamman na Malayalam, Tamil da Telugu,
A shekarar 2012 jarumar ta fara fitowa a Hindi Cinema da Film mai suna "Vicky Donor" inda suka fito tare da jarumi "Ayushmann Khurrana" inda kuma aka ci-gaba da damawa da ita har zuwa yanzu.
RADHIKA MADAN
Ita ma dai wannan matashiyar jaruma mai shekaru 27 yanzu haka wato "Radhika Madan" ta fara fitowa ne a wani Film mai dogon zango, wanda na gidan television ne mai suna "Meri Aashiqui Tum Se Hi" inda ta shafe shekaru biyu tana yin sa (2014–2016),
A shekarar 2018 wani Producer Director mai suna "Vishal Bhardwaj" ya sanya ta a wani Film mai suna "Pataakha" inda suka fito tare da jaruma "Sanya Malhotra",
Jarumar tayi matukar kokari a wannan Film, har saida ta samu kyautar "Screen Award for Best Female Debut" ma'ana lambar girma a matsayin ta na sabuwar fuska a Bollywood ɗin.
@AyƘoƘi