RUGUGIN RUGUNTSUMI DA RAGARGAZA
Izuwa yanzu dai ana iya cewa duniya ce gaba ɗayanta ke jiran fitowar ƙasurgumin shirin nan na ƙasar Indiya wanda jarumi Shamharu zai jagoranta mai suna Fatattaka. Shirin Fatattaka dai shiri ne wanda ya zamo abin tsumaye ga masoya jarumi Shamharu, yayin ya zamo abin caccakar 'yan adawa kuma hana-baccin maƙiya tun gabanin fitarsa. Abin ya ƙara ba wa ma'abota bibiyar fina-finan Indiya mamaki duba da irin yadda masu hasashe ke ganin cewa shirin a shirye yake tsaf da ya karya tarihin tattara matsabbai irin wanda suka haura wanda ƙasurgumin shirin Shantali Uban Mas'ud mai suna Babbanƙara ya kafa a yayin fitarsa. Wasu kuma gani suke ma shirin na ita ƙwamuso damman da suka kai karo 100 a cikin kwana biyu kacal. Maganar zahiri dai ita ce, ƙasar Indiya ba ta taɓa ganin irin wannan rugugin ba, kuma idan har wannan shiri ya samu karɓuwa, to lallai zai tada ruguntsumin da zai jawo ragargajewar tarihin fina-finani da dama a ƙasar. Shin Sarki Shamharu shahararre ne zai share wa 'yan adawa da maƙiya tantama ko kuwa su ne za su yi masa sakiyar da babu ruwa ya faɗo ta ka? Za mu ga yadda za ta kaya a yayinda da shirin ya fito a ranar 25 ga watan Janairun bana. Bayan Shamharu, shirin ya ƙunshi jarumai irin su Tsula mai tsula tsiya da tsiyataku, bijimi mai girman kawai da kuma fitowa ta musamman da ake sa rai Tumbiɗo zai yi shima.
Haiman राईस
#haimanraees
bollywoodnigeria.blogspot.com