MATA A FINA-FINAN INDIYA 02



MATA A FINA-FINAN INDIYA 02



                 Kashi na (02)

                   Tare da

          
                   Haiman Raees 
          

Tsiraici A masana'antun fina-finan Indiya. 

Kamar yadda na kawo rabe-ben irin halaye ko É—abi'un da mata kan fito a ciki a fina-finan Indiya. In kuka yi duba da kyau za ku ga cewa a yau mafi yawancin fina-finan da matan ke fitowa a ciki suna fitowa ce da shiga ko siffa ko hali kwatankwacin na matan da ke fitowa a cikin fina-finan turai. Misali; sau da dama ana nuna matan nan a fina-finai a matsayin ababen marmari ne kawai da sha'awa, wannan shi ya jawo tasgaro game da soyayya da kuma yadda ake bayyana mata a masana'antun fina-finan Æ™asar Indiya. 

A da, ba a san wani abu wai shi 'sumba' (wato kiss) a fina-finan Indiya ba, asali ma, sai da aka É—auki tsawon shekaru a wannan yanayi kafin a fara, amma yau fa? Abu ne mawuyaci a samu fina-finai biyar daga cikin fina-finai kusan dubu É—aya da ake fitarwa a cikin kowace shekara daga dukkan masana'antun fina-finan Indiya wanda ba a sumba, fitsara ko kuma nuna tsiraici a ciki. A cikin fina-finan da, nuna soyayya a fili an barshi ne wa fina-finan turai kawai, amma a yau za ka sha mamakin irin yadda ake fitsara da baÉ—ala a cikin fina-finan Indiya, abin har ya kai ga iyaye da dama a nan Æ™asar Hausa yanzu ba sa iya barin 'ya'yansu su kalli mafi yawancin fina-finan saboda fitsara ko ta'addanci da ya yi yawa a fina-finan, alhali da kusan kowane gida babu abin da ake kallo sama da su. 

A da, masu ruwa da tsaki wajen shirya fina-finai, musamman daraktoci. Suna amfani da hanyoyi uku ne wajen isar da saÆ™on soyayya ko tarayya ko alaÆ™a mai zurfi a tsakanin mace da namiji. WaÉ—annan hanyoyi kuwa su ne: shigar al'ada, mafarki da kuma bayan gari ko cikin daji. Bari in bi su É—aya bayan É—aya in faÉ—aÉ—a bayani. 

SHIGAR AL'ADA 

Kasancewar mafi yawancin fina-finan Indiya sun Æ™unshi rawa da waÆ™a, daraktoci na amfani da shigar al'ada wajen bayyana sassan jikin mace, musamman daga cikinta zuwa Æ™asan cibiyarta. 

MAFARKI 

Fitowar mafarki tana ba wa daraktoci damar bayyana tsiraici ko nuna yadda ake lalata ko aikata masha'a cikin sauÆ™i. Akan nuno mace sanye da sari, ruwan sama ko kuma na wani wuri can daban ya jiÆ™a mata jiki sarin ya manne da jikinta ta yadda kana iya ganin komai a bayyane, ko kuma in iska ta kaÉ—a ka ga ta yaye sarin komai ya fito waje. In ya so bayan an gama abin da aka yi niyya, sai a nuna wa masu kallo cewa ai duk ma a mafarki ne abin, shikenan. 

 BAYAN GARI KO CIKIN DAJI. 

Sau da dama waÆ™oÆ™i da raye-raye na ba wa jaruman shiri damar zuwa bayan gari ko cikin daji. A irin wannan fitowa akan ga jarumar ta ruga a guje ta shiga daji, yayin da shi kuma jarumin zai bi ta a guje shi ma su shige cikin ganyayyaki, da sun fito sai a nuno ta tana goge leÉ“enta, daga nan kai mai kallo ka san me ya faru. 

Wannan shi ne tsarin da ake bi a da wajen bayyana irin waɗannan abubuwa, to a da manya ne kaɗai ke iya fahimtar manufofin irin waɗannan saƙonnin. Kuma a hakan ma ba a wuce gona da iri, amma yanzu abin ya wuce inda ake tunani, kuma a ƙarshe dai, matan da su ake amfani wajen cimma burikan da ake so a cimma.

Zan ci gaba in sha Allah. 


  Haiman Raees 
# haimanraees 


Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form