Fassarar Waƙar Dheera Dheera



Fassarar Waƙar Dheera Dheera

▪️Waƙa - Dheera Dheera 
▪️Fim - KGF: Chapter 1
▪️Shekarar Fita - 2018
▪️Harshe - Kannada/Hausa 
▪️Sauti - Ravi Basrur
▪️Kamfani - 
▪️Rubutawa - Ravi Basrur
▪️Rerawa - Ananya Bhat, Santhosh Venky, Sachin Basrur, Puneeth Rudranag, Mohan Krishna, H. Shreenivas Moorthi & Vijy Aurs
 ▪️Fassarawa - Haiman Raees 

🇮🇳 Odalaaladi mucchitta kendava kattu bicchitta, Gandede dheera

🇳🇬 Jarumin mai zuciyar zaki ya fallatso garwashin da ke ruri oye a cikin wanzuwar halittarsa. 

🇮🇳 Kanakanavanu adimuriyanu kenaki
Rosha bicchitta entede shoora

🇳🇬 Hamshaƙin sadaukin ya antayo fushi da harzuƙarsa yana mai ƙalubalanta da dukkan takun sawayensa. 

🇮🇳 Kalikula kenaki kadalaala kenakida, Shoora ee sultaana

🇳🇬 Ƙasurgumin jarumin ya takali masarautar jarumai, ya kuma takurawa ƙasan teku, mai taurin rai kenan/jarumin sarki kenan. 

🇮🇳 Kalikula kenaki kadalaala kenakida, Shoora ee sultaana

🇳🇬 Ƙasurgumin jarumin ya takali masarautar jarumai, ya kuma takurawa ƙasan teku, mai taurin rai kenan/jarumin sarki kenan. 

🇮🇳 Dheera dheera dheera dheera ee sultaana x3

🇳🇬 Jarumi mai izza. Jarumi mai izza. Wannan shi ne jarumi kuma sarki mai izza. 

🇮🇳 Pratikaarada kidi Kudiyodeda gadi, Sidideddu ede ettida shoora

🇳🇬 Mai ƙarfin damtsen dukan maƙiya, jarumi mai izza kenan. 

🇮🇳 Ranarangada chadurangava bhedisi, Eduraaliya edegeragida eega

🇳🇬 Mai naci ne shi akan ƙudirinshi, ko ƙuda bai kai shi ba, babban jarumi kenan. 

🇮🇳 Tode tattida jagamondara seelida shoora ee sultana.

🇳🇬 Bashi da tamka, babban jarumi kuma sarki mai tarin ƙwanji. 

🇮🇳 Usira koneyalu maatu nenapirali

🇳🇬 Ko da a yayin numfashinka na ƙarshe ne, kada ka manta alƙawarinka. 

🇮🇳Mullu haadiye siguvudu jagadali

🇳🇬 Hanyoyi masu cike da ƙayoyi su za ka fuskanta a wannan duniyar. 

🇮🇳 Dhareye uridu nintharu saagi baa

🇳🇬 Ko da ƙasa za ta ƙone ta zama katanga, ka tsallake ta ka zo. 

🇮🇳Hatave bidade eduru nillu baa

🇳🇬 Ka tsaya a gaba ba tare da girgiza akan jajircewarka ba. 

🇮🇳 Dheera dheera dheera dheera ee sultaana x3

🇳🇬 Jarumi mai izza. Jarumi mai izza. Wannan shi ne jarumi kuma sarki mai izza. 

✍🏻 Haiman Raees 

Post a Comment

0 Comments