SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 03

SHAH RUKH KHAN DA BOLLYWOOD 03




RUBUTAWA: Anupama Chopra 

FASSARAWA: Haiman Raees 

ABBAS MUSTAN: 'Yan uwa ne da ke bada umurnin fina-finai tare. 

YASH CHOPRA: HamshaÆ™in mai shirya fina-finan da É—aukaka sosai kenan a Bollywood. 

B. R. CHOPRA: Yaya ne a wajen Yash kuma shi ma shirya fina-finan yake yi. 

ADITYA CHOPRA: Babban ɗa kenan a wajen Yash, shi ne ƙashin bayan tsayuwa da ɗaukakar kamfaninsu a duniya

KARAN JOHAR: Mai shirya fina-finan Indiya ne da yazo a Æ™arni na biyu a zamunnan Bollywood kuma shi ne ya bada umurnin wasu fitattun fina-finan Shah Rukh. 

YASH JOHAR: Shi ne mahaifin Karan kuma shima babban mai shirya fina-finan Indiya ne, ya mutu a 2004

SOORAJ BARJATYA: Mai shirya fina-finan Indiya ne da ya zo a Æ™arni na uku daga cikin zamunnan da ya kawo ci gaba da gyara sosai a shekarun 1990s da manyan fina-finansa. 

PRAHLAD KAKKAR: ÆŠaya ne daga cikin fitattun masu bada umurnin tallace-tallace da ya yi aiki sosai da jarumi Shah Rukh.

AISHWARYA RAI: Tsohuwar Sarauniyar kyau ta duniya wacce ta zamo babbar jaruma daga baya. 

GULSHAN KUMAR: hamshaÆ™in É—an kasuwa ne da ya zama 'Audio King of India' da 'yan daban Mumbai suka harbe shi ya mutu. 

ABU SALEM: Wani hamshaƙin ɗan daba ne da ya addabi Bollywood da barazana da kisa a shekarun 1990s.

DAWOOD IBRAHIM KASKAR: Babban É—an daba ne a garin Mumbai, shi ake zargi da shirya tashin bam a 1993.

RAKESH MARIA: Babban É—an sanda ne daga Mumbai, shi ne ya jagoranci binciken tashin bam É—in. 

MOHAN BHISE: Shi ne mai tsaron Shah Rukh. 

CHHOTA SHAKEEL: Babban É—an wasa ne a tawagar Dawood. 

SANTOSH SIVAN: sanannen mai bada umurni kuma mai horas da jarumai da suka yi aiki tare da 
 Shah Rukh.

HRITHIK ROSHAN: ÆŠa a wajen Rakesh Roshan wanda ya samu É—aukaka ta ban mamaki cikin dare É—aya tun bayan fitowar fim É—insa na farko Kaho Naa . . . Pyaar Hai.

SANJAY LEELA BHANSALI: Fitaccen mai bada umurni ne a Bollywood da babu kamarsa a salo. 

BHARAT SHAH: Fitaccen mai yaÉ—a fina-finan Hindi ne shi, ana kuma kiran Bharat da suna Mr. Moneybags.

NAZIM RIZVI: Matsakaicin mai ɗaukar nauyi ne da aka kama su tare da Bharat Shah bisa harƙalla da 'yan daba.

MAFARKAN BOLLYWOOD. 

Mafarki ya zama gaske a Dalton. Wani Æ™aramin gari ne da ke Georgia da ake yi wa laÆ™abi da 'carpet capi-tal of the world', wannan gari, gari ne mai cike da karamomi/mu'ujizozi. Bhavesh Sheth ya san hakan. 

Bhavesh, kakkauran mutum ne da ke yawan sa tabarau kuma yana da dunÆ™ulallen gashi tare da himma a cikin lamaransa. Ya fita daban a Dalton. Yana É—aya daga cikin Æ™alilan É—in indiyawan da ke zaune a wurin. Kaso biyu cikin yawan mutanen da ke rayuwa a wurin su 27,912 ne kawai suka zo daga yankin Asiya. Mafi yawancinsu likitoci ne, amma shi Bhavesh yana harkar masaukin baÆ™i ne. Mahaifinsa, Ramesh, shi ke kula da wani Super 8 Motel da ke kusa da cibiyar al'adu na Dalton. 

Sana'arsu ta ahali ce. Ramesh shi ne general manager yayin da shi kuma Bhavesh yake mataimakinsa. Matansu ma kan taimaka wajen kula da sana'ar tasu. Bhavesh bai taÉ“a zama a Æ™asar Indiya ba. Mahaifinsa ya bar Æ™asar ne tun a farkon 1970s, kuma an haifi Bhavesh ne a Canada a shekara ta 1974. Ramesh yana tafiya wurin da akwai aiki ne. Bhavesh ya girma ne a tsakanin Detroit, Houston, da Tennessee. Yakan ziyarci Indiya tare da iyayensa aduk lokacin da suke da halin zuwa, amma a 1999, an yi musu haÉ—in aura da wata mace mai suna Tejal wacce ita kuma a Gujarat aka haife ta kuma a can ta taso.  

Kamar dai sauran miliyoyin Indiyawa da ke ko'ina a duniya, Bhavesh yana alaÆ™antuwa da Indiya ne kawai ta hanyar fina-finan Hindi. Iyayensa na kallon su akai-akai, sau tari a bidiyo. Kwafin da ake siyarwa na satar fasaha duk da rashin fitowarsa sosai, hakan bai hana a siya a kalla. Duk sa'adda Amitabh Bachchan yayi wata mutuwa a cikin fim, Bhavesh wanda a wancan lokacin bai fi shekara tara ba, sai ya yi ta rusa kuka. Ramesh sai ya rarrashe shi tare da tabbatar masa da cewa hamshaÆ™in jarumin ba mutuwar gaske ya yi ba, mutuwar ba'a ce ya yi domin ya sake dawowa watarana ya mishaÉ—antar da su. A Yayinda yake Æ™ara girma Bhavesh ya ci gaba da kallon fina-finan Hindi sosai. Ita ma Tejal masoyiyar fina-finan ce, haka ma É—ansu Kishan wanda aka haifa a 2002, shi kam saboda son su ma tun kan ya fara iya magana ya fara kallon su. Hakan yasa a lokacin da aka fara shagalin taron rawa da waÆ™a na Temptation a 2004 ya zama babu zaÉ“i face kawai su halarta. Shi wannan shagali an shirya shi ne tare da manyan jaruman Bollywood a Gwinnett Center da ke Atlanta. Haka Bhavesh ya siyar da kyautukan zagayowar ranar haihuwarsa, da kyautukan ranar aurensa duka ya siya tikitai akan farashin dala $150 kowanne. Saboda a lokacin da ya kira, fitattun kujerun da ke kan farashin dala $200 tuni an siye su. 

Temptation shagali ne irin na haÉ—akar jaruman Bollywood yayin da suke hawan fitattun waÆ™oÆ™in fina-finai tare da rawa, barkwanci da kuma haÉ—uwa da masoyan jaruman. Manyan jarumai guda shida ne suka halarci shagalin, kowanne da irin yanayi da salon da ya É—auka. Amma wanda ya fi kowa jan hankali shi ne Shah Rukh Khan. An shirya zagayen wannan shagali ne akan cewa za a yi watanni biyu ana yinsa a cikin manyan birane shida a tsakanin Europe, United Kingdom, United States, da Canada. Kowane taro daga cikinsu yana É—aukar mutane a Æ™alla daga 7,000 zuwa 20,000. Mafi tsadar tikitan kuma an siyar da su ne akan kuÉ—i kimanin dala $300 zuwa dala $400, amma tsadar su bai hana masoya zuwa ba, a Toronto sai da aka kori mutane da dama a Æ™aton filin Air Canada Centre wanda ke É—aukar a Æ™alla mutane 19,800, inda a Æ™arshe dai dole aka shirya taro na biyu bayan kwanaki uku da yin na farkon. Haka ma aka yi London, can ma sai da aka yi taruka biyu a jere. A Antwerp ma an cike É—akin taron da Indiya waÉ—anda ke zaune a can. Indiyawa ne da aka kawo su Æ™asar Holland ta yankin gabas a tsakanin Shekarun 1873 da 1916 domin yin aikin Æ™arfi. 

Amma duk da cewa an daÆ™ile kusantuwarsu da Indiya na tsawon zamunna hakan bai dusashe soyayyarsu wa Bollywood ba. Kamar yadda mai shirya fina-finai Nasreen Munni Kabir ta bayyana a fim É—inta mai suna The Outer World of Shah Rukh Khan, ana yi wa jaruman Bollywood soyayya kamar yadda ake yi wa mawaÆ™i Elvis. Masoya masu magana da harshen turanci sun tsaya Æ™yam a zaurukan otal-otal da misalin Æ™arfe 2 a.m. Domin su samu damar ganin jarumansu. A yayin gabatar da taron kuwa, 'yan mata ne suke kuka da hawaye suna cewa “Muna sonka Shah Rukh Khan!” 

Masu shirya taruka na yankin sun ce sai da suka dinga Æ™in karÉ“ar tayin dala $2,000 domin samun damar shiga wurin fita ta baya. A Mujallar Time Magazine ta yankin Asiya wacce ke É—auke da hoton Shah Rukh a bangonta kuma take É—auke da bayanan jaruman yankin Asiya, jaridar ta ruwaito cewa mai tsaron jarumi Shah Rukh wanda yake Æ™aton mutum ne mai molo akansa yana kuma da 'ya'ya mata biyu a gida, yace mata da yawa sun kawo masa tallan kansu in yana so ya kwana da su ta yadda abin ma har ya zama ya dame shi. 

Zan ci gaba in sha Allah 

Haiman Raees
#haimanraees 

Post a Comment

0 Comments